Sashe 19
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu.
Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin.
A hankali Mommy ta ɗago Jabun Raiha tana yi mata sannu, Daddy ya zauna a ɗaya ɓangaren sannan ya riƙo hannunta ya ce, "Allah ya baki lafiya My Raihan." Jabun Raihan ta ɗago tana gyaɗa kai. Mommy ta miƙe tana faɗin, "Mu je na raka ki, ki yi sallah kin ga Magriba ta wuce ga Isha'i ita ma tuni an yi ta." Ras gaban Jabun Raihan ya faɗi don ko kaɗan bata ƙaunar sallah ba abin da ta ƙi jini irin ta ji an ambace ta. Idan aka ce ta yi ma bata san ta inda za ta fara ba tun da ba addininta bane, tana cikin nazari ta riski muryar Daddy yana faɗin, "Haba Zainab yaushe yarinyar nan ta farfaɗo, don Allah ki bari ta huta ta ci abinci ta sha magani tukunna." Mommy ta ɓata fuska tana faɗin, "Daddy babu wani uzuri game da mara lafiya a kan sallah, hatta majiyacin da yake kwance baya iya tashi matuƙar yana cikin hayyacinsa dole a yi masa alwala ko yana daga kwance ya gabatar da sallah..." Daddy ya katse Mommy cikin ɓacin rai yana faɗin, "So kike ki kafirta mu ni da Ƴata kenan? Ce miki na yi ba za ta yi sallah ba? Ki fita idona Zainabu akan katsalandan ɗin nan da kike min yana neman wuce gona da iri." Mommy ta miƙe cikin fushi ta fice daga ɗakin don ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba.
A hargitse Raihan ta waiga don ganin wanda yake shirin dakatar da ita ga cika umarnin Abar bauta, tana waigawa ta hangi Alhaji Ƙarami abokin mahaifinta. A hankali ya fara takowa gabanta cikin izza yana faɗin, "Matata ce irin dana dasa don ya ci gaba da yaɗo domin samun farinciki da rayuwa mai morewa." Raihan cike da ƙarfin gwiwa ta juya wurinsa tana cewa, "Wa'adin yabanyarka ya zo ƙarshe don a yanzu ba sai gobe ba zan sallamawa abar bauta jininta, ko mahaifana basu isa su dakatar da ni ga aiwatar da wannan kudurin ba." A zabure Alhaji Ƙarami ya fisgo Raihan da niyyar illata ruhinta, da sauri ta kauce ya kaiwa ƙasa duka. Duk abin da yake faruwa babu wanda ya lura daga masu naƙudar dake cikin halin naƙuda har zuwa Nurses ɗin da suke taimaka musu. Raiha ta kalle shi a fusace ta nuna shi da yatsa tana faɗin, "Ka fita a ido tun ban hallaka ruhinka kai da matarka ba, ka barni na yi abin da ya kawo ni tun ban fusata na yi ɓarnar da za ta girgiza ruhinka ba." Ko ba a faɗa ba Alhaji Ƙarami ya san wacece Raihan a cikin Daular ƙungiyar asiri, dukda ba ƙungiyarsu ɗaya ba ya samu labarinta da jimawa a wurin Babban Dodo, tun da jimawa ya so ya ringajayi ruhinta zuwa ta su ƙungiyar amma Huzaifa ya yi kaka gida ya hana shi aiwatar da abin da ya yi niyya. Amma dukda ya san wannan ƙarfin iko nata ba zai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin ya ƙwato rayuwar Matarsa ba don ita ce komai na shi a rayuwa. Ya kalleta cikin dakiya da ƙarfin zuciya ya ce, "Na salwantar da rayuwar Mahaifana don cimma burina, na sadaukar da ƙwayoyin haihuwar jikin matata don samun farincikina, duk wani ɗigon numfashi da matata take yi ƙarin arzikina ne, matsawar babu ita duk wahalar da na yi ta tsawon shekaru ta kau don haka dole na dakatar da ke." Raihan na cikin sauraronsa ta ji kuka jariri a gefenta tana dubawa ta ga ta biyun ce ta haihu sai Matar abokin mahaifinta da suke taƙaddama akanta ita kaɗai ta rage, Raihan ta bushe da wata mahaukaciyar dariya haɗe da dukan ƙasa wurin, nan take wasu manyan kunamu suka fara fitowa suna tunkarar wurin da Alhaji ƙarami yake, da sauri suka fara rarrafawa har suka mammaƙale a jikinsa suka fara kai masa sara ta ko'ina. Da sauri ta koma kan matarsa da take cikin wani hali tana nishi da alama ita ma kan jariri ya fara hararamar fitowa, juyawa ta yi wurin da Kunamun nan suke fitowa ta sa hannu ta ɗauko guda ɗaya ta leƙa ƙarƙashin matar ta tura mata kunamar ta cikin gabanta. Lokaci ɗaya matar ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, Raihan ta saki wani shu'umin murmushi ta waiga wurin da Alhaji Ƙarami da yake ta ƙoƙarin ganin ya ƙwaci kansa ta hanyar amfani da tsafi da sihiri, amma tuni kunamun suka kaishi ƙasa. Takawa ta yi har gabansa ta tsugunna a saitin furkarsa ta furta, "Da ka barni na yi abin da yake gabana da ka ceci rayuwarka, ba na son shisshigi a lamurana don haka bana jira ga duk wanda zai kawo min matsala." Tana gama maganar ta miƙe zuwa gaban Matar Alhaji ƙarami da Nurses suka rufu a kanta don ganin sun kawo mata ɗauki, tana nan tsaye Likita ya ƙaraso kanta don har ya fara tunanin a yi mata CS Raihan ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo sannan ta ɗauki ruhin Matar Alhaji Ƙarami ta wuce da ita zuwa kogon tsafinsu.