← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 110

Sashe 24

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kasancewar bacci bai ɗauki mommy da wuri ba sai wurin asuba ya sa ta makara, ba ita ta farka ba sa wajen ƙarfe bakwai saura, da sauri ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala tana fitowa ta fara bubbuga filon da Daddy yake kai tana faɗin, "Daddyn Raihan ka tashi mun makara." Cikin magagin bacci Daddy ya yi miƙa yana faɗin, "Asuba ta yi ne?" Haushi ne ya kama Mommy don tana burin ta ga mijinta na da tsayayyir ibada amma hatta sallar asuba sai ta tashe shi, idan kuwa ita ta makara to sai dai su yi sallah da safiyar Allah. Kan dadduma ta hau tana saka hijabinta ta ce, "Don Allah ka tashi bakwai saura fa dubi rana har ta fito." Daddy ya yi juyi yana mutsuka idanu, Mommy tana gama magana ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta jima a kan sallaya tana addu'o' sannan ta shafa ta koma kan Daddy ta sake tashinsa. Bayan ya shiga toilet hijabinta ta ajiye ta nufi hanyar fita don ta tashi Raihan saboda ta tabbatar bata tashi daga bacci ba. Tana tafe gabanta na faɗuwa don abin da ya faru a daren ranar ne yake sake faɗo mata, cikin dakiya ta ci gaba da takawa tana tafe tana karanta Amanarrasulu. Lokacin da ta zo bakin windon da ta ga Raihan na zaune ta jima a wurin tana kallo sannan ta wuce sashen Raihan ta tura ƙofa, tana shiga ta same ta daga ita sai wata yaloluwar riga iya cibiya tare da gajeren wando da kaɗan ya fi pants. Bubbuga fulonta Mommy ta fara yi tana kiran sunanta, Raihan har ta ɗago ta kafe Mommy da ido sai kuma ta sake tafiya luuuu bacci ya sake yin gaba da ita. Mommy ta sake ɗago da Raihan tana faɗin, "Ke Raihan me yake damunki ne tashi ki yi sallah." A hankali Raihan ta buɗe idonta sannan ta yunƙura ta tashi zaune cikin magagin bacci ta ce, "Mommy lokaci ya yi ne?" Mommy ta watsa mata harara tana faɗin, "A'a ke ake jira, yarinya kullin sai antashe ki sallah amma kullin abin ki ƙara gaba yake." Raihan ta tashi tana tura baki gaba ta ce, "Ai ke dama kullin mommy a cikin masifa kike shi ya sa nafi son Daddy wallahi." Kanta ba ɗan kwali ta nufi banɗaki da sauri Mommy ta buga mata tsawa tana miƙa mata hularta da ke kan katifa. Ba don ta so ba ta amsa ta faɗa ba tare da ta furta kalma ɗaya ta addu'a ba. Mommy na tsaye Raihan ta fito ta fara duba drower kayanta tana lalubar hijabinta. Ganin haka ya sa Mommy ta fice ta bata wuri, kai tsaye ta wuce sashensu Inno. Tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama tana faɗin, "Inno barkanku da safiya." Bacci ta same su suna yi ganin haka ya sa ta fice daga ɗakin, ɗakin baƙi ta leƙa ta samu Safara'u wasu ƴan uwan Inno da suka rage basu fi mutum biyar ba, sai da suka gaisa sannan ta fito. Tana shirin hawa sama ta riski muryar Mama Uwani na gaisheta sai dai yanda ta lura kamar Mama Uwani na cikin damuwa. Bayan sun gaisa har mommy za ta haye sama da juyo ta ce, "Uwani lafiya kuwa?" Idanun Mama uwani suka ciko da ƙwalla ta ce, "Hajiya ina cikin damuwa, yanzu haka yau da farar safiya aka yi min waya ciwon Mahafiyata ya tashi." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Ciwon Inna ne ya sake tashi." Mama Uwani ta gyaɗa kai tana sharce hawaye, Mommy ta yi ƙasa da muryar cikin tausayawa ta ce, "Allah ya bata lafiya amma gaskiya ya kamata ki je ki dubo ta yau don Mahaifi ba wasa ba." Mama uwani ta goge ƙwallar idonta tana faɗin, "Allah ya saka da alheri Hajiya." Mommy ta ɗan bata fuska ta ce, "Na ce ki daina yawan yi min wannan godiyar mama uwani mun riga mun zama ɗaya. Ki shirya yanzu idan kin gama ki yi min magana, kafin ki tafi ki shiga store ki tafi musu da kayan abinci." Mama Uwani ta tsugunna har ƙasa tana godiya bisa tsautsayi kofaton ƙafar Mama uwani ya bigi ƙafar mommy har sai da mommy ta ɗan yatsuna fuska saboda zafin da ta ji, amma sai bata kawo komai ba ta ɗago Mama Uwani tana faɗin, "Haba Uwani tashi don Allah. Mama Uwani ta tashi sannan mommy ta wuce wurin Daddy.

Raihan na ɗago hijabi ta ji wani irin jiri na ɗaukanta, da ƙyar ta iya dafa bango ta ƙarasa bakin gadonta, ƙarasawarta keda wuya ta yanke jiki ta faɗi. Abar bauta na ganin ruhin Raihan ya fita daga jikinta ta yi murmushin samun nasara, Raihan ce tsaye a bakin ɗakin arziƙi wani irin farin hayaƙi mai ɗauke da surar wata irin hallita ya fara zagaye Raihan, sannu a hankali Abar bauta ta zagaya gaban Raihan ta ce, "Kasancewarki a nan yana nufin zamtowarki Shugaba, buɗe bakinki domin mallakar shuɗaɗɗan ruhi." Ba musu Raihan ta hangame bakinta nan take wannan farin hayaƙin ya fara shiga ta cikin bakinta, ya jima yana tafiya sannan ta haɗiye shi gabaɗaya. Tana gama Haɗiyarsa wani irin tari ya turniƙeta idanunta suka yi jawur, kanta ya fara sara mata ga wani irin gumi da yake tsattsafo mata. Ana cikin haka jikinta ya fara wata irin karkarwa kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta fara ƙoƙarin durƙushewa, cikin bada ƙarfin gwiwa Abar bauta ta fara magana da ƙarfi, "Kin kasance jaruma karki bari wani ruhin ya rinjaye ki, kin kasance mai nasara kuma har abada za ki kasance mai nasara." Ruhin Raihan ya sake yunƙura da ƙyar yana layi sannan ta samu ta miƙe tsaye daram, tashinta tsaye ya sa kogon wurin ya fara girgiza haɗe da hasken walƙiya. Lokaci ɗaya Hatsabibiya da abar bauta suka ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya cikin haɗin baki suka furta, "Barka da shiga sabuwar rayuwa yake shugaba." Raihan bata kulasu ba ta wuce ɗakin Kujera ta haye kan wata karagar kujera mai ɗauke da ƙoƙon kawunan bil'adam a saƙale a jiki. Sai da ƙare musu kallo cikin izza, isa da nuna tsantsar mulki ta ce, "Barka dai, a wannan lokacin bana buƙatar hayaniya hutu ya wajaba a gare ni." Tun bata rufe baki ba suka dare daga gabanta kowanne ya kama gabansa.

Kafin wani lokaci Tuni Mama Uwani ta shirya tsaf cikin atamfa, sai da ta yi sallama da su Inno har ta zo bakin ƙofa Inno ta ce, "Saboda Allah Uwani idan muka bari kika tafi dubiyar nan ke kaɗai ba mu yi rashin kara ba?" Mama Uwani ta yi musu murmushi ta ce, "Babu komai Inno ni ma ai gobe zan dawo." Goggo ta yi karaf ta ce, "Ita fa ziyarar mara lafiya lada gare ta, ina ni ina barin lada a wurin Allah? Uwani bari na ɗauko mayafina mu tafi saboda Allah mahafiyarki ai kamar tamu ce gabaɗaya."

(Har na gano idon Goggo a duniyar aljanu)

Mama Uwani ta sake murmushi ta ce, "Ai na ga kuna amsar baƙi ƴan gaisuwa shi ya sa da kin yi zamanki Goggo." Goggo ta yi jim sannan ta ce, "Ke Uwani yi tafiyarki kin ji, ina ni ina zuwa ƙauyenku bansan kalarsu ba haka kawai su lashe min kurwa. A'a raba ni da wannan tafiyar daga nan gidan sai albasu, Albasu babu mai kambun baka balle maita je ki sai kin dawo ki duba mai jiki." Huzaifa ya yi dariya don har zuciyarsa Diramar su Inno bashi dariya take, sannan ya fice daga ɗakin. Kuɗi masu yawa Mommy ta ɗiba ta bawa Mama Uwani tare da kayan abinci sannan suka yi sallama.

Huzaifa na fita daga gidan nan take ya ɓace ya fara lulawa cikin iskar sararin samaniya, bai tsaya a ko'ina ba sai Dajin Bolgal-Kissam a cikin ƙarƙashin ƙasa cikin wara tsohuwar ƙorama. Yana zuwa wasu dakarun aljanu suka dakatar da shi, waɗanda suke zagaye da wani tsohon aljani tukuf. A fusace Huzaifa ya fara fisgewa yana shirin yin magana Dattijon aljanin da ke zaune a tsakiyarsu ya furta, "Tabbas lamarinka ya munana Huzaifa, a kullin ina gaya maka kowa ya bar gida; gida ya bar shi."

TO ME KUKE HARSASHE SHIN HUZAIFA ZAI SAMU BIYA BUƘATARSA KO ƘAƘA😂 INA LABARIN SHUGABA RAIHAN? 😂 INA MUKU FATAN ALHERI🥰

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan number 0706 206 2624

12
Chapter 24 · 0% Book details