Sashe 36
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Abdullahi Muhammad Zango shi ne ainihin cikakken sunan Daddy, Mahaifinsa Marigayi Muhammad Zango asalinsu mutanen Daura ne cikin unguwar Zangon Daura. Su uku ne rak a wurin Mahaifinsu da mahaifiyarsu Alhajia Al'ƙasim shi ne babba, Marigayi Alhaji Haruna mai binsa sai Alhaji Muhammad Zango ɗan autansu wato Mahaifin Daddy. Ana kiransa da Alhaji babba sakamakon cin sunan kakansa na wurin Mahaifiya da ya yi, Mahaifinsu Marigayi Alhaji Babba riƙaƙƙen ɗan boko ne ya karanci fannin Law. Don haka Mahaifinsu Daddy gabaɗaya sun yi karatun boko mai zurfi, kuma dukkansu suna da rufin asiri. Alhaji Babba sun taso cikin gata da rufin asiri kasancewar Mahaifinsu yana haɗawa da harkar kasuwanci yana da rufin asiri sosai, Alhaji Ƙasim shi ya fara yin aure yana koyarwa a babbar jami'ar Sokoto sai da ya shekara bakwai da aure ƴaƴansa biyu sannan mai binsa Haruna ya yi aure, shi kuma yana aiki a ƙarƙashin hukumar kare hatsarirrika da ababen hawa (Road safety.) Bayan ya yi aure da wata biyar Mahaifin Daddy ya kammala bautar ƙasa shekara na zagayowa ya samu aiki a babban asibitin Katsina da yake fannin likitanci ya karanta. Rayuwarsu sun taso gwanin birgewa tare da haɗin kai a tsakaninsu, suna matuƙar mutumta junansu don haka akwai kyakkyawar alaƙa da soyayyar ƴan uwantaka a tsakaninsu. Mahaifin Daddy shekararsa uku da fara aiki ya haɗu da Inno, a lokacin ankwantar da Mahaifiyarta a asibitin da yake aiki bayan sallamar Mahaifiyarta Alhaji Babba har garinsu Inno ya je, Inno Bafulatanar ƙauyen Madaka ce bata yi karatun boko ba, sai dai ta yi makarantar allo da makarantar dare. Ita kaɗai iyayenta suka haifa gaba da baya, da sassafe suke fita kiwon shanu sai yamma ta doso sannan suke dawowa su huta su ci abinci wurin ƙarfe huɗu su tafi makarantar allo. Idan dare ya yi bayan magariba su tafi makarantar dare, da farko ƴan uwan Alhaji babba ba su so auren Inno da shi ba don a ganinsu me zai yi da ƴar ƙauyen da ko cikakkiyar hausa bata ji. Amma da suka ga yana so a kan dole suka yi masa addu'a da fatan alheri, kuma cikin lokaci ƙanƙani maganar aurensu ta kankama aka tsaida lokaci aka sha biki. Bayan biki Alhaji babba ya ɗauki matarsa ya tafi da ita cikin garin katsina ya yin da yake ziyartar ƴan uwansa lokaci-lokaci, dama kuma tun kafin aurensa da Inno ma haka yake yi.
An yi auren Inno da Alhaji babba da wata biyar Allah ya yi wa mahaifiyar su Alhaji babba rasuwa, wannan rashi ba ƙaramin taɓa su ya yi ba. Ana nan har Allah ya bawa Inno ciki sai dai cikin ikon Allah ta riƙa haihuwa suna mutuwa har sai da suka fidda rai da samun rayayyan ɗa. Kusan shekara goma da aurensu sannan Allah ya bawa Inno cikin Daddy a lokacinma ba su taɓa tsammanin zai rayuwa ba, amma cikin ikon Allah ya ɗore. Bayan haihuwarsa da shekara biyu Inno ta sake samun cikin Mama Hasiya bayan wata tara ta haifeta sai dai daga kansu bata sake samun haihuwa ba. A haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu suka ci gaba da rainon ƴaƴansu cikin birgewa, kwatsam watarana aka wayi gari da rasuwar Mahaifiyar Inno ko kwana arba'in ba a yi ba shi ma mahaifinsu Alhaji Babba ya ce ga garinku nan. Wannan mutuwa ba ƙaramin girgiza su ta yi ba don kusan duka mamatan mutuwar faraɗ ɗaya suka yi.
Mahaifinsu Alhaji babba ya rasu babu jimawa Alhaji Ƙasimu ya samu ci gaba ya yin da ya samu koyarwa a wata babbar jami'a da ke ƙasar Ingila. Ƴan uwansa ba ƙaramin daɗin samun wannan ci gaban nasa suka yi ba, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi har Daddy ya shekara goma sha biyu a duniya, ya yin da Hasiya take da shekara tara. Kwatsam wata rana Alhaji babba ya tafi Zangon daura yi wa Yayansa Alhaji Alƙasim barka da zuwa da yake ya zo hutu daga Ingila, a hanyarsa ta dawowa ya yi hatsari nan take ya rasu ko shurawa bai yi ba. Wannan mutuwa ta girgiza Inno saboda zaman lafiya suke yi ita da mijinta ba ƙaramin kulawa suke samu ita da ƴaƴanta a wurinsa ba, gawar Alhaji Babba zangon daura aka mayar da ita. Alhaji Ƙasim ya aika aka ɗauko Inno da yaranta, kowa ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata matuƙa. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta lalace har wani irin baƙi ta yi ko ruwan kirki bata iya sha, wasu daga cikin mutane har sun fara tunanin Inno na da ƙaramin ciki a lokacin, sai daga baya kowa ya fahimci tsantsar damuwa ce. Bayan sadakar Bakwai aka tara su Inno a ɗaki tashin farko da Alhaji Ƙasim ya sanarwa da Inno zai ɗauke ƴaƴan ɗan uwansa, Daddy da Mama Hasiya zuwa ƙasar Ingila. Inno na jin haka ta rushe da kuka nan take mutuwar mai gidanta ta sake dawowa mata sabuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce sam bata ƴarda ba. Sai da aka kai ruwa rana sannan Alhaji Ƙasim ya amince zai barwa Inno Hasiya, don acewarsa babu yadda za a yi ta tafi da ƴaƴan ƙaninsa ƙauye. Ita kuma a lokacin Mahaifinta ya ce sam ba za ta zauna ita kaɗai daga ita sai yara a wani gari ba, ba tare da aure ba dole ta koma gidansa. Wannan lamari ya sake dagula rayuwar Inno tana ji tana gani aka tafi da Daddy, ranar da suka tafi kwana ta yi tana kuka daga ƙarshe ta fauwala wa Allah lamuranta ta rungumi ƴarta Hasiya ta ci gaba da bata tarbiyya.
Rayuwar gidan Alhaji Ƙasim kusan rayuwar turawa suke yi, suna karatun boko sosai sai dai karatun addini ne basu bashi ƙarfi sosai ba. Ƴaƴan Alhaji Ƙasim suma a haka suka taso zuwan Daddy gidan ya sa shi ma ya ɗora daga in da suka tsaya, saboda da farkon zuwansa idan ya yi wani abin har dariya suke yi masa suna yi masa kallon ɗan ƙauye, sannu a hankali ya riƙa ɗaukan ɗabi'unsu har shi ma ya koma kamar yadda suke. Daddy sai da ya shekara biyar a Ingila (England) sannan suka zo ganin gida, Inno ba ƙaramin mamakin girman Daddy ta yi ba. Kamarsa da ta mahaifinsa ta sake fitowa sak, a lokacin Hasiya tana aji uku ƙaramar sakandire ta fara zama budurwa manema har sun fara fitowa, sai dai fir Hasiya ta ƙi basu fuska a cewarta ita ma so take ta zama babbar likita kamar yadda Mahaifinta ya zama. Da farko Inno ta ɗauka shafar aljanu ne ya hana Hasiya kula samari, don har ta fara yi mata ƴan jiƙe-jiƙe, amma da ta ji manufarta sai ta mara mata baya don duk wani abu da za a ce don a yi koyi da Alhaji babba ne, yana matuƙar faranta mata don tana alfahari da haka. Baffajo duk yadda ya so ya ga Inno ta yi aure haka ta ƙeƙashe ƙasa taƙi yarda don ta san muddin ta ce za ta yi aure ƴan uwan Mahaifin Hasiya ba za su bari ta yi agolanci a wani gidan ba. Ƴan uwan Mahaifin Daddy daidai gwargwado na zumunci suna taimakawa Inno da Hasiya don duk wata suke yi mata aike da kuɗi masu tsoka, wannan dalilin ya sa suka fita zakka ita da Hasiya a garin hatta mahaifinta ya huta babu yawon gonar da yake zuwa musamman da shekaru suka ƙara turawa. Lokacin da su Daddy suka zo sun kawo musu tsaraba kala-kala sai dai abu ɗaya ne bata ji daɗi ba ganin yadda yanayin tarbiyya da ɗabi'un Daddy suka sauya, hakan ya ɗaga mata hankali sai dai duk lokacin da ta yi sallah sai ta saka shi cikin addu'arta. Watansu ɗaya da zuwa suka koma a wannan karon Inno ta sawa zuciyarta dauriya, don ko hawaye bata yi amma ta fi sati tana jin kewar ɗanta a zuciyarta. A haka rayuwa ta ci gaba da shuɗawa har Daddy ya kammala karatunsa ya karanci Business Administration, Yaran Alhajin Ƙasim mazan tuni suka dawo Nigeria duka sun yi aure, Daddy na kammala karatunsa suka tarkato suka dawo gida Nigeria sakamakon yin ritaya da Alhaji Ƙasim ya yi, a lokacin tuni Hasiya ta yi aure ta auri wani lectural su da yake ta ci gaba da karatu zuwa matakin NCE a FCE Bichi amma ma zaunin garin kano ne. Alhaji Ƙasim ya ƙanƙare gidansa na gani na faɗa a cikin garin Katsina. Ya yin da Daddy ya koma wurin ɗayan ƙanin Mahifin nasa Alhaji Haruna da ke zaune a garin Kano, sakamakon wani babban kamfanin takalma da Alhaji Aƙasim ya buɗe masa. Sannu a hankali Daddy ya fara cin gashin kansa wannan dalilin ya sa ya sayi ƙaramin gidan a unguwar Sallari, Ya dawo da Mahaifiyarsa a cewarsa bai ga amfanin zamanta a ƙauyen ba tun da shi ma mahaifin nata ya rasu sai ƴan uwa da abokan arziƙi. Inno ba ƙaramin farinciki ta yi ba saboda ko ba komai ta dawo kusa da ƴaƴanta, tun da dama kullin hankalinta yana kansu. Shekararsa biyu da fara aiki ya haɗu da mommy a cikin garin albasu, lokacin ya je shi da Alhaji Haruna ganin wata ƙatuwar gona da za su siya a sake gida kamfanin shinkafa. Da haɗuwarsu ko shekara ba a rufa ba manya suka shiga magana, aka tsayar da ranar aure lokaci na cika aka ɗaura musu aure.
Mu Dawo Labari, amma fa ba shi kenan ba za mu sake tafiya a gaba don jin asalin Goggon Æ´ar garin Albasu.
Littafin Kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar 0706 206 2624
19