← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 110

Sashe 68

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama Hafsat tana tafe zuciyarta fal fargaba da tashin hankali, zuciyarta ce ta shiga wassafa mata tunane-tunane ban da saƙa da warwara babu abin da take yi, lokaci ɗaya zuciyarta ta karye tsora ya dirar mata tana fatan kada Allah ya tabbatar da abin da take zargi. Shiru motar ta ɗauka babu mai iya furta komai, don lamarin ba ƙaramin ɗaure kai gare shi ba. Suna tsaka da tafiya wayar mommy ta shigo wayar Mama Hafsa, gabanta ne ya faɗi ta rasa ya za ta yi don ta san idan ta ɗauka baya wuce ta ce a bata Raihan su yi magana, tun da dama kafin su taho ta gaya mata idan ta je gidan ta haɗa su za su yi magana. Ajiyar zuciya ta sauke ta ajiye wayar ba tare da ta ɗauka ba, idonta ta mayar kan titi haɗe da furta, "Hasbunallahu Wani'imal Wakeel." A ƙofar gidansu Huzaifa suka yi parking ɗin motocinsu, jiki a sanyaye Mama Hafsa ta kashe motar tare da fita tana gaba suna biye da ita, suna shiga suka ci Karo da Mahaifiyar Huzaifa ta rako baƙin da za su tafi tana yi musu su gaida gida. Ganin su Mama Hafsa ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa, ku shiga ciki kafin na shigo." Mama Hafsa yaƙe ta yi ta amsa sannan suka shiga ciki aka yi musu masauki a falo. Jigum-jigum suka yi suna nan zaune aka kawo musu ruwa amma babu wanda ya iya ɗauka ya sha. Mahaifiyar Huzaifa ce ta shiga ɗakin fuska ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya sannunku ya gajiyar hidima da jama'a?" Mama Hafsa ta yi murmushin da bai kai zuci ba ta ce, "Alhamdullah." Sai da ta gyara zamanta tana kallon Mahaifiyar Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Hajiya dama wata magana ce tafe da mu." Mahaifiyar Huzaifa ta tattara hankalinta wurin Mama Hafsa ta furta, "Ina jin ku Hajiya." Mama Hafsa ta kashe wayarta ta jefa jaka sannan ta ce, "Yanzu haka daga unguwar su Raihan muke, mun tafi domin raka bayin Allahn da ba su samu damar zuwa jiya sun ga ɗaki ba." Mahaifiyar Huzaifa ta saka dariya haɗe da cewa, "Allah sarki ya ƴarta tawa da fatan sun tashi lafiya?" Mama Hafsa ta kalleta ta ce, "Gaskiya ba ƙalau ba." Gaban Mama ya yanke ya faɗi tana shirin yin magana Mama Hafsa ta ci gaba da cewa, "Mun shafe sama da awa guda a unguwarsu Raihan amma gidanta ya ɓace mana sama da ƙasa babu shi babu alamarsa, hasalima duk wanda muka tambaya gidan da aka kawo amarya sai dai su ce ba nan unguwar ba ne." Mama Hafsa ta tsahirta cikin damuwa ta dubi Mama ta ci gaba da cewa, "Na san kin san ni ƙanwar Mahaifiyarta ce cikinmu ɗaya, hasalima tun kafin bikin nan muke zarya ni da Mahaifiyarta muna kai kayan jere. Gidan Raihan ba ɓoyayyen wuri ba ne ko a jiya da dare na je gidan mun kai yarinya amma a yau da nake yi miki magana babu gidan Raihan babu alamarsa. Hatta yarinyata a jiya da dare ta manta wayarta a gidan amma da suka koma tun a daren suka nemi gidan suka rasa, da take gaya min ban kawo komai ba na yi zaton dare ne ya sa ba su gane ba kuma abokin Huzaifa shi ya mayar da su. Shi ya sa muka ce bari mu zo mu ji yadda aka haihu a ragaya." A rikice Mama ta ce, "Ban gane ba a ga gidan Raihan ba kamar wani gidan tsuntsuwa, Hajiya wai me kike faɗa ne haka?" Mama Hafsa ta furta, "Abin da dai kika ji na faɗa Hajiya haka ne, mu kan mu muna cikin tsananin mamakin wannan lamarin." Mama ta fara ƙwalawa ƙanwarta Maryama kira, tana zuwa ta nuna mata wurin zama haɗe da faɗin: "Zauna Maryama ba zancan tsaye ba ne. Jiya ba ku kuka ɗauko amaryar Huzaifa ba?" Maryama da gyaɗa kai. Mama ta wara hannu tana faɗin, "To kin ji wai gidan Huzaifa ya shafe babu shi an neme shi an rasa." Nan take Maryama ta saka dariya don ita gani take kamar ma zolaya ce, ganin haka ya sa ran Mama Hafsa ya ɓaci nan take suka ɗauki abin da muhimmmanci don cewa ta yi dole su zo a je a ƙara duba gidan tun da sun ɗauki abin a zuwan wasan yara. Ba shiri Mama ta kira Mahaifin Huzaifa ta sanar masa halin da ake ciki tare da yayansa. Kusan mota huɗu suka yi har da ta su Mama Hafsa suka nufi unguwar su Raihan, Yayan Huzaifa ne ya kira Dr Hussain ya sanar masa halin da ake ciki, nan take shi ma ya zayyane musu abin da ya faru da su da dare na komawa da suka yi karɓo waya amma ba su ga gidan ba. Wannan magana ba ƙaramin sake ɗaga hankulansu ta yi ba, haka suka je unguwar su Raihan suka gama bulayi amma ko gida mai yanayi da na Raihan ba su gani ba. Mama Hafsa da tuni zuciyarta ta karye nan take fa fara kuka tana faɗin akan dole sai su Mama sun faɗi wurin da Huzaifa ya ɓoye musu Raihan, a ɓangare ɗaya kuma tana tsoron kada Allah ya sa ba Huzaifa aljani ne ya ɓatar da su ba ita da mijinta ba. Carko-carko suka yi a wurin da suke tsammanin nan ne daidai gidan Raihan, wani babban fili ne mai ɗauke da kangwaye sai wata ƙatuwar bola wacce da alama duka ƴan unguwar a cikinta suke zuba shararsu. Yara da manya na bakin layin ne suka fara kallonsu kowanne da alama mamakin ganinsu suka yi a tsaitsaye a wurin. Mahaifin Huzaifa ne ya ciro waya ya kira kambar Huzaif don duk cikinsu babu wanda ya yi wannan tunanin, da yake ya ware sifikar (Speaker) wayar nan take suka ji wayar tana shiga. Sai dai har ta katse ba a ɗauka ba yana shirin sake kira wayar Huzaifa da shigo, hannun Baba har rawa yake sannan ya ɗauka yana faɗin, "Huzaifa kana ji na..." Ƙit Baba ya ji an katse wayar gabaɗaya. A hanzarce Baba ya sake kiran wayar amma ɗif ya ji ta a kashe. Hankalin mutanen wurin har ya fi na koyaushe tashi, sunan tsaye saƙo ya shigo cikin wayar Baba da sauri ya shiga dubawa kamar haka haɗe da karantawa a fili.

" _Ku daina wahalar da kan ku akan sai kun nemo wurin da Raihan take domin tana tare da ni, kuma yanzu haka da ni da ita muna kallon duk abin da kuke yi, Ina kallonku a tsaitsaye wurin ƙofar gidana don haka ya kamata kowa ya kama gabansa kafin na ɓatar da ku kamar yadda na ɓatar da gidan tare da Amaryata Raihan. Ni kaɗai ni ne mamallakin Raihan ni ne mijinta na har abada HUZAIFA._"

Ɗago wa suka yi daga kallon wayar ilahirin jikinsu ban da rawa babu abin da yake yi. A ruɗe Baba ya ce, "Wai yaron nan yana da hankali kuwa an ya bai shiga ƙungiyar asiri ba? Kuna jin abin da yake faɗa kuwa?" Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciyar tana faɗin, "Tabbas akwai wata a ƙasa, yanzu dai kun tabbatar da abin da muke faɗa ko? Shi kenan ku dakace mu." Tana gama magana ta yi wa sauran mutanen da suka zo tare magana suka shiga motar suka wuce gida. Sai da suka kusa ƙarasa wa Mama Hafsa ta yi parking a gefen titi sannan ta ciro waya ta kira lambar Daddy, sai da ta kusa katse wa sannan ya ɗauka yana faɗin, "Maman Safna!" Mama Hafsa a sanyaye ta amsa, "Daddyn Raihan kana ina akwai maganar da nake son yi da kai." Da matuƙar mamaki Daddy ya furta, "Ni kuma? Me yake faruwa ba dai wani abu ne ya faru a gidan Raihan ɗin ba ko?" Mama Hafsa ta ce, "Ina son magana da kai da fatan baka kusa da Aunty Zainab." A gaggauce Daddy ya ce, "Kina ina yanzu ni fito wa zan yi yanzu dama." Mama Hafsa ta ce, "Muna kan titinku za ka ga motoci biyu a har tawa." Daddy bai jira cewarta ba ya katse wayar. Ko minti uku Daddy bai ƙara ba ya fito daga gidan saboda tashin hankali da fargabar abin da za a gaya masa ko mota bai fito da ita ba, Mama Hafsa ce ta fito daga motar tun bai ƙarasa wurinta ba ya ce, "Hafsa me yake faruwa da Raihan? Me ya samu mijinta ko shi ma mutuwa ya yi?" Mama Hafsa idanunta suka ciko da ƙwalla tana faɗin, "Daddyn Raihan mun rasa gidan Raihan hasali ma daga ƙarshe har wani saƙo Huzaifa ya turo wa Mahaifinsa a waya..." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe sai da Mama Hafsa ta sanar wa da Daddy, a hargitse ya furta: "Huzaifaaaaa! Dama na faɗa sai da jikina ya ba ni wannan Huzaifan ba alheri ba ne."
Chapter 68 · 0% Book details