← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 110

Sashe 26

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da Mommy koma ɗakin Daddy tuni ya yi sallah ya koma ya kwanta, a gefensa ta zaune murya a sanyaye ta fara yi wa Daddy magana. "Daddyn Raihan!" Janye blanket ɗin fuskarsa ya yi bai amsa mata ba ya zuba mata ido tare da sakar mata murmushi, ganin yanayinta kaɗai ya tabbatar masa da tana cikin matsananciyar damuwa. Nan take ya ji ta bashi tausayi don shi kansa ya san macece mai juriya da ƙarfin hali, tana shirin yin magana ya rigata da cewar: "Zainab!" A hankali ta ɗago idanunta tana kallonsa ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki." A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta fashe da wani irin matsanancin kuka, hannu Daddy ya sa a bayanta yana bubbugawa a hankali yana faɗin, "Shiiiii ba kuka na ce ki yi min ba." Mommy sai ta yi mai isarta sannan ta ɗago tana faɗin, "Daddyn Raihan gidan nan sam bashi da kyau, don Allah ka sauya mana domin jiya tsorata ni aka yi Allah ne kaɗai ya sa ina da yawancin kwana." Ido ya zura mata yana kallo sai kawai ya ji ta bashi tausayi, ya samu kansa da cewa: "Ina kike son mu koma? Kar ki manta kwananmu ɗaya yau da tarewa." Mommy ta yi jim sannan ta ce, "Haka ne amma gaskiya ina jin tsoro." Duk abin da ya faru da ita sai da Mommy ta sanar masa shi kansa Daddy jikinsa ya yi sanyi don haka ya amsa mata da cewar: "Kin ga muna shirye-shiryen tafiya India mai zai hana mu fara nemawa Raihan lafiya idan za mu dawo sai mu sauya gida, ina ga kamar haka zai fi." Mommy har ta fara aminta da maganar Daddy ta ce, "To idan mu za mu tafi India ya za mu yi da su Inno? Ina jin tsoron kar a tsorata su kasan ga jikin girma." Cikin gamsuwa Daddy ya gyaɗa kai yana cewa, "Tabbas kin yi tunani mai kyau a yau insha Allah zan san abin yi ina jin na sa a gyara gidana na Rijiyar zaki." Ba ƙaramin daɗi mommy ta ji sannan ta ce, "Ya kamata a yi saukar Alƙur'ani kafin a shiga gidan saboda shaiɗanu." Daddy ya yi dariya yana faɗin, "Oh Zainabu ko da mai rauhanai zan sa miki? Kullin baki da magana sai ta shaiɗanu, to ai shi kenan yadda kika ce haka za a yi uwargida sarautar mata tun da kin maidani mijin hajiya." Mommy ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin, "To ai dama ba a canzawa tuwo suna." Daddy ya birkitota jikinsa yana cewa, "Wai yaushe za ki nemar mini ƴar budurwa na aura ne, ko a ƙawayen Raihan ki duba min mai hankali man." Mommy ta yi masa harar wasa tana faɗin, "Na ga ka fini manyan idanu ka duba wacce ta fi maka, ba don ina kishi ba da sai na ce ka auri Intisar don ta fi sauran nutsuwa." Daddy ya sa dariya ya ce, "Wai Allah don Allah daina faɗa gemai-gemai da ni ai sai girma ya faɗi, kedai kawai kin binne min kan angulu don kar na ƙanƙaro amarya." Gabaɗaya suka saka dariya.

A ranar Daddy ya bada umarnin a gyara gidansa da ke Rijiyar zaki, mommy ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Bayan tafiyar Mama Uwani ta ƙara saka karatun kur'ani ta sake kwanciya don bata sami wadataccen bacci ba. Daddy na hanyar komawarsa gida ya kira lambar Dr sai da suka gaisa Daddy ya ce, "Dr ya ake ciki da maganar tafiyarmu, bizarmu fa ta fito duk abin da ake buƙata ya kammala na ji baka sake yi min maganar ba, ga shi har yau ba mu sake yin waya ba." Dr ya yi jam sannan ya ce, "Wacce irin tafiya Alhaji? Wallahi jiya na so na kira na baka haƙuri a kan rashin zuwan da na yi, sakamakon wani yanayi da na ji amma sai na ga dare ya yi..." Daddy ya katse Dr da cewar, "Ban gane abin da kake nufi ba." Dr ya yi gyaran murya ya ce, "Alhaji jiya ba ka kira ni akan rashin lafiyar Raihan ba?" Daddy cikin sauri ya amsa da, "Eh haka ne." Dr ya ci gaba da cewa, "Na taso zan zo dubata kaina ya sara ban kuma sanin wurin da nake ba sai goma saura, to na so na kira ka kuma dare ya yi." Daddy jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, a hanzarce ya ce, "Dr ni fa kaina ya kulle jiya ba kai ka zo ka dubata har ka yi min maganar zuwa India ba?" Dr cikin mamaki ya ce, "Kai an ya kuwa Alhaji ko dai baka gidan ne Alhaji." A gaggauce Daddy ya ce, "Kana ina yanzu zan zo na same ka."Kai tsaye Dr ya kwatanta masa wurin da yake, Daddy ya bawa motarsa wuta yana gabda ƙarasawa ya ci karo da mata matashiyar budurwa tsugunne a kan titi ta kifa kanta cikin cinyoyinta da alama kuka take yi.

Yau kunsha kura-kurai ban yi Editing ba a yi sorry🥱

LIttafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min magana ta wannan lambar. 0706 206 2624

13

Da mamaki Daddy yake bin wurin da kallo don hanyar babu hatsaniya kasancewar magriba ta fara kawo kai, horn ya fara yi a hankali a tunaninsa ko wata lalurar ce tasa yarinyar za ma a kan titi. Sai dai ko gezau bata ɗago ba duk da yana tafe yana ci gaba da danna horn ɗin motarsa har ya kusa ƙarasawa wurinta. A hankali ya gangara da niyyar yin parking wayarsa da take ringing ta katse shi, number Dr ya gani ya sake kiransa da sauri ya ɗauka ya kanga a kunne yana faɗin, "Hello Dr ga ni na taho wurinka." Daga can ɓangare aka amsa da cewar, "Alhaji ka yi haƙuri ɗazu arashi aka samu wani ƙanina ne ya ɗauki wayar ya maganar tafiya Indian?" A fili Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido ya ce, "Ni dama na yi mamaki da jin irin maganganun da aka yi ɗazu, yanzu kana ina?" Daga can ɓanagaren aka amsa da cewar, "Yanzu ka jira ni a gida zan zo na same ka." Daga haka suka sallame wayar, Daddy na ajiya wayar ya ɗago da niyyar ci gaba da Driven ya hangi saman titin fayau babu yarinyar babu alamarta. Da mamaki ya fara kallon wuraren don ko kaɗan bai lura da lokacin da ta tashi daga wurin ba, cikin rashin damuwa ya ci gaba da tafiya yana saƙa yadda tafiyarsu za ta kasance.

Yana komawa gida har ɗaki ya je ya samu su Inno bayan sun gaisa ya ɗan sosa kai ya ce, "Inno dama zuwa na yi da wata magana." Goggo ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabinta ta ce, "Audullah don Allah ba ka cewa na baku wuri za ku yi sirri? Allah ya sani ba zan zauna na ji sirrin ɗa da uwa ba." Daddy ya yi murmushi yana faɗin, "Goggo ba fa wata magana bace, dama gobe idan Allah ya kaimu za mu wuce ƙasar India wurin duba lafiyar Raihan, sai kuma maganar sake gida da za mu yi." Inno ta yi kasaƙe tana kallonsa sannan ta ce, "Ita dai Raihanu ba zan hana ka nema mata lafiya ba, amma saboda Allah Audullahi me ye aibun gidan nan?" Goggo ta wara hannuwa tana faɗin, "Ta ya ni gani kuma wallahi ko a Albasu babu ƙerarran gida kamar wannan." Daddy ya zauna sosai yana cewa, "Zainabu ce ta buƙaci haka tana ganin kamar nan ya muku girma idan muka tafi, dukda zan sa a kawo wacce za ta ci gaba da taya ku zama." Goggo ta ɓata fuska ta ce, "To yanzu fusabillahi ƴan zaman makoki haka za mu riƙa gantalin gaya musu mun sauya gida daga wannan zuwa wannan, Allah ya sani ƙawayena na Albasu rankatakaf sun ce za su zo sadakar uku haka za su riƙa bilayin nemanmu?" Inno ta taɓe baki ta ce, "Bar shi Zinaru, Audullahi so yake ya nuna mana yawan arzƙinsa to Allah ya sani daga gidan idan ka matsa min sai na koma wani wurin zan bi zinaru mu koma Albasu." Daddy ya yi shiru don yadda ya ga sun rikice masa da wuya idan zai shawo kan tsofaffin, ganin ya yi shiru Inno ta leƙa fuskarsa ta ce, "Amma dai ba haushina kake ji a zuciyarka ba ko Audullahi?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "Haba Inno kawai ina tunanin wacce zan ɗauko ta taya ku zama ina ga a samu budurwa da Dattijuwa ko?" Inno da Goggo suka washe baki suna faɗin, "Eh haka ya yi Allah ya yi albarka." Daddy ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Yana zuwa ya sanar wa da Mommy yadda suka yi da su Inno, Mommy ta so a sauya musu gida amma babu yadda ta iya haka za ta haƙura. Sai dai ta bawa Daddy shawara a kan ya kirawo malamai su zo su yi saukar karatun alƙur'ani. Kuma a ranar dangin Mahaifin Daddy na nesa suka zo, ita ma mommy ta yi wa wata ƙanwarta Hajiya Hafsa magana akan ta zo gidanta ta zauna kafin ta dawo daga tafiya.
Chapter 26 · 0% Book details