← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 110

Sashe 46

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana sauran kwana biyu za a sallami Raihan Daddy da kansa ya kira malamai suka yi saukar alƙur'an, a ranar da suka koma haka aka turare gidan da Habbatussauda Mommy ta kai kayan Raihan ɗakinta don ta gama tsara Raihan a wurinta za ta koma da kwana. Kwanan su Mommy biyu da dawowa aka ɗebo su Inno aka dawo da su, da ido suka riƙa bin Raihan da kallo. Har sai da Raihan ta tsargu ta ce, "Inno Lafiya wannan kallon fa." Inno ta yi tsumu kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ra ce, "Haba Raihanu me kika gani?" Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wallahi duk na ga kwana biyu kun zama wasu salihan bayi tsofaffin nan an ya ba wani abin kuke ƙullawa ba?" Mommy da ta kawo kai cikin ɗakin ta watsa wa Raihan daƙuwa ta ce, "Gidanku Raihan Iyayen nawa ne za su ƙulla miki wani abin?" Raihan ta yi dariya mai sauti tana nuna Goggo da ta rufe ido a zuwan bacci take yi, amma kana kallon yadda take motsa ƙwayar idonta za ka fahimci ba bacci take ba. Raihan ta ce, "Allah da gaske ki ga fa yadda Goggo take mintsina idanu kai da gani kasan baccin ƙarya take." Mommy ta kai mata dukan wasa ta ce, "Raihan wai yaushe kika raina su Goggo haka?" Goggo ta ɗago da kai ta ce, "Duk wanda ya raina uwar wani ta shi ya raina." Daddy ya shigo ɗakin ya zauna suka ci gaba da hira, ita dai Inno sai ɗari-ɗari take yi tana tsoron abin da kaje ya zo.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidansu Raihan gwanin birgewa don a wannan lokacin sam ba su da wata damuwa, duk wasu hanyoyi da suke katange ɗan adam daga kaidin aljan su Mommy suna ƙoƙarin ganin sun bi. Hatta al'amuran yau da gobe Mommy ta fara nusar da Rainan, har aikin gida da girki babu wanda bata nuna mata saɓanin lokacin baya da sai dai a girka a bata ta ci. Daddy yana ganin duk abin da yake faruwa sai dai uffan bai ce ba don nasihar Malam Usman ba ƙaramin ratsa shi ta yi ba, kuma lokaci bayan lokaci suna ci gaba da karɓo mata magunguna da turarika. Babban abin da ya tsayewa Raihan a rai tun da ta kwanta jinya ko a waya Intisar bata kira ta ba balle ta je duba ta, bata kawo ƴan Department ɗin su za su je ba saboda da dama wasu ba mu'amala suke da ita ba. Mazan ajinsu uku ne suka taɓa zuwa gidansu Raihan, Kabiru ya kwatanta musu Waraka Islamic Chemist, lokacin da suka je duba Raihan Daddy da Mommy ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Raihan na zaune ta dubi Mommy ta ce, "Ni kam na yi tsammanin ko kowa zai guje ni Intisar ba za ta guje ni ba, tun fa a Asibiti rabona da ita ko da muka dawo gida bata zo ba, babu waya ko text message yau fa sama da wata biyu da yin ciwona." Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ki yi mata uzuri mana Raihan kin san ɗan adam jiki da jini kika san abin da ya hanata zuwa? Me ya sa baki kirata kin ji uzurinta ba? Ni fa ina ga haka kawai ba za ta ƙi zuwa dubiyarki ba kema kin sani." Cike da gamsuwa Raihan ta ce, "Haka ne Mommy amma duka layikanta a kashe idan na kira, kuma kin san tun kwanaki iyayenta suka koma Kaduna a hostel take da zama kin ga da sai na je gidansu na ji ko lafiya. Amma zan kira Farida hostel ɗin au ɗaya." Mommy ta jinjina kai ta ce, "Allah ya sa mu ji alheri." Raihan ta amsa da Amin.

Raihan ta warware garau har Daddy ya yi yunƙurin mayar da ita makaranta suka nuna ya yi wuri a mayar da ita, saboda da yin ciwonta da komawarta makaranta ko wata shida ba a yi ba. Ganin za a bata lokaci ya sa Daddy ya yi mata transfer zuwa wata Al-muwadda Privite University, babu ɓangaran da ba sa koyarwa. A tashin farko suna bawa ɗalibi zaɓi idan kai tsaye zai rinƙa ɗaukan darasi ko kuma ta online, saboda larurar Raihan ya sa Daddy ya cike mata karatu ta online. Duk wani abu da ya dace daddy ya yi mata, kuma ta ci gaba da karatunta daga in da ta tsaya. Wannan lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba ita da Mommy su Inno kuwa sai mita suke, wai ita dai a boko za ta ƙare kullin tana abu ɗaya gara ta fitar da miji ta yi aure. A kullin bayan la'asar Khalid zai fito harabar gidan ya yi ta karatuttuka daga na Alƙur'ani har zuwa sauran littafan addini, ganin yana da ilimi mai zurfi ya sa Mommy ta yi masa magana akan zai riƙa ƙara wa Raihan karatu idan ya so sai a ƙara masa albashi. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Kabiru ba kasancewar kuɗin da yake samu duk wata a wurin jinyar Mahaifinsa take ƙarewa, kuma a hakanma ba isar Mahaifiyarsa suke yi ba. Kuma ko da ganganci bai taɓa sanarwa da Daddy akan ya taimaka masa ba. Raihan sam bata da girman kai don haka duk yammaci take tafiya wurin Kabiru yana yi mata ƙarin karatu, don a lokacin ko izu talatin bata haɗa ba. Tun Kabiru yana ɗari-ɗari da Raihan ya fara sakin jikinsa da ita, don ta mayar da shi kamar kakanta kasancewarsa hausarsa ba ta daidaita ba yana magana za ka gane cikakken bafulatani ne. Da wannan take zolayarsa har take kiransa da suna Fillo, daga ƙarshe ma cewa ta yi bayan karatun addini har fillanci zai riƙa koyar da ita. Kwana Raihan biyu da fara ɗaukan Darasi suna zaune za su fara karatu sai ga Inno ta taho sanye da hijabi hannunta ɗauke da kur'ani. Raihan ta dube ta don ta fahimci sarai abin da Inno take nufi, tana shirin yi wa Inno magana ta ji Goggo ta ce.

"La'ilah'illahu Muhammada Rasulillahi Sallallahu AlaihiWasallam. Yanzu haka za ki min saboda Allah daga na ce miki zan fara ɗaukan darasi wurin Kabiru sai ki rigani?" Inno ta ja farar kujera ta zauna ta ce, "Shi dai karatu ba a yi masa masifa, ki bi a sannu Zinaru wallahi kika sa masifa ƙwaƙwalwarki ta ƙi ɗauka. Ina dalili don za a biya min karatu ki hau kaina da faɗa, Izifina goma sha biyar ke kuma kin ce goma Allah na tuba ko sauka sai na kusa shekara da yi kafin ki sauke." Goggo na daga wurin da take ta sauri ta ce, "Tuf tuf tuf bakinki ya sari ƙaton kashi, wallahi ko a albasu na haure izifi ashirin, sauka kuma kamar na yi na gama." Raihan ta kalli Inno ta ɓata fuska tana cewa, "To wai Inno wa ya ce ku zo a biya muku karatun?" Inno ta dubi Kabiru ta nuna shi da yatsa, Kabiru ya zaro ido don shi bai san lokacin da aka yi haka ba da shi ba, yana tsaka da tunani ya ji Inno ta ce, "Yanzu Kabiru samun ladan tsofaffi har sai an ce maka ka yi?" Kabiru yana murmushi ya ce, "Shi kenan Inno amma ku bari na gama biya mata sai na dawo kanku." Da wannan shawara ya samu ya shawo kan su har ya fara biyawa Raihan karatu, Goggo na ƙarasowa a ƙufule ta ce, "Wallahi idan ban yi wa mutum adda'u ƙwaƙwalwarsa ta toshe ba." Inno ta watsa wa Goggo harara ta ce, "Mutum yana surutu ana karatu idan ya zama daddawa babu abin da zai hana ni kai shi kasuwa na sayar, na sayi lamurje na sha na fitsarar da abin banza."

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

25

Goggo na jin haka ta zabura za ta yi magana Kabiru ya katse karatun da yake yi ya ce, "Don Allah ku yi haƙuri Goggo idan ana karatun alƙur'ani ba a surutu saboda muhimmancinsa." Inno ta sa hannu a saitin bakinta ta ce, "In dai ni ce kabiru an bar maganar har abada." Murmushi ya yi mata ita ma Goggo ta ja bakinta ta yi shiru, sai da ya gama biya wa Raihan karatu sannan ya biya wa su Inno kowacce ya yi mata ƙari daga in da ta tsaya. Suna cikin karatu Daddy ya shigo abin ba ƙaramin birge shi ya yi ba, karo na farko kenan da ya ji Kabiru ya matuƙar birge shi. Sai da ya yi musu sannu da hutawa sannan ya wuce gida. Yana shiga Mommy ta tare rungumo shi tana faɗin, "Daddy barka da zuwa." Zagayo da ita jikinsa ya yi haɗe da ɗora kansa a jikin wuyansa ya ce, "Zainabuna bakya girma." Mommy ta juyo wa ta yi ta kashe masa ido ɗaya ta ce, "Addu'a nake Allah ya kawo wa Raihan mijin aure ta tafi gidanta ta ba ni wuri ta yadda zan ci duniyata da tsinke." Daddy ya yi dariya yana faɗin, "A gaban su Inno?" Mommy ta ɗaga masa kafaɗa cikin nuna rashin damuwa ta ce, "Su Inno tuni ai sun zama Kakannina don budurin da suke yi, yadda ka san a gidan Raihan haka suke yi." Daddy ya yi dariya har da ƙyaƙyatawa ya ce, "Ai ko baki faɗa ba na sani don diramar su Inno sai mai haƙuri ne zai iya jurawa." Ɓangaren Daddy suka wuce ta taimaka masa ya shiga wanka bayan ya fito suka ci abinci.
Chapter 46 · 0% Book details