← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 110

Sashe 109

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asubar fari jikin Kabiru ya rikice a dadddafe gari ya waye Daddy ya da su Inno wuro suka wuce da Kabiru wurin Malam, don tuni dama Daddy ya kira Malam ya sanar masa abin da yake faruwa. Suna zuwa bayan da Malam ya shigo Kabiru ya ce, "Assalamu alalikum." Malam ya amsa masa sannan ya ce, "Malam Ibrahim lafiya ka tayar da bayin Allahn nan ido biyu?" Kabiru ya amsa da cewar, "Lafiya ba lau ba. Domin tare muke da Huzaifa, mun yi gwagwarmaya mun yi artabu da shi har Allah ya ba ni nasara akansa na kamo shi." Malam ya faɗaɗa fara'arsa ya faɗin, "Kai Alhamdulillah. Huzaifa sai ga ka an kamoka ina cin alwashin naka?" Huzaifa ya yi dariya sannan ya ce, "Ba zan taɓa karaya ba wallahi, Ɗanka Aminu ya kusanci matata ya shiga gonar da bata tashi ba wallahi sai na kashe shi kamar yadda na Kashe Alhaji Shatima, salati Malam ya ɗauka ya ce. "Dama kai ne ka kashe Alhaji Shatima?" Huzaifa ya amsa. "Tabbas ni ne, aurenta da Al'amin ni na kashe shi saboda na bi duk hanyar da zan bi don na cutar da shi amma hakan ya ci tura don haka na ɓullo ta hanyar makirci, kuma na yi amfani da zafin zuciya da ƙiyayayyar da yake yi mata, don haka a duk lokacin da Raihan za ta yi wani kuskure zuciyarsa za ta hauhawa har ta ka ga na yi duk abin da na ga ya fiye min har ya sake ta. Da farko ban yi niyyar kashe Alhaji Shatima ba saboda bai aureta saboda yana son zama mai ɗorewa da ita ba, ya aureta ne don cin dukiyar mahaifinta. Ni kuma sai na ci alwashin talauta shi na fara saka masa gobara a gidan gonarsa, so na yi na mayar da shi matsiyancin ƙarfi da yaji. Kwatsam sai ya samu nararsa kusantarta don tun a daren da ya yi niyyar kusantarta na so halaka shi ƙarfin addu'a da tasirinta ne ya hana ni, na so na wahalar da shi kafin na kashe shi don haka na ga ɓatawa kaina lokaci ne saboda haka na jefa motarsa gidan mai suka ƙone ƙurmus." Huzaifa na rufe baki Ibrahim ya ce, "Shi kuma Aminina me ya yi maka da ka ɗauke masa ɗansa?" Kai tsaye Huzaifa ya amsa, "Kulawa ce ta sa, saboda yana ƙaunarta kuma yana matuƙar bata kulawa ni kuma ya sa na ji ina kishin haka, kuma duk hanyar da zan bi don na cutar da shi na kasa saboda mutum ne shi mai riƙo da addini shi ya sa na fakaici matarsa watarana ta fito fitsarin dare ba tare da addu'a ba na sauya mata shi na ɗauke wancen na binne shi da ransa. Wallahi kamar yadda na faɗa da farko hatta mahaifinta ba don na san babu aure a tsakaninsu ba irin kulawar da yake bata da tuni na gama da shi." Ran Malam ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ya ce, "Waɗannan abubuwan da ka yi zalinci ne ka hana yarinya zaman aure kana zalintar mutane kai wanne irin mara imani ne? A yau ba sai gobe ba zan ƙoneka domin kai ba irin sheɗanun da za a bawa zaɓin tuba ba ne, kai azzalumi ne ba za taɓa tuba na fahimci ba ka da rabo." Huzaifa ya bushe da dariya tare da furta, "Ba zan tuba ba matuƙar addinin musulunci kake so na karɓa domin babu addinin da na fi tsana sama da shi, kuma tun a daren jiya na ci alwashin zan kashe kaina na kashe Raihan domin babu amfanin zamanmu a duniyar, don ba zan iya rayuwa a doron ƙasa na ganta tana rayuwa da wani Ɗa namiji a matsayin miji ba ni ba, Raihan tawa ce ba zan taɓa barin rayuwarta ba matuƙar ina duniya tana duniyar. Da ace za ku mallaka min ita zan amshi musulunci saboda soyayyar da nake yi mata, amma matuƙar ina raye Raihan ba za ta taɓa zaman aure lafiya ba in dai ba ni za ta zauna ba." A fusace Malam ya ce, "Ai kuwa ka yi karya a mallaka maka Raihan domin ita ba jinsinka ba ce, don babu wata soyayya tsakanin mutum da aljan don haka har abada ba za ka same ta ba." Huzaifa ya ce, "Eh ba jinsina ba ce kuma yanzu haka ba ita kaɗai ce matata ajinsin bil'adam ba amma na fi jin soyayyarta don ita a wurina ta musamman ce. Matana goma na jinsinku. Ta ɗaya na aure ta saboda rashin addu'ar kwanciyar bacci na shiga jikinta don a duk lokacin da na rasa Raihan a wurinta nake yada zango na biya buƙatata, ta biyu saboda idan tana al'ada daina duk wani azkar take yi hatta ta shiga banɗaki irinmu kuma dama haka muke so. Ta uku na shiga jikinta saboda yin charting ɗin tsakiyar dare domin kullin idan ta yi charting ta gama wayar ma hannunta take ko data bata kashewa bacci yaka awon gaba da ita. Ta huɗun kuwa matar aure ce bata da aiki sai yawo da ɗaurin ƙirji a cikin gida kai ba ɗankwali ni kuma surarta ta burge ni kawai na shige jikinta don yanzu haka rabonta da mu'amala da mijinta kusan wata huɗu kenan, shi mijin na rage masa sha'awarta ita kuwa dama na cire mata sha'awar komai a ranta. Ta shida budurwa ce amma har ta fara manyanta domin na saka mata baƙin jini babu wani namiji da take birgewa har ya ji yana ƙaunarta, ita kuma na aureta ne saboda shigar tsiraici da ƙarin gashin da take yawan yi burinta maza su kalli tsiraicinta. Duk da ina matuƙar son komai na Raihan amma kwalliyar Rukayya mai fidda surar jikinta ta fi jan hankalina saboda har waƙa take kunnawa ta yi bacci ni kuma na yi ta shan shagalina da ita. Ta bakwai ma matar aure ce kuma amarya ce na aureta ana gabda bikinta lokacin da Mahaifiyarta ta kaita wurin Malam Murtala akan a yi mata aiki akan mijin da za ta aura, ita dama na ci alwashin ba zan bari ta haihu ba, don yanzu haka watanta biyar da aure ɓarinta uku. Ta takwas kuma ƙanƙanuwar yarinya ce don bata fi shekara uku ba, mahaifiyarta bata ciki saka mata wando ba don sau tari na je wucewa zan ganta da yara suna wasa wani lokacin a gida wani lokacin a waje daga haka har al'aurarta ta birgeni tun ina wasa da wurin har na yanke shawarar aurarta yadda zan samu yadda nake buƙata. Ta goman kuwa yau kwanana goma da aurenta ciff wata ƴar matashiyar budurwa ce bata fi shakara sha biyar ba, saboda tsinanniyar ƙasanzatarta na aureta saboda Mahaifiyarta irin iyayen nan ne marasa kula. Tuni yarinyar ta fara Al'ada amma har ta yi ta gama uwar bata san ta yi ba, hasalima har yau uwar bata son ta fara al'adar ba. Kuma hatta ɓangarori na jikinta bata gyarawa kuma Mahaifiyarta bata sakata ta gyara, ga shi ko wankan tsarki bata iya ba. Wannan ƙarni da wari-warin jikinta ya sa nake baƙuntarta saboda mu ba ya damun mu tun da dama wurin najasa nan ne makwancinmu. To ka ga duk cikin matan nan nawa wallahi babu wadda nake jin ba zan iya rayuwa babu ita ba sai Raihan, Raihan jinina da tsokata ce ban taɓa son wani abu a duniya kamarta ba don Allah karka raba ni da ita. Don Allah Malam tun ina ganin mutumcinka karka shiga tsakanina da Raihan, Na so Raihan na ƙaunaceta ka barni da ita har ƙarshen rayuwata." Malam ya sauke ajiyar zuciya yana cewa, "Dole kuwa na rabaka da su ba Raihan kaɗai ba domin kana zalintar bayin Allahn da ba su ji ba ba su gani ba." Malam na gama magana ya yi bismillah ya ɗauki haramara ƙone Huzaifa. Taurin kai da taurin zuciya irin na Huzaifa bai sa ya saduda ko ya karaya ba duk irin azabar da yake ji a cikin jikinsa, abu ɗaya kawai yake nanatawa sunan Raihan. Da farko wata zuciyar har ta cewa Malam ya ɗaga masa ƙafa ko zai haƙura da rayuwar Raihan amma sai kuma ya tuna irin ɓarnar da taurin kan da Huzaifa yake da shi da zalincin da ya aikata nan take Malam ya ci gaba da buɗe masa wuta da ayar Allah, tun Huzaifa yana iya magana yana kiran sunan Raihan har ta kai ga ya yi laushi Malam ya ƙone shi ƙurmus. Goge gumin fuskarsa Malam ya yi ya furta, "Alhamdulillahi dukkan yabo sun tabbata ga subhanahu wata'ala. Wannan shi ne ƙarshenka domin matuƙar kana doron ƙasa ba za ka daina aikata ɓarna ba." Ibrahim ya ce, "Malam ni zan wuce don ni ma sai na yi jinyar jikina saboda irin raunin da Huzaifa ya ji min." Malam ya yi wa Ibrahim godiya sannan ya matsa daga jikinsa.

Wunin Ranar a a wurin Malam Kabiru ya ƙarasa sai da magriba sannan Malam ya sallame shi, bayan da Malam ya bawa Daddy magugunan ya ɗora da cewa, "Yarinyar nan Raihan ya kamata ta sake dagewa da addu'a tun da akan kunnenka kana jin rabe-raben matan da Huzaifa ya aura kuma kowacce ya kawo dalilinsa. Yawancin mata suna da saka ci don haka jinnu suka fi raɓar jikinsu, Allah ya sake kare mu ya tsare mu daga kaidinsu bakiɗaya. Daddy ya amsa da Amin.
Chapter 109 · 0% Book details