← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 110

Sashe 13

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihan kallon ramin ta yi da yake ci gaba da rozayewa ƙasar wurin na ruftawa, ya yin da ramin yake ci gaba da ƙara girma yana tunkaro wurin da take. A hankali ta riƙa ja da baya cikin rawar jiki, firgici da tashin hankali. Tuni hawaye ya wanke fuskarta ta ci gaba da yin baya ba tare da ta fahimci wurin da take jefa ƙafarta ba, bata yi aune ba ta ji wani dutse ya tokareta ƙasar da ke zaftarewa ta ƙaraso har wurinta har sai da ya rage bai fi taku ɗaya ba ta dakata bisa bin umarnin Huzaifa da ke cikin surar Mama Hasiya. Cikin kuka Raihan ta dubi shi tana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni, ban san abin da na yi miki ba kika kawo ni wurin nan alhalin mommy ta ce mini kin mutu." Huzaifa ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya ya fara takowa wurinta yana tafe yana zare sauran ƴan yatsun hannunsa yana zubarwa, kafin ya ƙarasa wurinta tuni ya tsinke yatsun hannunsa sai iya dungulmin kaɗai ya rage, daga guraben ƴan yatsun wasu baƙaƙen farata ne suka fara tsirowa a hankali har sai da suka fito zaƙwa-zaƙwa da su, ta cikin ramin ya shiga kamar ƙiftawar ido ya dira a gabanta cikin wata irin murya mai amsa kuwwa ya sake ce mata. "Ki biyo ni cikin ramin nan idan ba haka ba za ki dauwama a nan." Raihan ta sake girgiza masa kai tana cewa, "Don Allah ki mayar da ni wurin su Mommy." Baki ya buɗe zai fara dariya wasu dogayen fiƙoƙi suka fara fitowa, da sauri Raihan ta runtse ido tana ƙwallah wata razananniyar ƙara. Wata iska ta ji mai sanyi na ratsa jikinta a hankali ta buɗe idonta, ga mamakinta sai na yi ta yi wurin ya sauya mata ta ganta wani kogon dutse mai ɗauke da ƙananan bishiyu, a hankali ta fara takawa har zuwa bakin kogon dutsen don ta hango hasken rana daga bakin dutsen. Tana fita daga cikin dutsen ta fara gudu da iya ƙarfinta don ganin ta ceci rayuwarta.

Daga nesa-nesa ta fara jiyo kukan jarirai haɗe da haniniyar doki, a hankali ta fara rage gudunta don yadda ta lura hanyar da take tunkara a nan take jin sautin kukan jaririn na sake karaɗe kunnuwanta. Tana tafe tana waiwaye ta bata yi aune ba ta ji ta yi karo da wata murgujejejiyar hallita, hallitar riƙe take da wasu ƙananan jarirai masu surarta, tsayin hallitarta ya ninka ta sau biyu, tana da ƙiba sosai don kaurin cinyar hallitar ya yi kaurin Raihan sau huɗu. Tana ɗauke ƙafa da hannuwa irin na birrai sai ƙaton kai irin na dorinar ruwa. Bakinta tsayi gare shi idanunta kwala-kwala masu ɗauke da launin ja, Raihan na shirin ja da baya Hallitar ta ƙurawa Raihan Ido tana miƙa mata hannu alamar ta zo gare ta. Da gudu Raihan ta juya don ta koma cikin kogon dutsen, karaf ta ji ta yi karo da Hazaifa da ke ɗauke da surar Mama Hasiya sai dai kammanina sun sake munana.

Ajiyar zuciya ta sauke don ko ba komai ta ji daÉ—in ganinsa, hankalinta ya fi kawanciya da shi a kan na wannan mummunar hallitar. Hallitar na ganin Huzaifa ya É—auke Raihan sun koma zuwa kogon dutsen ta juya ta koma daga wurin da ta fita, Huzaifa ya saki malalacin murmushi bayan sun koma ciki ya zaunar da Raihan akan wani faffaÉ—an dutse, ya zauna a gabanta yana kallonta. Tana shirin yin magana ya katseta da cewar, "Kina son komawa gida?" Da sauri Raihan ta gyaÉ—a masa kai. Jinjina kai ya yi sannan ya ce, "Zan mayar da ke gida amma da sharaÉ—in..." Da sauri ta katse shi da cewar, "Na amince da kowanne sharaÉ—inki indai za ki mayar da ni gida."

Wannan jaririn hallitar ya ɗauko mata mai shige da siffar kunkuru ya ce, "Ya zama wajibi ki shayar da wannan domin shi ɗin jininki ne." Idanunta ne suka firfito waje ta ƙarewa hallitar kallo tana yamutsa fuska, bai saurari abin da za ta faɗa ba ya ci gaba da cewa. "Ya zama wajibi ki yanke alaƙarki da wannan yarinyar Intisar." A hargitse Raihan ta sake ɗagowa ta yi tana kallonsa don a duniya bata da aminiya sama da Intisar, bata da wacce tasu ta zo ɗaya sama da ita amma lokaci ɗaya ya ce dole ta rabu da ita.

*********

A haukace Daddy ya yi kan Kabiru ya rufe shi da wani mahaukacin duka, sai da ya gaji don kansa sannan ya janye Jabun Raihan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A cen gafe Kabiru ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya yana sauke numfashi cikin wahala, ɗagowa ya yi suka haɗa ido da Jabun Raihan a fakaice ta sakar masa wani malalacin murmushi ta fara motsa baki tana magana ba tare da ta wani ya ji abin da take faɗa ba. Duk maganganun da Jabun Raihan take yi a kannen Kabiru, ransa ne ya sake ɓaci ya dubi Daddy da yake jifansa da mugun kallo, cikin bagwariyar hausarsa ya ce, "Alhagi shi wannan yaron ba mutumin kirki ba ne, azzalumi ne so yake ya shushe ki." Daddy ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Kabiru naushi a baki ya ce, "Don uwarka a gabana kake ce min ƴata ba mutuniyar kirki ba ce, ina maka kallon mai hankalin ashe kaima ɗan iska ne, wallahi a yau ba sai gobe ba sai an rufe min kai na ga gatanka mahaukacin banza mahaukacin wofi." Raihan da ke maƙale da Daddy ta sake langwaɓewa tana ɗangale ƙafa. Alhaji Mustafa Indabawa ne ya dubi Daddy yana faɗin, "Abokina don Allah ka yi haƙuri, yanzu mu ƙarasa wurin da gawar yaron nan take." Kabiru ya yunƙura da kyar bakinsa na ɗigar da jini. Daddy na leƙa cikin ɗakin ya yi tozali da gawar Sulaiman, da sauri Daddy ya ja da baya jikinsa na tsuma don ba ƙaramin tsorata ya yi ba. Alhaji Mustafa shi ma yana leƙawa a zabure ya ja da baya har suna gware da Daddy. Lokaci ɗaya Daddy ya yi zuru-zuru hankali a tashe ya furta, "Wannan tashin hankalin ne ya faru a ɗakin Raihan?" Intisar da ƙarasowarta kenan ta amshe maganar da cewar, "Daddy tun da nake ban taɓa ganin maciji mai muni irin wannan ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyaya ya fara jinjina kai, suna nan tsaye macijin nan ya fara warware kansa daga jikin Sulaima. Ganin haka ya sa mutanen wurin suka fara darewa, Kabiru ne ya dafa ƙofar a hankali ya zura ƙafarsa ɗaya cikin ɗakin.

Kallon-kallo aka fara yi tsakanin kumurcin macijin nan da Kabiru, a hankali Kabiru ya fara karanta duk wata addu'ar tsari da ta zo bakinsa. A zabure macijin ya fara ja da baya Kabiru na sake tunkararsa, wani kofi Kabiru ya hango da ruwa a jarka da sauri ya ɗauka ya zuba ruwa a kofi ya fara karanta ayoyin tsari yana tofawa. Daddy ban da leƙe babu abin da yake yi. Kasancewar Jabun Raihan ta san irin soyayyar da Mahaifin Raihan yake yi mata ya sa ta kwaɓe baki a lokacin da ta ga Kabiru ya tasamman halaka Macijin da ubangidanta ya turo, ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin, "Daddy wuyana." Kabiru ya waiwayo yana kallonta, Daddy ya kai hannu kan wuyanta yana faɗin, "Mu je asibiti a duba ki, wallahi duk abin da ya samu ƴata ka kuka da kanka." Daddy ya ƙarasa maganar yana watsawa Kabiru mugun kallo. Raihan ta sake langwaɓewa ta ce, "Daddy don Allah a bar korar macijin nan kar wani ya ƙara mutuwa kawai ka kira fire service." Daddy ya kalli wurin da Kabiru yake ya ce, "Kai maza fito daga ɗakin nan kar kaima ka yi mana mushe." Intisar ta kalli jabun Raihan ta watsa mata harara, sannan ta mayar da kallonta wurin Daddy ta ce, "Daddy amma naga kamar macijin ya fara ja da baya mai zai hana a bari a ga ƙoƙarinsa..." Alhaji Mustafa ya katse ta da cewar, "Tabbas ni ma haka na gama ayyanawa don yaron nan kamar akwai wani taimako da zai yi mana." Kabiru bai bi ta kansu ba ya sake tunkarar wurin macijin, lokaci ɗaya ya watsa masa ruwan tofin hannunsa bakinsa na ci gaba da ambaton Allah. Nan take macijin ya faɗi gefe yana wani iri gurnani, zaburowa ya sake yi da niyyar kai wa Kabiru sara da sauri Kabiru ya watsa masa sauran ruwan da ke hannunsa. Wata dariyar farinciki Intisar ta saki don ko ba komai ta san an yi wa Mama Uwani illa, jikinsu Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ganin gwagwarmayar da suka yi tsakanin Kabiru da macijin.

Jabun Raihan ta sake kallon Intisar ta saki ƙwafa a takaice, ta so ace Huzaifa ya bata umarni da tuni ta nunawa Intisar iyakarta. A wahalce Kabiru ya sa hannu ya hanyo macijin, ya fito daga ɗakin fuskarsa ɗauke da gumi lokaci ɗaya Daddy ya ji Kabiru ya birge shi saboda jarumtar da ya nuna, wannan ne karo na farko da ya ji ba zai iya ɗaukan mataki a kan wanda ya taɓa gudan jininsa ba, saboda yana matuƙar son mutum mai dakakkiyar zuciya. Sai dai har lokacin yana jin haushin Kabiru saboda abin da ya yi wa Raihan a idonsa.

Kusan tare suka tarkata suka fito daga sashen, kowa da abin da yake faɗa. Kabiru fita ya yi da macijin can bayan gidan Daddy ya kai ya wurgar da shi, Daddy da kansa ya sa aka rufe sashen Raihan tare da cewar sai ya kira ma'aikata sun yi wa ɗakin feshin magani, a ɓangare ɗaya yana tunanin barinsu daga gidan gabaɗaya.

*************
Chapter 13 · 0% Book details