← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 110

Sashe 40

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ilahirin waɗanda suke wurin daga jinsin mutane har zuwa jinsin aljanu sun yi jigun-jigun don da alama yanayin da suke ciki ba mai daɗi ba ne. Abar bauta ce ta miƙe cikin tsananin fusata ta fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya tana jinjina kawunan jikinta, tana zuwa wurin wani dutse ta fara buga kanta da dutsen cikin ɓacin rai har sai da ta fara illata kanta. Hatsabibiya ta miƙe ta ƙarasa wurinta tana son taɓa ta don ta dakatar da ita amma tsoron abin da kaje ya zo ya sa ta tsaya daga baya tana faɗin, "Yake Abar bauta wannan ba ita ce mafita ba." A zabure Abar bauta ta juyo wannan karon bakinta har fidda amon wuta ya ce, cikin wata irin fusatacciyar murya ta ce, "Yana neman ruguza alƙaliman tsafinmu, cikin ƙasa da wuni guda ya yi mana mummunar asara. Na shafe dubannin shekaru ina burin cimma burina amma ya wargaza farincikina ya wargaza tasirina, me kuka ganin za mu yi me ye mafita a halin yanzu domin a halin da muke ciki Huzaifa ne ya kawai yake ba mu kariya, yana ba mu kariya ne saboda yana jikinta amma idan ba mu yi da gaske ba matuƙar ya fita daga jikinta ta mu ta ƙare gabaɗaya hallakar da mu za a yi. Don na lura wannan malamin da yake yaƙarmu da gaske yake ba da wasa ba, kuma yana da matsananciyar kariya da tuni mun dunfare shi mun gama da shi, sai dai na san ko karen hauka ya cije mu ba za mu yi gangancij yin haka ba don lokaci ɗaya zai gano mu kuma ya hallaka mu, tun da yanzu babu wanda ya san tana tare da mu hatta shi kansa Huzaifa." Mugaza da ke gefe ta yi shiru tana nazari don idan Huzaifa ya fita daga jikin Raihan tafi kowa farinciki, sai dai ita ma a halin da take ciki matuƙar ta ce ita kaɗai za ta gudanar da nata ɗaukan fansar za ta iya halaka, don yadda aka halakar da tsaunin abar bauta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba. Ta ci alwashin ko ba komai sai ta shayar da Raihan azaba ta hanata kwanciyar hankali kamar yadda ita ma ta hanata nutsuwa. Daga wurin da take ta miƙe tsaye ta fara magana, "Matuƙar ina raye Huzaifa ba zai taɓa barin jikin Raihan ba." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta cikin mamaki, ganin ta ja hankalinsu ya sa ta ci gaba da cewa, "Ƙwarai abin da na faɗa haka ne, Huzaifa ba zai bar jikin Raihan ba matuƙar ina raye domin daga nan zan je na sake tunzura shi akanta. Babu abin da ya tsana sama da na ce dole zai bar jikinta ko na furta kalma mara daɗi a kanta." Cikin jin daɗi Abar bauta ta matso ta rungumi Mugaza, abin da bata taɓa yi wa wani a cikin tsibirin ba. Mugaza ta yi shu'umim murmushi don ita kaɗai ta san manufarta ta gaya musu haka, a ganinta idan ta yi haka za ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Na farko za ta ƙara jefa soyayyarta da samun shiga a wurin abar bauta da ƙungiyar tsafinsu. Darajarta za ta ƙaru matsayinta zai ɗaukaka za ta zama ƴar gaban goshin abar bauta. Na biyu za ta ci gaba da hillatar Raihan har sai ta kai mizanin da take son aiwatar da mugun ƙudurinta a kanta. Nan take suka ci gaba da tattaunawa Intisar na ci gaba da yaudararsu da zantuka kala-kala don ta ga maganganunta ba ƙaramim shigar su ta yi ba.

"Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari sai a sakar masa ƙota, dama na gaya maka idan wani ya yi rawa an biya shi wani idan ya yi duka zai ci. Amma ba zan fasa gaya maka Raihan ta fi ƙarfinka, ka fita daga rayuwarta. Wai me za ta nuna min da kake neman salwantar da rayuwarka a kanta, idan ka mutu sun kashe banza sun kashe wofi fa. Ka ga an cuce ni da ƴaƴana akan wata sakarai." Mugaza ta yi maganar cikin zolaya da son harzuƙa zuciyar Huzaifa. Kallonta ya yi yana huci don ta kara wa Barno dawaki domin dama ransa a matuƙar ɓace yake kuma ta ƙara masa da wani. Gyambon jikinsa ya sa wani ruwan magani yana wankewa ta sake bushe wa da dariya a lokacin da idonta ya sauka a kan wata lafceciyar kuna a gefen kafaɗarsa, tana shirin magana ta riski muryarsa yana faɗin.

"Ki bar murna karenki ya kama kura, domin koda kura ta rame ta fi ƙarfin ƙosassun karnuka. Ba zan taɓa bari a raba ni da Raihan ba wannan alƙwari ne da na ɗaukar wa kaina, domin ita rabin jikina ce. Na yi sakankancewar da babu mahalukin da zai raba ni da ita, idan kuwa aka nemi halaka ni zan kashe ta kowa ya rasa don ko da na mutu gawata ba za ta iya jurar jin Raihan ta tare da wani namijin ba ni ba. Na yi rantsuwa da girma tsafi da hatsabibancin kakana idan na fito daga tsatson jinin hatsabibin kakana sai dai Raihan ta mutu babu aure, yanzu haka shiri zan sake yi na tunkari Malamin don sai ya fahimci a cikin jinsinmu ma rukuni-rukuni ne, domin wasu jinnun rako wasu suka yi duniyar ni da kike gani bil'adam bai isa ya ga bayana ba. " Daɗi ya ratsa zuciyar Mugaza don ko ta wannan fannin ta san ta yi galaba akansu, kafin ita ma ta fara dasa nata ɗaukar fansar.

Kafin fitarsu sai da Daddy ya jadaddawa Kabiru cewar duk wanda ya zo basa nan kar ya buɗe masa gida kuma ya ce masa kawai sun fita unguwa ne, Kabiru shi kansa ta maza yake yi don tun da ya ga an ɗaɗe an bar shi, shi kaɗai yake saƙa da warwara. Ganin tunanin banza na neman yi masa yawa ya sa ya ɗauro alwala fara tilawar Alƙur'ani. Su Mommy suna zuwa bakin ƙofar Waraka Islamic chemist Raihan ta coge, juyin duniya aka yi da ita ta fito ta ƙi. Kifa kanta ta yi a jikin kujerar mota ko ɗago wa ta kalle su bata yi ba balle su saka ran za ta kula su. Malam Usman bai yi mamaki ba don kusan masu irin matsalarta suna yin fiye da abin da ta aikata. Da kansa ya ƙarasa wurin motar ya tsaya, Raihan bata ɗago ba ta ci gaba da zama kamar yadda take. Malam Usman ya dafa jikin murfin motar yana faɗin, "Ka taso ka fito mu shiga ciki ta daɗi tun ban shigar da kai ta yanda ka ɓullo ba." Raihan ta ɗago da kanta ta kalli Malam da idanunta da suka rine kamar sabon barkono. Kamar ba za ta tanka masa ba sai kawai ta kalli wurin da Malam Usman yake tsaye ta tofar da yawu nan take wuta ta tashi a wurin. Baya Malam Usman ya yi yana jinjina kai don ya lura abin Huzaifa ƙara gaba yake ba baya ba. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tana daga gefe ban da hawaye babu abin da take yi. Malam Usman kira ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaransa ya basu umarni akan su kawo masa ruwan addu'a, suna kawo masa ya watswa wutar tare da Raihan ɗin gabaɗaya. A fusace Raihan ta kalli Malam tana cewa, "Malam karka bari na kai bango akan hukuncin da kake son yankewa a kaina. Meye haɗinka da yarinyar nan da kake son raba ni da ita ƙarfi da yaji? Na gaya mata matata ce ba zan fita ba ana dole ko so kake sai na illataka, tun da ban ji maganar Mahaifiyata ba kana tunanin kai da na haɗu da kai sama ta ka zan bi umarninka ne?" Malam Usman bai bashi ba amsa ba ya ci gaba da zuba masa ruwan addu'a yana nan tsaye ɗaya daga cikin yaransa suka kawo kasko da wuta aciki ya fara yi masa turare da habbatussauda.Cikin ƙaraji Huzaifa ya dubi Malam Ya ce, "Ya isa haka Malam mu je zan shiga." Matsa wa Malam ya yi sannan Raihan ta fito jiki ba ƙwari don Malam ya gama sagar da duk wani kuzarinsa. Kallon titi Raihan ta yi ta hango wata babbar motar da alama cike take da fetir, kukan kura Huzaifa ya yi ya faɗa kan tsakiyar titin. Don yanda ya ayyana wa ransa da ya bar jikin Raihan gara ya yi sanadin da za ta mutu, idan ya so kowa ya rasa.

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan lambar.0706 206 2624

21
Chapter 40 · 0% Book details