← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 110

Sashe 104

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A hargitse Alhaji Shatima ya furta, "Kai yaro saurare ni da kyau ka san da wanda kake magana kuwa." Dariya mai sauti ya ji an yi sannan aka ce, "Azarɓaɓin me kake yi haka Dattijo, indai ni ne da sannu za ka fahimci ko wanene ni." Daga haka ya ji ƙit an kashe wayar." Shiru ya yi yana kallon lambar, Raihan da ke gefe ta ɗago ta ce, "Lafiya kuwa Alhaji." Alhaji Shatima ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali don tuni hantar cikinsa ta kaɗa ya ce, "Wani sakarai ne ya kira ni yana yi min surutan iska da wofi, amma share kawai irin ƴan iskan gari ne." Sai da ya ajiye wayarsa ya fara naɗe hannun babbar riga ya ce, "Mutane ba su da hankali wallahi, sai kana cikin farinciki su nemi su dagula maka lissafi." Har ya kai bakin toilet wayarsa ta sake yin ƙara ya saki guntun tsaki ya furta, "Ƙyale ƴan wahala sa yi su gama." Banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala ya dubi Raihan ya ce, "My baby shiga ki ɗauro alwala." Ajiye mayafinta ta yi har ta gifta ta gefensa ya rungumo ya haɗe ta da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi jikinta ya fara rawa. Alhaji Shatima ya sakar mata kiss a kumatu sannan ta shiga banɗaki don ta ɗauro alwala. Yana zaune ya ga lambar Alhaji Tasi'u ta shigo wayarsa, da mamaki ya dubi lambar ya kai hannu ya ɗauka cikin shaƙiyanci ya ce, "Haba mutumina wannan lamarin akwai shiga haƙƙi fa, ka sa ni ko ina nan ina takara da miraja'a za ka kira ni yanzu..." Bai ƙarasa maganar ba Alhaji Tasi'u ya katse shi da cewar, "Wai baka san abin da yake faruwa ba ne Alhaji Shatima?" Gaban Alhaji Shatima ya yanke ya faɗi cikin hanzari ya furta, "Ban gane ba wani abu ne ya faru?" Alhaji Tasi'u ya ce, "Ga ƴan kwana-kwana can a gidan gonarka tana ta ci da wuta nima yanzu Hafuz ya shigo yake gaya min ya wuce ta hanyar ya ga abin da yake faruwa." Wani irin gumi ne ya riƙa tsattsafowa Alhaji Shatima, jiki da karkarwa ya ce, "Don Allah abin da kake faɗa haka ne?" Haushi ya fara kama Alhaji Tasi'u a daƙile ya ce, "Wai ina yi maka irin wannan wasan ne? Ai ko zan yi maka ƙarya ba zan yi maka akan wannan abin mara daɗin faɗa ba." Alhaji Shatima tun bai katse kiran ba ya wurgar da wayar ya fice a guje wurin harabar motarsa, yana shiga motarsa ya riƙa sakin horn har sai da Maigadi ya fito da sauri ya buɗe masa gate ya fice a guje. Yana fita Raihan ta fito da gudu don ta ji fitarsa ta samu mai gadi a tsaye da alama shi ma jimamin yanayin yadda Alhaji Shatima ya fita yake yi. Da sauri ta tambayi Maigadi wurin da Alhaji ya tafi, hannuwa biyu ya rungume sannan ya ce, "Wallahi Hajiya idan na ce ga wurin da Alhaji ya tafi na yi ƙarya, ina cikin ɗaki na ji yana zabga horn sai na fito na buɗe masa ya fice a guje." Jiki a sanyaye Raihan ta amsa sannan ta koma ɗaki ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido, dabara ce ta faɗo mata ta ɗauko wayarta ta kira lambarsa sai jin ringing ɗin wayar ta yi a bayanta. Tagumi ta zuba hannu bibbiyu tana jiran ta ji shigowar mijinta amma har ta fara gyangyaɗi bata ji motsinsa ba. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta, ta gabatar da shafa'i da wuturi sannan ta koma gado ta zauna tana nan zaune bacci ya yi awon gaba da ita. Sama-sama cikin baccinta ta ji motsin shigowarsa, da sauri ta zabura tana mutssika idanu ta kalle shi ta ce, "Alhaji ina ka je haka? Tun ɗa zu nake jiranka." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka ya zauna ya haɗa hannuwa biyu ya rafka uban tagumi, tana shirin sake yi masa magana sai gani ta yi hawaye na zuba bibbiyu a fuskarsa. A rikice Raihan ta dube shi ta ce, "Me yake faruwa ne Alhaji?" Zuciyarsa na zafi ya furta, "Gidan gonata gabaɗaya ya babbake da wuta, hatta dabbobi da tsuntsayen da suke ciki babu wanda ya tsira. Wannan wacce irin masifa ce a ce a daren Angwancina wannan bala'in ya faru da ni." Jikin Raihan ne ya yi sanyi a hankali ta furta, "Innalillahi'wainna ilahirraji'un. Addu'a za ka yi Allah ya sa haka ne ya fi alheri..." Tun bata rufe baki ba a zafafe Alhaji Shatima ya furta, "Alheri a gidan uban wa? Asara kamar wannan ta same ni ki ce Allah sa shi ne mafi alheri? Ko shanu kaɗai kin san guda nawa ne a ciki? Ko shanun da suka ƙone sun haure guda tamanin kar a zo ga raguna da ƙananan dabbobi." Shiru Raihan ta yi don ta lura kamar akanta yake shirin sauke zafin da ya ɗauko, a hankali ta bi gefen gado ta zauna tana nan zaune har bacci ya sake yin awon gaba da ita. Kiran asubar farko ne ya tashe ta, tana tashi ta hangi Alhaji Shatima ya ɓingire a jikin gado da alama shi ma a zaune baccin ya yi awon gaba da shi. Sai da ta ɗauro alwala ta yi raka'atanal fijir sannan ta fara tashinsa, a hargitse ya farka yana faɗin, "Ku yi sauri ku kashe shanu da awakin ciki za su ƙone." Murza ido ya yi da ya ji muryar Raihan tana faɗin, "Na ji masallaci sun kusa shiga ka tashi ka yi sallah." Guntun tsaki ya yi ya miƙe don wani irin haushinta yake ji uwa-uba ga ɓacin ran da yake damunsa. Yana dawowa daga masallaci wayoyin mutane suka fara shigo masa, mafi yawa daga cikinsu masu yi masa jajae ne. Daga cikin masu kira har da Daddy don tun cikin dare ya samu labarin faruwa lamarin, sai da ya yi masa jaje sannan ya ce zai tura masa da tallafin wasu ƴan kuɗaɗe don ya rage asara. Ba ƙaramin daɗi Alhaji Shatima ya ji ba haka abokanansa suka riƙa kiransa kowa da irin gudummawar da yake bashi. Wannan ne ya rage masa raɗaɗin zafin abin da ya faru don wunin ranar haka ya yi ta amsa wayar mutane, Nura da Abubakar ƴaƴansa ne biyu rak a duniya. Suna karatu a Sudan suma sun samu labarin abin da ya faru don haka suka kira mahaifinsu suka jajanta masa akan abin da ya faru.

Washegarin ranar haka ƴan uwa da abokan arziki daga ɓangaren Raihan zuwa na Alhaji Shatima suka riƙa zuwa suna yi musu jajaen abin da ya faru, gidan su bai sarara da mutane ba sai bayan la'asar sannan Raihan ta samu ta sake fesa wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda. Ranar da Raihan ta tare Al'amin ji ya yi kamar zai yi hauka saboda tashin hankali, hatta Sumayya ta fahimci abin da yake faruwa da shi don haka ta riƙa baya-baya da shi don ta tabbata idan bata yi da gaske ba sai ya sauke faɗan akanta. Haka daga ɓangaren Kabiru wani abu ya ji ya tsaye masa a rai don har ji ya yi kamar ya fice daga gidan saboda yadda duniyar ta yi masa zafi.
Chapter 104 · 0% Book details