Sashe 64
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ana gobe ɗaurin auren Kabiru da amaryarsa Dije su Raihan suka dira a garin su Kabiru da kwatance ta waya, duk sai kunya ta kama Kabiru da ya tuna irin katafaren gidan da su Mommy suke rayuwa a ciki ya duba nasu gidan, ya ga ko kwatan na Daddy bai kai ba. Haka su Inna wuro suka riƙa nannan da su Mommy don ɗaki guda suka basu gabaɗaya ita da su Inno. Shi kuma Daddy aka sauke shi a gidan Mahaifin Amarya wato yayan Baffajo. Raihan gabaɗaya ji ta yi kamar tana kewar Kabiru don kusan kullin tun tafiyarsa sai sun yi waya da shi wani lokacin idan Barista Huzaifa ya ji tana yawan ambatar sunan Fillon har haushi yake ji. A daren ranar da suka sauka bayan sun huta Kabiru da Raihan suka fito suna tafiya a cikin garin, don Raihan ta tilasta masa sai ya kaita gidansu amarya ta ganta. Amma a ɓangare ɗaya haka kawai ta riƙa jin ranta yana matuƙar ɓaci, ganin yanayinta ya sa Kabiru ya furta, "Lafiyarki kuwa fillo?" Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Ba komai Fillo, wai don Allah baka yi missing ɗina ba saboda Allah ace amini guda wai ko dai ka samu sabbin abokai ne Fillo?" Kabiru ya yi dariya zuciyarsa wasai don ko ba komai ta nuna ta damu da shi sannan ya ce, "Da gaske ne abin da kike faɗa fillo kin yi kewata?" Kabiru ya tambaye ta kasancewar ya gane me kalmar missing take nufi. Raihan ta taɓe baki cikin zolaya ta ce, "Wai fa har ka ji daɗi ko? To ni ma zolayarka nake yi." Ƙarasa maganarta ya yi daidai da zuwansu wani ƙofar gida da yara suke ta atisaye da ƙasa. Kabiru yana shirin aika yaro don ayi sallama da Dije Raihan ta dakatar da shi tare faɗin ita za ta shiga ta fito da amarya da kanta. Da sallama ta shiga cikin gidan, lokaci ɗaya suka tsaya suna kallonta saboda daga shiga da sautin muryar Raihan duk ta bambamta da ta su. Bayan sun amsa mata Raihan ta ce, "Ina Amarya Dije." Dije na jin haka ta mayafi ta rufe fuskarta, saboda tsananin kunyarta. Ras Raihan ta ji gabanta ya faɗi wani irin abu ya turniƙe zuciyarta. A hankali ta ƙarasa wurin ta ce, "Tare muke da angonki yana ƙofar gida mu je yana jiranki." Dije ƙin buɗe fuska ta yi sai ƙyar Raihan ta samu suka fito suna zuwa ƙofar gida hasken farinwata ya haske fuskar Dije. Wani abu ne ya sake taso wa Raihan amma sai ta kawar da kanta ta ci gaban da zolayar amarya da ango. Don ita kanta bata san dalilin da ya sa take jin haushin Dije ba, duk da wannan ne haɗuwarsu ta farko. Sun jima suna hira sannan Su Raihan suka yi mata sallama suka koma gida. A washegarin wayewar garin Juma'a aka ɗaura auren Kabiru da Dije akan sadaki Dubu hamsin, Daddy ne ya bayar da kuɗin bayan an gama abin da za a yi suka ɗauko hanya suka nufo garin Kano.
Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa, har Kabiru ya gama rayuwar amarcinsa da amaryarsa ya koma bakin aikinsa na gadi, a lokacin bikin Raihan saura bai fi sati biyu. Daga ɓangarorin nan biyu duka kowanne shirye-shiryen biki suke yi, Daddy shi kansa ya dage sai sayayya yake haka daga ɓangaren mommy abin ba a cewa komai. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har aka shiga satin bikin Raihan.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
35
Tun da bikin Raihan ya ƙarato kullin cikin ɓacin rai Kabiru yake, har sai da Raihan ta gagara haƙuri ta same shi a harabar gidansu. Wannan karon ma ɗaure fuska ta yi tamau kamar wata uwarsa ta nuna wata farar kujera da hannunta ta ce, "Zo ka zauna." Ba musu Kabiru ya ƙarasa ya zauna jiki babu ƙwari. Hannuwa biyu ta haɗa ta zabga tagumi tana zura masa ido sannan ta ce, "Fillo!" Yadda ta ambaci sunansa har tsakiyar kansa kallonta yi ba tare da ya furta mata koda kalma ɗaya ba sannan ta ci gaba da cewa, "Fillo me yake damunka?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Tabbas ina cikin damuwa, zuciyata na azalzalata domin furen da nake ƙoƙarin bawa ruwa ya bushe. Na jima ina ƙoƙarin ganin na mallaki ɗan itaciyar amma tuni bakin alƙalami ya bushe domin sama ta yi wa yaro nisa sai kallo sai hange daga nesa. Ki taya ni roƙon Allah da ya cire min sonta a cikin zuciyata domin babban goro sai magogin ƙarfe." Ran Raihan ba ƙaramin ɓaci ya yi ba a fusace ta dube shi ta furta, "Yanzu akan wata kake ɓata ranka a banza, ba na gaya maka ka cire ta a ranka ba tun da kullin cikin cewa ka rasa ta kake yi." Muryar Raihan ce ta fara rawa idanunta suka ciko da ƙwallah cikin rawar murya ta ci gaba da cewa, "Wacece wannan da ba za ka iya rabuwa da ita ba? A ina take? Me ya sa za ka takura rayuwarka a kanta, ka cire ta daga zuciyarka ko dole ne sai ka so ta?" Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan wanda ita kanta bata san dalilin zubarsa ba, jiki a sanyaya Kabiru ya kai hannunsa saitin zuciyarsa da take buga masa da sauri-sauri sannan ya furta, "Da ina da halin cire ta a raina da tuni na cire na huta da azabtacciyar soyayyarta, kamar yadda na gaya miki ki taya ni da addu'a shi ne mafita." Raihan ta miƙe a sanyaye sannan ta ce, "Shi kenan Allah ya kyauta." Taku biyu ta yi Kabiru ya ce, "Wai Fillo dama haka kike ji da ni? Gaskiya zan yi kewarki idan kika tafi." Raihan ta juyo ta taɓe baki sannan ta ce, "Kar ka min sharri haka nace maka?" Raihan na ƙarasa maganar ta wuce cikin gida. A ranar haka Raihan ta wuni duk jikinta ba daɗi, zuciyarta a dagule daga baya da ta rasa dalilin fushinta akan Kabiru sai da watsar da lamuransa ta ci gaba da harkokin gabanta.
Washegari kamar kullin Kabiru yana zaune a harabar gidan gefe ɗaya ga rediyo tana ta aiki ita kaɗai, a yadda ya nutsu za ka rantse da Allah sauraron ma'aikatan gidan redio yake amma a baɗini sam ba haka ba ne, hankalinsa da tunaninsa sun tafi duniyar tunani daban. Raihan ce tsaye a kansa ta kira shi ya kai sau uku sannann ya yi firgigit ya ɗago haɗe da sakar mata wani yalwataccen murmushi. Guntun tsaki ta yi ta ƙarasa ƙofar ɗakinsa ta janyo kujera ta zauna suna fuskantar juna, yana shirin yin magana Raihan ta ɗaga masa hannu fuska babu walwala ta ce, "Don Allah idan zancen wannan budurwar taka za ka min na yafe, tun da baka da aiki sai na begenta. Kuma wallahi idan ka cika ni zan kira ƙanwata Dije na gaya mata halin da ake ciki, don ba zai yuwu ka aje min ita a can Shanono ba ka zo kana begen wata." Da ido Kabiru ya bi Raihan yana kallon yadda take sauke kowacce kalma ɗaya da bakinta, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta juya masa ido haɗe da tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Fillo don Allah ba wannan ba, zuwa na yi kaban shawara game da bikin nan ka ga saura kwana huɗu, kuma Barrista ya ce yana son a yi dinner da wacce uwa ni kuma yanzu duk waɗannan abubuwna ba sa gabana." Raihan ta jim sai kuma muryarta ta fara rawa idonta ya ciko da ƙwalla ta ci gaba da cewa, "Ban sani ba ko za mu yi doguwar rayuwa da Barista don gabana faɗuwa yake ina jin tsoron kar wani abu ya faru da shi kamar yadda ya faru da Salim, Fillo soyayyar Salim a jinina take har yau na saka cire shi a zuciyata. Ranar ɗaurin aurena da take tunkaro ni a kullin na tuna sai gabana ya faɗi ina fargabar kar wani abu ya sake faruwa tun da shi ma na riga da na saki jiki da shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bashi ba, sai dai duk da yana jin zuciyarsa na ɗaci a game da aurenta bai hana shi ya lallasheta ba saboda yana matuƙar san ganin farincikin Raihan. Har cikin zuciyarsa ya ji baya ƙaunar aurenta da Barista Huzaifa amma ba shi da wata hujja ko wani dalili da zai sa ya furta wannan maganar, ta wani fanin kuma yana ganin kamar ya so kansa da yawa idan ya ce baya son Raihan ta yi aure domin rayuwar mace taƙaitacciya ce, kuma shi bai furta mata kalmar soyayya ba ai baya rugeje mata tata soyayyar ba.