← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 110

Sashe 102

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Auwalu na kaiwa Raihan takardar hannunsa mamaki ne ya kamata, a sanyaye ta karɓa don bata yi tsammanin ga daga wurin wanda takardar ta fito ba. Tana karɓa ta fara karantawa kamar haka: "Amincin Allah ya tabbata a gare ki, na zo ne domin na baki haƙuri a bisa zamantakewarmu domin har yanzu zuciyata ta gagara nutsuwa akan abin da na aikata miki. Na zo neman yafiyarki don Allah ki yafe min duk abin da na yi miki a zamantakewarmu ta baya. Saƙo daga Al'amin." Tana gama karantawa daga ƙasa ta hangi lambar wayarsa, hawaye ne ya ciko idonta tana jin wata irin kewa da ƙaunarsa ta mamaye mata zuciya. Rungume takardar ta yi a hankali ta furta, "Na yafe maka duniya da lahira Al'amin saboda kai na musamman ne a birnih zuciyata, na yafe maka saboda Allah, Allah ya yafe mana gabaɗaya." Ƙwallar idonta ta goge ta tashi ta shiga ɗakinta ta ajiye takardar acikin takardunta masu muhimmanci. A ranar kusan kwana ta yi tana tunane-tunane don soyayyar Al'amin sabuwar fil ta dawo mata a zuciya. Al'amin na fita daga gidansu Sumayya kai tsaye gidansa ya nufa, a hargitse ya fara birkice ɗakin Sumayya yana zazzage filonta sai ga layu sun faɗo, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa bi yana buɗe su yana karantawa shi abin ma zame masa ya yi tamkar a mafarki. Nan take wata nadama da kewar Raihan ta kama shi yana jin sam bai kyauta ba, don tun da yake a duniya zai iya cewa wannan shi ne abu mafi muni da ya taɓa aikatawa wato cin zarafi da wulaƙanta Raihan. Ranar Lahadi da dare Daddy ya kira shi bayan ya zauna Daddy ya fara yi masa magana, "Aminullah na kira ka ne domin na sanar da kai Kaza na taka ƴaƴanta ne ba don bata son su ba sai don ta koya musu zaman duniya ne, na yi maka hukuncin baya ne don na nusar da kai laifin da ka aikata sam baka kyauta ba, abin da ya faru tsakaninka da yarinyar nan Raihan ban ji daɗinsa ba sai dai ba ni da yadda za mu yi Allah ya rubuta ba za ku yi zama mai tsayi ba, a kullin a kodayaushe ka zama adali ko ba akan Raihan ba kai namiji ne ta yuwu za ka iya ƙara aure nan gaba don haka idan ka ce za ka fifita soyayyar matarka za ka kai kanka halaka. Ka shirya gobe idan Allah ya kaimu ka ɗauki matarka ku wuce gida don..." Da hanzari Al'amin ya furta, "Haka ne Daddy amma wani hanzari ba gudu ba gaskiya ba zan iya mayar da Sumayya gidana yanzu ba. Ita kuma Raihan wallahi na yi nadama Daddy Allah da dama sai na mayar da ita..." Dariyar Daddy ta katse shi sannan ya ce, "Dama ta riga ta wuce maka Aminu. Ita kuma matarka meye dalilin ƙin mayar da ita?" Al'amin ya furta, "Ba komai amma a ɗan bari sai bayan kwana biyu." Jim Daddy ya yi yana nazartarsa sannan ya ce, "Ban lamunce ba, maza umarni na baka gobe ka ɗauki yarinyar mutane ka mayar da ita tun da dama ni na bada umarnin ta wuce gidansu." Fitar Al'amin ke da wuya Daddy ya yi jim yana nazartar lamarin su Al'amin don ya san ruwa baya tsami banza. Kamar yadda Malam ya gaya masa washegari Al'amin ya je ya ɗauki Sumayya ita kanta ba ƙaramin mamaki ta yi ba, don ta fara fidda rai da sake komawa gidansa saboda tsananin fushin da ya ɗauka da ita, sai dai kallo ɗaya ta yi masa wani irin tsoronsa ya ɗarsu a zuciyarta don fuskarsa a tamke take babu alamar wasa. Suna zuwa gida ta shiga ɗakinta a sanyaye shi kuma ya faɗa ɗakin Raihan don tuni ya saka ƙaramar katifa a ɗakin yake kwana a ciki. Zaman Al'amin da Sumayya sai ya koma tamkar zaman doya da manja, saboda daga gaisuwa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu. Ko girki ta yi sai ya ga dama yake ci, idan abincin bai yi masa ba ya fita ya siyo takeaway tana kallo ya cinye.

BAYAN WANI LOKACI.

Abubuwa da dama sun faru Raihan ta cire komai a zuciyarta don haka ta kama kasuwancinta hannu bibbiyu, wannan ya sa ta mayar da jikinta ta yi kyau don babu wani abu da yake damunta domin ta fahimci idan so cuta ne haƙuri magani ne. Kabiru gagara haƙuri ya yi da soyayyar Raihan yana son ya tunkareta da maganar yana shakkun abin da kaje ya zo, domin a kullin yana duba matsayinsa da matsayinta don haka watarana ya samu Inno wuro don jin shawararta game da gabatar da soyayyarsa ga Raihan, sai da ta gama saurarsa cikin tashin hankali, tsoro da firgici ta furta, "Hai lallai Kabiru na yarda baka da hankali, yanzu saboda ka samu wuri har bawan Allahn nan ya taimake mu ya jawo mu jikinsa har za ka ce za ka auri ɗiyarsa? Kana cikin hayyacinka kuwa an ya Kabiru baka haukashe ba? Ka dubi ƴar mai arziƙi kamar wannan ka ce ita za ka aura? Aradun Allah ka na aikata wanna ɗanyen aikin ka san shan ruwanmu a gidan nan ya zo ƙarshe, a kull ka rufa mana asiri mu ci arziƙi mu bar arziƙi a mazauninsa." Cikin Damuwa Kabiru ya furta, "Inno wuro wallahi ba tun yau nake son yarinyar nan ba..." A harzuƙe Inno wuro ta katse Kabiru haɗe da yi masa daƙuwa tana faɗin, "Soyayyar gidanku Kabiru, wai yaushe mutanen birni suka lalataka har kake fitsara a gabana. Kwarankwatsa dubu idan Alhaji ya ji maganar nan sai ya kaika wurin Gunduman garin nan, idan baka yi sa'a ba ya sa a ɗaureka har igiya ta yi saura." Zuciyar Kabiru a dagule ya dubi Inno wuro jiki a sanyaye ya ce, "Yanzu shi kenan Inno haka zan haƙura da Raihan?" Inno Wuro ta wara hannuwa tana faɗin, "Eh ka haƙura da ita tun da dai aurenta ba farillah ba ne, muna hannun Allah muna hannun Alhaji shi yake yi mana komai a rayuwa. Idan kuma bijirewa maganata za ka yi ga ka ga hanya nan je ka Kabiru." A sanyaye Kabiru ya amsawa Inno wuro sannan ya fice daga ɗakin, can ɗakinsu ya wuce ganin yanayinsa ya sa Maryama ta fara tambayarsa amma fir ya ƙi sanar mata abin da yake damunsa, sai dai ta lura ransa a matuƙar ɓace yake.

Jim Daddy ya yi bayan gama jin jawabin Alhaji Shatima, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Alhaji ka san dai matsalar yarinyar ba sai na gaya maka ba, amma Alhamdulillah jikinta yanzu ya yi sauƙi babu wani abin da yake faruwa da ita. Kuma ban san daga ɓangaren ita Raihan ba ko yaya za ta amshi wannan maganar." Farinciki ya mamaye zuciyar Alhaji Shatima, ya dubi Daddy ya ce. "A yi mata a hankali ka san yara wani lokacin ba a tikasta su, kuma ba da faɗa ake yi musu magaba ba, maganar lalurarta wannan ai mai sauƙi ne Alhaji tun da ansan ciwon neman magani ai ba zai gagara ba." Daddy ya yi murmushi sannan ya ce, "Shi kenan Allah ya tabbatar mana da alheri." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Daddy ne ya raka Alhaji Shatima bakin mota suka yi sallama, yana komawa gida ya samu Mommy tana zaune a dianning da alama jiransa take. Bayan ya zauna ta fara zuba musu abinci tana cewa, "Daddyn Raihan tun ɗazu cikina yake kiran ciroma, har na yanke shawarar zuba abinci na ci don na san hirarku da su Alhaji Shatima bata ƙarewa." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Neman auren ƴarki ne ya kawo shi." Mommy ta yi murmushi don ta ɗauka zolayarta yake ta ce, "Alhaji Shatima da ba ƴaƴa maza ba wa zai nemarwa aure, ai gara ku nemi wata dattijuwar ku ba shi tun yau kusan shekarar Hajiya Asabe uku da rasuwa." Daddy ya ɗauki cokali ya fara cin abin ci sannan ya ce, "Allah da gaske Raihan yake so da aure." A hargitse Mommy ta ce, "Raihan kuma?" Daddy ya gyaɗa mata kai. Mommy ta ajiye cokalin hannunta cikin sanyin jiki tana ci gaba da cewa, "Amma kana ganin Raihan za ta amince da shi, duk da bai kaika a shekaru ba amma fa ya bawa Arba'in baya sai na ga kamar ya yi mata tsufa." Daddy ya saka dariya cikin zolaya ya furta, "Ni ma na yi tsammanin haka amma idan ta ga ya yi mata ai shi kenan, ba Alhaji Shatima ba ko yanzu ai zan iya ɗaukan budurwa don hango wata fillo a rugar su Kabiru." Mommy ta wurga masa hararar wasa sannan ta ce, "To zan yi mata magana na ji Allah ya tabbatar da alheri. Ai ba wani abu ba ne Daddyn Raihan ni da kaina zan haɗa maka laife ka ga MD ya samu mai raino." Dariya Daddy yake sosai don ya san halin Mommy macece mai kishi amma duk zafin kishinta ba za ta bari ka gane lagonta ba.
Chapter 102 · 0% Book details