← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 110

Sashe 96

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan Raihan ta fito daga wanka doguwar rigar Mommy ta zaman gida ta saka, har lokacin fuskarta a kumbure take ta ƙarasa falon. A inda ta bar su a nan ta koma ta same su, tana zuwa Daddy ya nuna mata kujera yana faɗin, "Zauna nan." Ta lura da Fuskar Daddy babu alamun wasa don haka jikinta ya yi sanyi, a takure ta zauna Daddy ya dube ta yana cewa, "Laifin me kika yi Al'amin ya sake ki don na san haka kawai ba zai sake ki ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba." Hawaye ne ya zubo mata ta kalli Daddy za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta. Murtuke fuska ya yi cikin tsawa ya ce, "Ba kuka na ce ki raira min ba amsa za ki ba ni idan ba haka ba, ranki ya yi mummunan ɓaci." Tun da take da Mahaifnta wannan ne karo na farko da ta gan shi a wannan yanayin ba, bakinta na rawa hawaye na zuba ta ce, "Wallahi ban san me na yi masa ba ina fitowa daga wanka na ji ihun Sumayya, zuwana wurinta ke da wuya sai kawai ya wanke ni da mari daga ƙarshe ya ce ya sake ni." Kafe ta da Ido Daddy ya yi tana rufe baki ya furta, "Kin tabbata abin da kike faɗa haka ne?" Raihan ta gyaɗa masa kai. Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe fuska Daddy na miƙe wa ta ciro wayarta daga cikin ɗan tofinta ta miƙe masa tana faɗin, "Audullahi ungo kira min Faruku." Da mamaki Daddy ya ce, "Inno wane Faruku kuma." Inno ta sake ɗaure fuska ta ce, "Faruku barista ɗan uwana za ka kira min wallahi mai hana ni ɗaure wannan fitsararren yaron Aminu sai Allah, saboda Allah baiwa aka kai masa zai rufe ta da duka ya korota kamar mara gata?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "To kawo akira shi." Daddy karɓa ya danna lamabar Inno ya kira don ya san idan ba haka ya yi mata ba, tun da ta hau sama ba za ta yadda da duk lallashin da zai yi mata ba. A kunnenta ta ji ƴar baturiya na magana, don haka ta ja dogon tsaki ta miƙa hannu ta karɓi wayar tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace shi dai Faruku a haka zai ƙare kullin waya a kashe." Daddy fita ya yi ya bar su Inno suna ta sababi. Ita kuwa Mommy baƙinciki goma da ashirin ne ya mamaye zuciyarta, don haka uffan bata tanka musu ba tana ayyana abubuwa da yawa a cikin zuciyarta. Da farko Daddy ya yi niyyar ya taka har gidan Malam ya same shi amma sai ya yanke shawarar kiransa a waya, ɗakin da yake saukar baƙi ya shiga ya zauna ya danna wayar Malam bugu biyu Malam ya ɗauka da sallama sannan ya ce, "Alhaji ɗazu muna magana ba mu ƙarasa ba." Muryar Daddy babu walwala ya furta, "Malam akwai ƴar matsala." Da sauri Malam ya furta, "Ta me fa?" Nan take Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa, salati Malam ya ɗauka ransa a matuƙar ɓace ya furta, "Yanzu haka Al'amin zai watsa min ƙasa a ido ban sani ba, ni Al'amin zai wulaƙanta ya nuna ban isa ba kenan?" Daddy ya ce, "A'a Malam abi lamarin a sannu kasan sha'anin yaran nan ka fara jin ta bakinsa ka ga sai a ji komai." Malam cikin huci ya furta, "Ina zuwa Alhaji." Malam ya kira wayar Al'amin ya fi a irga amma ba a ɗauka ba da yake ya saka ta a silient. A fusace ya shi ga motarsa kai tsaye ya nufi asibitin, saboda tsabar sauri gani yake hanyar na ƙara yi masa tsayi. Wurin da aka tanada saboda ajiye motoci (Parking space.) Ya ƙarasa ya ajiye motarsa, a gaggauce ya fito ya ƙarasa cikin asibitin tun daga nesa ya hango Al'amin a bakin wani ɗaki a tsaye. Al'amin na hango Malam hantar cikinsa ta kaɗa gabansa ya yi mummunar faɗuwa, Malam na ƙarasawa Ammi ta furta, "Malam har ka ƙaraso?" Bai tanka mata ba ya ƙarasa wurin Al'amin ya ɗauke shi da wani azababban mari, yana ɗago wa ya sake ɗauke shi da wani marin. Takaici, baƙinciki haɗe da baƙin rai suka sake mamaye zuciyar Malam. Ya dubi Al'amin a fusace yana faɗin, "Na gode Al'amin, na gode ka ji. Yanzu ka nuna min na haife ka ne amma ban isa da kai ba. Wallahi ka ji na rantse idan har ni na haife ka, ka je maza ka ɗauki ƴar mutane ka wuce gidanka da ita." Ammi da bata fahimci komai ba ta shiga tskiyar su Malam tana faɗin, "Me yake faruwa Malam?" Da hannu ya nuna mata Al'amin sannan ya furta, "Ki tambayi ɗanki zai gaya miki irin rashin mutumcin da ya aikata." Malam ya juya a fusace zai bar wurin har ya fara takawa ya juya ya ce, "Idan ka ga dama ka same ni a gida." Daga haka bai sake furta komai ba ya wuce ya shiga motarsa ya fice daga asibitin. Da tsananin mamaki Ammi ta dubi Al'amin ta ce, "Me yake faruwa Al'amin." Al'amin da hankalinsa ya fi na koyaushe tashi ya ce, "Ammi laifi ne don na saki Raihan alhalin cin amanata take yi, Ammi har fa maza take kawo min cikin gida amma kina jin abin da Daddy ya faɗa." Idanu ta zaro waje ta ce, "Innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un. Yanzu dai kar ka ɓata lokaci ka ga a yadda mahaifinka ya fita maza ka je kiran da ya yi maka." Amsa mata ya yi jiki babu ƙwari ya wuce wurin da motarsa take, Mahaifiyar Sumayya ce ta cika fam don ba ƙaramin haushi ta ji ba ganin irin abin da Malam ya yi wa Al'amin akan Raihan amma ko ta kan tata ƴar da take kwance bai bi ba. Lokaci-lokaci take kallon wurin Ammi tana wurga mata harara, suna nan zaune wata Nurse ta ƙarasa wurinsu ta ce za su iya shiga wurin Sumayya amma bata buƙatar hayaniya.
Chapter 96 · 0% Book details