Sashe 30
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kabiru tun fatar jikinsa na damunsa har abin ya fara zame masa jiki, watarana yana zaune a ɗakinsa bayan ya gama tulawar alƙur'ani, ya samu kofi ya karanta Ayatul kursiyyu bakwai falaƙi da nasi bakwai-bakwai sai ayatulkursiyyu da Amanarrasulu uku-uku kamar yadda ya saba kullin bayan ya gama tilawar alƙur'ani. Yana gama tofawa ya sha ya shafe jikinsa babu jimawa bacci ya ɗauke shi, ya jima yana bacci sai bayan wani lokaci ya farka kai tsaye ya ɗauki buta ya wuce banɗaki don lokacin har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar, ba ƙaramin mamaki ya yi ba na bacin da yai mai tsawo, bayan ya idar da sallah kamar wanda aka cewa ya kalli mudubi sai gani ya yi jikinsa fayau babu wannan fatar macijin, farincikinsa ne ya ƙi rufuwa sai shafa jikinsa yake yana sake duddubawa. Nan take ya faɗi ya yi wa Allah godiya bisa ni'imar da ya yi masa ta yaye masa wannan lalurar da ya yi, kamar wanda aka yi wa bushara da gidan aljanna haka Kabiru ya riƙa shige da fice cikin farinciki. Washegari har mai ƙosai ya kaiwa kuɗi ta yi wa yara sadaka don nuna godiyarsa ga Allah S.W.A.
Da mamaki Mommy ta dubi Rain don ta yi tsammanin har lokacin Raihan na cikin ciwonta, tana nan tsaye Daddy ya turo ƙofa yana ganin Raihan a zaune ya washe baki cikin jin daɗi ya ce, "My baby." Raihan ta yi wa Daddy murmushi sanna ta ce, "Daddy ina me wannan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna mayafin jikinta, hannuwa ya wara mata yana faɗin, "Ban san na waye na, ina jin na wata classmate ɗin taki ce..." Turo ƙofar da Intisar ta yi ya katse maganar Daddy, Raihan ta girgiza kanta ta ce, "Wannan ba na kowa ba ne sai na mijin da zan aura wallahi Daddy ina son shi." Lokaci ɗaya Mommy da Daddy suka zaro ido don wannan baƙuwar kalma ce da basu taɓa jin ta a bakin Raihan ba, ko a baya da samari suke nuna soyayyarsu gare ta ba su taɓa ji ko ganin ta nuna alamun soyayya ga wani ba. Daddy ya yi saurin cewa, "Wane ɗan baiwa mai rabon ne wannan?" Intisar da ke gefe ta furta, "Daddy wani mai rabo ne, don nima yau sai da ta yi min maganarsa." Mommy ta mayar da kallonta ga Intisar ta ce, "Au wai da gaske ne lamarin?" Raihan ta tura baki gaba tana faɗin, "Mommy da baki yarda da abin da na gaya miki ba?" Mommy ta sa hannu a baki ta kare ta ce, "Ina na isa na ce uwar maigari ta yi ƙarya." Gabaɗaya suka saka dariya, tiryan-tiryan Raihan ta yi masa bayanin yadda aka yi suka haɗu da Al'amin, sai da suka gama sauraronta Mommy ta ce, "To Yanzu Raihan daga haka ta haɗa ku da mutum bai ce yana sonki ba sai kawai ki fara son shi, shin ma ke kin tabbatar da wannan mayafin na shi..."
"Haba don Allah Zainabu yanzu ke ba murna za ki yi ba, kina gani duk saurayin da ya fitowa yarinyar nan ƙinsa take yi yanzu ba sai mu tayata so da neman yaron nan ba." Daddy ya katse Mommy cikin faɗa. Mommy ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta furta, "Daddy ka fahimci abin da nake nufi, shin shi yaron yana sonta ne? kawai daga haɗuwa bata san halinsa ba sai ta faɗa soyayya da shi?" Daddy ya ɓata fuska ya ce, "Ki bar batun soyayya idan kuɗi na magani zan nemar mata soyayyarsa a wurinsa, zan shi ga makarantar tasu na nemi wurin da yaron yake, ke kin tabbatar ɗan makarantar ku ne Raihan?" Raihan ta gyaɗa fuskarta ɗauke da murmushi don har ayyanawa take sun tsunduma cikin soyayya. Kwanan Raihan ɗaya aka sallameta saboda babu wani abu da yake damunta, a ranar ne Daddy ya fara binciken Al'amin sai dai ko mai kama da shi babu wanda ya ce ya sani. Wannan maganar ba ƙaramin ɗaga hankalin Raihan ta yi ba, hatta abinci sai mommy ta yi da gaske take samu ta ci. Ga binciken duniya da likitoci suka yi sun ce bata da wani ciwo sai matsalar damuwa (Depression) ce ta yi mata yawa, don haka za ta riƙa abubuwa kamar mara hankali ko shafar iska. Daddy na jin wannan bayanin ya hau kai ya ɗare har yana yi wa mommy ƙarin bayani dangane da ciwon, ita dai Mommy ta ji shi ne amma har zuciyarta bata aminta da maganar ba, daɗin da ta ji da likitan ya ce zai ɗorata a kan allurai wanda za a riƙa bata a kai akai, wanda za su taimka mata wurin rage halin da take shiga. Daddy na fitowa daga asibitin suka haɗu da Dr Muhsin sai dai duk lokacin da Daddy ya ɗago masa da zancen ciwon Raihan zuwa tafiyarsu India sai ya ji ya manta komai, sai dai ya yi ta yi wa Daddy kame-kame. Ganin haka ya sa Daddy ya haƙura ya daina yi masa maganar har ya yi tunanin sake mata wani likitan. Suna haɗuwa suka gaisa faram-faram Dr Muhsin ya tambayi jikin Raihan daga haka suka yi sallama, Daddy na shiga mota saƙo ya same shi daga hukumar makarantar su Raihan, daga harabar asibitin kai tsaye makarantar su Raihan ya wuce. Takarda suka aka bawa Daddy na dakatar da Raihan da aka yi daga makatantar har sai ta samu lafiya, wannan labarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Daddy ya yi ba. Lokacin da ya shiga mota har sai da ƙwalla ta zubo masa, zuciyarsa a dagule ya wuce gida yana zuwa ya sanarwa da Mommy abin da yake faruwa. Ita kanta bata ji daɗi ba amma sai ta fauwalawa Allaha lamuranta, tare da addu'ar Allah ya bayyana ainihin ciwon da ke daminta da hanyar warakarsa. A wannan lokacin Mommy ta dage sosai da sallar dare kuma tun abin da ya faru da ita a baya bai sake faruwa da ita ba, wani lokacin idan tana sallar dare har kuka take tana gayawa Allah buƙatunta don komai ya dagule mata, ga mitar da su Inno suke yi mata a kan yarinya ta girma babu tsayayyan miji, abu goma da ashirin ne ya haɗe mata.
Tun bayan dawowar Mama Uwani daga dubiyar mahaifiyarta duk ta sauya musu, hatta fara'a walawala da sauran abubuwan da take yi duk ya ragu, idan ba aiki za ta yi ko wani abin ba kodayaushe tana cikin ɗakinta. Da farko su Inno sun ɗauka jimamin rashin lafiyar mahaifiyarta amma daga baya sai suka lura da mu'amarce ta cikin jama'a bata so don haka suma suka ja baya da ita don tun suna tambayarta ko wani abu yana daminta ta ce a'a har suka zuba mata ido. Har bayan dawowar su Mommy ita kanta ta lura da haka amma sai ta yi mata uzuri kasancewar ɗan'adam ajizi ne yau da daɗi gobe babu. Amma abin na Mama Uwani ƙara gaba yake don yanzu ko aikin gida bata yi, wani lokacin Mommy ta yi ta ƙwalla mata kira amma fir ta ƙi zuwa. Wannan sabon yanayin da aka samu ya sa mommy ta fara tunanin ko gajiya Mama Uwani ta yi da aikin gidan, wata ranar laraba yamma liƙis Mommy ta ƙwallawa Mama Uwani kira tana zaune a falo yana kallo, sai bayan wani lokaci sannan Mama Uwani ta fito fuska babu walawa. Dama kuma Mommy ta kirata ne don ta tambayeta ko ta gaji da aikin a yi mata ihisani a sallameta a ɗauko wata. Ganin surar da Mama Uwani take ciki ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tun fitowara daga ɗaki ta fara ƙarewa ƙafarta kallo ƙirjinta na ci gaba da matsanancin bugu. Ilahirin jikinta rawa yake tun Mama Uwani bata lura da halin da Mommy take ciki ba har ta fara shan jinin jikinta, kallon idon mommy ta yi ta lura da wurin da take kallo nan take ta sauke kanta ƙasa tana kallon ƙafafuwanta, ganin Mommy ta gama ganin manyan kofatan dawakai ya sa Mama Uwani ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, Mommy na daga kan kujera ta fara ja da baya don bata taɓa tunanin haka daga wurin Mama Uwani ba. Ɗago kofatonta ɗaya ta yi tana nunawa Mommy ta ce, "Gane-ganenki ya kaiki ganin abin da zai hana ki bacci. Tun da kin gano da idonki zan fayyace miki komai, ni ba mutum bace kamar yadda kuka yi tsammani tsawon shekaru. Hasalima ni zaman maye gurin nake yi domin ba ni ce ainihin Uwanin da kuka sani ba, ni sunana Mar'usa ƙanwace a wurin Huzaifa wato mijin ƴarki Raihan. Ya ajiye ni ne don na maye gurbinsa saboda wata doguwar tafiya da ya yi, idan ku ba daƙiƙai ba ne baku lura ɗabi'armu da tashi ta sha bamabam ba? Shi ya zauna da ku shekara da shekaru yana yi muku bauta saboda matarsa a gidan nan take, ni kuwa da babu uwar da zan ƙaru da ita kina ganin zan zage na yi muku bauta. Shi ma aikin da kika ga yana yi ya fansar da aikin wahalar ne a matsayin sadakinta, tun da yanzu kin san komai ni zan yi tafiyata sai ki jirayi dawowarsa don ba zai barki haka ba." Tana rufe baki Inno na ƙaraso wa wurin tana shirin yin magana turus ta tsaya baki a sake murya na rawa ta ce, "Na shiga aljanna na kasa fitowa, Uwani kofato nake gani a ƙafarki ko idona ne?" Mar'usu ta turawa Inno kofaton tana faɗin, "Ni ba Uwani bace ita kanta uwanin da kuke tsammani ba mutum ba ce." Tana rufe baki ta ratsa ta jikin bango ta wuce, Mommy na zaune bata yi aune ba sai ji ta yi kijiffff Inno ta faɗi ƙasa tana faɗin, "Lahamakasabat Wa'alaina makasabat, hasbunallahu La'ilaha'illahu. Wa'innahumin Sulaimanu..." Da sauri Mommy ta yi kanta tana tarota Daddy da shigowarsa kenan ya ƙarasa wurin yana salati, hankalina tashe ya ce, "Lafiya kuwa Inno garin yaya." Inno da ta fita hayyaccinta ta ce, "Idan mafarki nake yi Allah ka farkar da ni, Ina Zinaru take ta riƙe ni mu shiga ƙofar aljanna, Kalidina fiha'abadan cikin aminci."
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
16