Sashe 61
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da ido Raihan ta bi su don ba Æ™aramin mamaki ne ya kamata ba, musamman ganin Barista da ta yi don sarai ta gane fuskarsa. MiÆ™e wa ta yi ta nufi wurin Daddy ta karÉ“i jakar hannunsa ta furta, "Daddy barka da zuwa." Tana amsar jakar Daddy ta kalli Dr Hussain ta furta, "Dr yau kai ne a gari?" Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Ba zuwana ba ne ni ma taso ni aka yi." Ya yi maganar yana kallon Barista haÉ—e da yin dariya. Raihan ta taÉ“e baki ba tare da ta kalle shi ba, tana niyyar wuce wa cikin gida Daddy ya ce, "Raihan ki kawo wa su Dr abin sha muna falon baÆ™i." Æata fuska Raihan ta yi don ko kaÉ—an ba ta so ba, murya can ciki ta amsa sannan ta wuce cikin gida. Daddy ne ya yi musu jagora suka wuce falon da Daddy yake saukar baÆ™i, bayan sun shiga Dr da Barista suka zube Æ™asa cikin ladabi suka gaida Daddy. Daddy ya yi mamakin wannan gaisuwa ta Dr Hussain don sun daÉ—e da shi kuma bai taÉ“a yi masa irin haka ba, kujera ya nuna musu ya ce, "Ga kujera ku zauna man kwa zauna a Æ™asa." Dr ne ya fara miÆ™e wa sannan Barista ya miÆ™e suka hau kan kujera. Da sallama Raihan ta shiga ta dire tiren hannunta wanda yake É—auke da ruwa da kayan lemuka, bayan ta ajiye ta sake fita ta shigo da wani farantin mai É—auke da kayan marmari ta ajiye, sannan ta fice daga É—akin. Daddy ya zuzzuba ya miÆ™a musu sannan ya É—ora da cewa, "Ai lokacin da ka kira ni Dr na fito daga office babu jima wa don haka ba ce kawai mu haÉ—u a gida, sai ga shi mun zo kusan lokaci É—aya." Dr Hussain ya yi murmushi sannan ya ce, "Alhaji dama wata magana ce tafe da mu don haka na ce ya dace mu fara samun ka da maganar hakan ya fi dace wa, wannan dai abokina ne tare muka taso tun muna Æ™anana shi ma É—an Kano ne daga baya da kowa ya samu aikin sai kowa ya kama gabansa. Sunansa Barista Huzaifa kuma haifaffan unguwar Kurawa ne, lauya ne a babbar kotun shari'ar musulunci da ke jihar Kaduna." Daddy ya sake kallon Barista Huzaifa yana jinjina kai sannan Dr ya É—ora da cewa, "Tun kwanaki lokacin da aka yi wa Hajiya aiki ya ga Raihan ya ji yana sonta da aure, don haka da ya same ni da maganar ya ce ya fi son ya fara samun mahaifinta ya sanar da shi kamar yadda ya fi cancanta. Cikakken sunansa Huzaifa Rufa'i Mustafa, amma ana kiransa da Barista Huzaifa." A firgice Daddy ya É—ago yana kallon Barista tare da furta, "Huzaifa!" Da mamaki duka suka kalle shi jin yanda ya ambaci sunan. Dr ya É—an sosa kai sannan ya ce, "Alhaji shi ne muka ce bari mu zo ba mu sani ba ko an yi mata miji." Daddy ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta, "Raihan ba a yi mata miji ba amma gaskiya ina buÆ™atar yin nazari sannan kuma sai na ji daga bakin yarinya." Barista Huzaifa ya jinjina kai sannan ya ce, "Babu damuwa Daddy Allah ya zaÉ“a mana abin da ya fi alheri." GabaÉ—aya suka amsa da Amin. Lemo kawai suka sha don sauyin da suka gani a tattare da Daddy ba Æ™aramin sanyaya gwiwarsu ya yi ba, ba su jima ba suka yi wa Daddy sallama suka wuce don shi Barista tun a lokacin ya fidda rai da samun Raihan saboda yanayin Daddy kaÉ—ai shi zai tabbatar maka da yana cikin É“acin rai. Suna fita Daddy ya yi cikin gida a lokacin har an fara kiran sallar Magriba, sai da ya yi alwala ya yi sallah É—sannan ya samu Mommy da maganar. Duk abin da Dr ya gaya masa game da Barista haka ya ba wa Mommy labari sannan ya É—ora da cewa, "Maganar gaskiya ba zan bawa yaron nan Raihan ba, ba don komai ba sai don yana É—auke da sunan wanda na fi tsana a duniya. Kin san komai game da Huzaifa yanzu kina ga wani zai zo mu bashi aurenta ne?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Don yana É—auke da suna Huzaifa ba zai zama aibu ba Daddyn Raihan matuÆ™ar mutumin kirki ne, yanzu don Huzaifa aljani ya cutar da Raihan sai mu ce duka masu Suna Huzaifa ba su da Hali kenan? Ka yi tunani sosai Daddyn Raihan kuma ka yi bincike tun da gidan iyayen Dr Hussain ba É“oyayyun ba ne ka ga kuwa shi ma gidansu Barista Huzaifa ba zai yi wuyar sani ba. Amma batun ka hana shi auren Raihan bai ta so ba, tun da shekarun yarinyar nan Æ™ara gaba suke yi yanzu a Æ™alla Raihan fa ta tafi shekara ashirin da huÉ—u." Daddy ba Æ™aramin gamsuwa ya yi da maganar Mommy ba don haka ya numfasa ya ce, "Shi kenan Allah ya zaÉ“a mana abin da ya fi zama alheri." Mommy ta amsa masa, "Amin ya rabbi. Addu'a ita ce mafita." Daddy ya karÉ“i Muhammad yana yi masa wasa sannan ya ce, " Zan sanar da Raihan idan ta amince sai na bincika wanene yaron, asalinsa da tarbiyyarsa." Mommy ta faÉ—aÉ—a murmushi sannan ta ce, "Allah ya sa mu ji alheri." Daddy ya amsa da amin.
A daren ranar Daddy ya sanar wa da Raihan abin da yake tafe da Barista, Raihan mamaki abin ya bata. Don haka ta cewa Daddy sai ta yi shawara tukunna, su Inno na jin wannan zance suka riƙa murna da farinciki Goggo har da guɗa yadda kasan an ce mata ɗaura auren Raihan aka yi. Washegari da yamma tana zaune a wurin Kabiru suna hira, don Kabiru shi ya zame wa Raihan babbar ƙawa duk wasu shawarwari a wurinsa take nema kuma yana bata shawarwari masu kyau. Tun da su Barista suka zo gaban Kabiru yake faɗuwa ya rasa dalili, fargabarsa ɗaya kar ace masa manema aurenta ne, amma da ya ga sun fito da wuri sai ya ɗauka kawai baƙi ne wani uzuri ya kawo su. Suna zaune Raihan ta dube shi ta ce, "Fillo shawara na zo nema!" Ras! Ya ji gabansa ya faɗi sai ya yi ƙarfin hali ya ce, "Ina jin ki fillo me yake faruwa?" Raihan ta ajiye lemon hannunta ta ɗora da cewa, "Ina mutanen da suka zo jiya? Ba ka lura da wani mai baƙar hula ba?" Da sauri Kabiru ya gyaɗa kai gabansa na ci gaba da faɗuwa, Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wai sona yake da aure shi ne ya zo ya samu Daddy da maganar kasan abokin Dr da ya yi wa Mommy Cs ne." Nan take Kabiru ya sauya fuska cikin yanayin damuwa, gudun kar Raihan ta harbo jirkinsa ya ce, "Ah kai masha Allah, Allah sanya alheri." Raihan ta ɓata rai ta ce, "Shawara da na zo ka bani ko ka ga ya yi ne." Hararar wasa ya yi mata sannan ya ce, "Malama ki ce kin faɗa sonsa kawai, to da za ki tambaye ni, ni zan zauna miki da shi?" Raihan ta yi murmushi cikin zolaya ta ce, "Ina za ka zauna min da shi na zauna da abina dai, kaima wataƙila kana can da amaryarka." Wannan maganar ba ƙaramin dagula wa Kabiru rai ta yi ba, cikin damuwa ya miƙe yana faɗin, "Fillo kin yi na lokacinki sai gobe." Raihan ta miƙe tana dariya don ita bata kawo komai ba ta ce, "Au yaji za ka min, shi kenan wallahi idan ni ce ina zaune za ka zo nemana." Tana gama maganar ta wuce cikin gida. Kabiru na shiga ɗakinsa ya fara kaiwa da kawo wa don zuciyarsa ba ƙaramin zafi take yi ba, shi kansa ya san Raihan ta yi masa nisa amma babu yanda zai yi don zuciyarsa har kullin azalzalarsa take ƙaunarta na ci gaba da ruruwa a ruhinsa.