Sashe 60
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Su Inno suna tafe sai kalle-kalle suke babu damar a zo wurin danja sai su hau mitar an tsayar da su, a haka suka ƙarasa asibitin har lokacin Daddy yana zaune. Shigar su Inno ya sa Daddy ya miƙe har zai fita Inno ta ce, "Audullahi dawo magana nake son yi da kai." Daddy ya koma ya zauna Inno ta ci gaba da cewa, "Audullahi saboda Allah me muka tsare wa ƴarka ta ɗauki karan tsana ta ɗora mana, ko don muna zaune a gidan iyayenta." Inno na gama magana Mommy ta waiga ta kalli Raihan saboda dama tun da ta gansu tare ta san za a rina. Daddy ya dubi Raihan rai a ɓace ya ce, "Raihan me kika yi wa su Inno?" Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Saboda Allah Daddy me zan yi musu kasan dai halin tsofaffin nan fa." Goggo ta yamutsa fuska ta ce, "To idan saboda zaman mu ai sai mu kama gabanmu ina dalili, daga mun ce za mu zo asibiti yarinya ta saka mu a gaba da jaraba." Daddy ya kalli Raihan ya ce, "Bata kyauta ba amma Inno ku yi haƙuri, ke kuma..." Daddy ya katse zance shi yana nunata da yatsa sannan ya ci gaba da cewa, "Idan kika sake kika ƙara sai ranki ya ɓaci." Inno ta gyaɗa kai sannan ta ɗora da cewa, "Audullahi duk ba wannan ba gaskiya mota za ka saya mana kowa ɗaiɗai, mu riƙa tuƙa abar mu muna zuwa inda ranmu yake so. Haka kawai kullin za ka fita a riƙa ja maka rai, shi kuma direban yaron can ba shi da saiti. Kullin ya zo a ɗame wando kamar zai tsage sai kace jikan Elinzabet, a'a raba ni da wannan lamarin don wallahi sumar kansa tsoro take ba ni ga wari kamar an buɗe shadda."Daddy sai da ya gama jin jawabin Inno ya ce, "Inno mota fa? Duk motocin cikin gidan ba su yi muku ba? Idan Abbati ne bai yi muku ba ai sai na sauya wani." Goggo ta ɓata fusta tana cewa, "A'a ka bar Abbati kar mu zama silar barin cin abincinsa, amma dai mota za ka saya mana ka koya mana. Don idan ka saka Raihanu ta koya mana alƙur'an wataran murje mu za ta yi kamar ƴaƴan boris."
Gabaɗaya mutanen ɗakin sai da suka saka dariya har Daddy don yadda Goggo ta yi maganar ne zai baka dariya, Daddy ya dubi Goggo ya ce, "Goggo yanzu dai don Allah ku ɗan tsahirta da siyan motar nan a bari Zainab ta samu lafiya jikinta ya yi ƙwari kun ga duk abin da zai zo daga baya mai sauƙi ne." Su Inno suka jinjina kai cike da gamsuwa sannan Daddy ya tashi ya fice. A ranar da yammma aka sallami Mommy saboda dama a ƙa'idarsu kwanan mace huɗu da yin Cs suke sallamarta idan har ita da Babynta suna lafiya. Komawar Mommy gida ƴan dubiya da barka suka riƙa zarya, suna zuwa sake ganin Mommy sai dai bata yi taron suna ba don ta ce ta wuce wannan lokacin, taron suna sai Raihan ta haihu. Mommy ta yi shar da ita gwanin birgewa ita da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya, Daddy ya so saka sunan Mahaifinsa amma gudun rigima tsakanin Inno da Goggo ya sa ya saka masa suna Muhammad. Kusan rainon Muhammad a wurin su Inno da Raihan ake yi don Mommy aikinta bayar da mama kawai. Wata ranar talata suna zaune da yamma suna hira; Muhammad a lokacin kwanansa arba'in cif, Raihan na rungume da shi sai kawai ta ji ina ma ita ma ace Muhammad Ɗanta ne. Ta ɗago ta dubi mommy ta ce, "Wallahi mommy Allah ya taimake ki ina gida da ban san ya za ki yi da rainon Muhammad ba, yanda yaron nan yake da rigima ba ƙaramin wuya za ki sha ba." Mommy ta kalli su Inno ta ce, "Yanzun ma ai bake kike min ba ga iyayena su suke min raino, dan gidanku da za ki ce haka da wa ya yi min naki rainon?" Raihan ta miƙe tsaye ta miƙa wa Goggo Muhammad ta ce, "Ai kuwa shi kenan daga yau kuwa na daina taya su." Tana gama maganar ta wuce bakin gate, sanye take da doguwar rigar abaya kanta yane da mayafi. Kujera ta janyo tana ƙawala wa Kabiru kira, yana fitowa ya hangota sannan ya janyo kujera yana fuskantarta ya ce." Don Allah fillo ki daina min kiran mafarauta." Raihan ta yi dariya sannan ta ce, "Ango! Ango!!" Tsaki Kabiru ya yi ya ɗauke kai gefe zai yi magana Raihan ta ce, "Wai ya shgalin bikin zai kasance? Sai wani basarwa kake ka zo mu yi shawara ko garinku ba a komai lokacin biki?" Cikin yanayin damuwa Kabiru ya ce, "Tun farko na gaya miki ba na son auren nan saboda akwai wacce na mallaka wa zuciyata. Amma me ya sa za ki riƙa tambayata akan shirin biki bayan kin san ba son auren nan nake yi ba, biyayya ce kawai zan wa su Baffajo." Ba ƙaramin tausayi ya bawa Raihan ba don haka ta ce, "Ba tun yau ba na tambaye ka, wacece ita a ina take? Idan ka na ganin ni na yi yarinta sai na sa mommy a maganar amma wannan kamar ka daɓa wa kanka ne." Kabiru na shirin yin magana ya ji an fara horn a bakin gate, da sauri ya miƙe ya buɗe ganin motar Daddy ce, sai wata motar da take biye da shi. A jere suka shigo har wurin parking space, Daddy ne ya fara fito wa sai Dr Hussain da ya fita daga tashi motar. Daga ɓangaren mai zaman banza Barista Huzaifa ne ya buɗe ya fito cikin farar dakakkiyar shadda, sai baƙar hula, baƙin takalmi da baƙin agogo ɗaure a hannunsa. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cikakken bafulatani ne, kayan jikinsa ba ƙaramin amsarsa suka yi ba don shi dama ma'abocin son ado da kwalliya ne.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
33