← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 110

Sashe 45

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciya Malam Usman ya yi yana furta, "Alhamdullah." Kayan aikinsa Yaransa mata suka shigo suka fara kwashe wa jin hamdalar da Malam ya yi ya sa su Mommy suka fahimci an yi nasara. Fitowa ya yi ya ce Malama Rahama da Mommy su shiga su taimaka mata don jikinta gabaɗaya babu ƙwari, a hankali Raihan ta fara kallon wurin tana ganin Mommy ta miƙa mata hannu. Mommy ɓoye ƙwallar idonta ta yi don kar Raihan ta fahimci abin da yake faruwa, ɗakin da Raihan take har da toilet a ciki don haka mommy ta taimaka wa Raihan suka shiga ta sauya kaya, kafin su fito Malama Rahama ta kunna garin habbatussauda. Da mamaki Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Mommy ina ne nan?" Mommy ya ce, "Raihan baki ji daɗi ba ne muka kawo ki nan amma insha Allah kina ƙarasa warware wa za mu koma gida." Jinjina kai ta yi sannan ta ce, "Ina Daddy fa?" Mommy ta yi murmushi ta ce, "Oh Raihan wannan rai naki yana son Daddy ƙila da ni ce ba za ki tambayi inda nake ba ko?" Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Kai Mommy wallahi a'a."

Abinci aka kawowa Raihan ta ci tana cikin ci Daddy ya shigo, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin ta samu lafiya. Ya jima a zaune sannan ya tafi office ɗin Malam don ya ce yana son ganinsa. Da sallama Daddy ya shiga bayan sun gaisa Malam ya fara yi wa Daddy bayani, "Alhamdulillah mun samu nasara ya fita daga jikinta, amma za ta ci gaba da zama a nan tana karɓar magani na tsawon sati guda. Sai dai ya zama dole a kiyaye wasu abubuwa kuma koda komawa gida kuka yi dole ne a riƙa kunna karatun alƙur'ani akai-akai, a hanata jin kiɗe-kiɗe da yawaita bayyana tsiraci. Ta riƙa zama da alwala kuma so samu a farko-farkon nan kar a riƙa bari tana kwana ita kaɗai a ɗaki don shi shaiɗani binbini gare shi fiye da yadda kake tsammani. Sauran bayanin zan yi muku ranar da za a sallame ta, don a kiyaye Allah ya bata lafiya." Daddy cikin jin daɗi ya ce, "Amin Malam mun gode ƙwarai Allah ya ƙara ilimi."

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624

24

A wannan lokacin ganin halin da Huzaifa yake ciki ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, da farko ta so share shi saboda kishin Raihan da yake cinta a zuciya amma da ta tuna mijinta ne kuma uban ƴaƴanta akan dole ta yakice komai ta ƙarasa wurinsa da yake kwance kamar gawa. A hankali ta ɗago shi ba shiri ya saki ƙara sakamakon wani irin raɗaɗi da yake ratsa cikin jikinsa, ganin halin da yake ciki ya karya zuciyarta lokaci ɗaya ta rungumo shi a jikinta ta fashe da matsanancin kuka. Sai da ta yi mai isarta ta ɗago shi cikin kuka tana faɗin, "Ina amfanin irin wannan rayuwar Huzaifa, me ya sa ba za ka tsaya a iya matsayinka ba? Dubi irin azabtarwar da aka yi maka duk akan yarinyar nan meye take da shi wanda ba ni da shi. Haka kawai za su kashe min kai su illata ka su cuci ƴaƴana, gaskiya ya kamata ka sauya rayuwa Huzaifa wannan ba hanyar ce mai ɓulle wa ba." Huzaifa bai tanka wa Mugaza ba kasancewar yana cikin wani yanayi mai wuyar fasaltuwa, taimaka masa ta yi ta gyara masa jikinsa sannan ta shiga jinyarsa.

Abar bauta hankalinta ya kai matuƙar tashi don ganin irin illar da aka yi musu lokaci ɗaya kuma aka fatattaki wanda suke ganin shi ne bango madafarsu. Taron gaggawa ta sake haɗa musu don sanin makamar abin da za su gudanar dangane da Raihan. Ilahirin ƴan tawagar ƙungiyar asirin sun hallara a wurin Intisar ce kawai bata samu halarta ba sakamakon jinyar Huzaifa da take yi, wannan uzurin da ta kawo bai sa ta samu wata matsala ba saboda abar bauta ta san abin da yake faruwa. Sai da ta ƙare musu kallo sannan ta fara magana, "Ya zame mana wajibi mu tashi tsaye don mu yi yaƙi da hannuwanmu, tabbas an cutar da mu kuma ba za mu bari wannan cutarwar ta tashi a banza ba. Malam Usman ya fatattaki Huzaifa idan muka zura kanmu a yanzu muma za a iya fatattakarmu, me kuke ganin shi ne mafita a gare mu?" Abar bauta ta wurga musu tambaya, aljani batoyi ya miƙe tsaye ya ce, "Ni a ganina mu afka musu lokaci ɗaya don sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi." Abar bauta ta jinjina kai ta kalli sauran haka suka riƙa tashi suna faɗar ra'ayinsu sai daga ƙarshe Hatsabibiya ta miƙe ta ce, "A ganina mu sararawa Raihan na tsawon lokaci matuƙar ba ma son kwaɓarmu ta yi ruwa, jinkirtawar da za mu yi ba shi zai nuna gazawarmu ba sai dai don mu samu damar da za mu farfaɗo da ƙungiya idan muka ce gaggawa za mu yi tabbas za mu iya tsintar talatarmu a laraba. Mu ci gaba da gina ƙungiya idan ya so daga baya sai mu yi zaman shawarar da za mu sake jawo Raihan cikinmu, kin ga kafin lokacin ƙarfinmu ya dawo muna da jajircewar da za mu iya tunkarar Raihan ba tare da wata matsala ba." Abar bauta na gama jin haka ta fara ɓaɓɓaka dariya saboda shawarar ba ƙaramin daɗi ta yi mata ba, don haka a lokacin ta bada umarnin a fito don a samo mata jarirai biyar sababun haihuwa, sai jinin tsofaffai uku da na matasan samari biyu. Kafin wani lokacin tuni an aiwatar da abin da ta buƙata, nan take suka farke musu kayan ciki suka sha jini suka ci gaba da harkokinsu da tunanin yadda za su gyara ƙungiya su sake ƙafata ta tsaya akan ƙafarta.

Jikin Raihan na ci gaba da samun sauƙi saboda yadda take samun kulawa daga cibiyar Waraka islamic chemist, tana cin abinci sosai babu wani abin da yake damunta. Akwai magugungunan da ake bata safe da yamma da turarrikan da ake yi mata haɗe da wasu mayuka da ake shafa mata masu haɗe da magani a jiki. Ita kanta Raihan sai da ta ji daɗin jikinta sakamakon jinta wasai da take yi, duk wasu miyagun mafarkai ta daina yi. Ta daina mafarkin an biyota da gudu ko wani namiji yana saduwa da ita, hatta ɓacin rai da take yawan jin haka kawai ranta na ɓaci ta daina. Wannan sauyi da ta samu ba ƙaramin faranta zuciyar su Mommy ya yi ba, Daddy ne kaɗai yake komawa gida ya kwana shi ma a ranar farko da ya koma tsoro ne ya fara kama shi, sai da ya ɗauko laptop ɗin Mommy ya kunna karatun Alƙur'ani sannan ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi. Haka ya ci gaba da zarya daga gida zuwa wurinsu Raihan duk wasu harkokinsa ya dakatar da su, don ko fita ya yi hankalinsa na wurinsu. Su Inno da suke garin Albasu ta waya suke kiran mommy ko ta kira su, don su ji sauƙin jikinta. Yadda suka ji jikinta ya yi sauƙi ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba. Satin Raihan guda Malam Usman ya basu sallama, a ranar da za su tafi Malam ya jima yana yi musu nasiha da cewar:

"Masha Allah, dama an ce komai ya yi farko zai yi ƙarshe amma don Allah ina so ku bani aron kunnuwanku. Duk abin nan da ya faru da Yarinyar nan dama can rubutacce ne a wurin Ubangiji, amma kun san komai yana da sanadi." Lokaci ɗaya Daddy da Mommy suka gyaɗa kai sannan Malam Usman ya ci gana da cewa, "Kun yi sakaci matuƙa dangane da tarbiyar yarinyar nan musamman kai Mahaifinta, a mafi yawan maganar da Aljanin ya yi duka idan ka tattara maganganunsa yana nuna cewar kai Mahaifinta kai ne ka fi bashi goyon baya wurun samun zama a jikinta, ya nuna gazawar addu'a ƙarara don haka yanzu dole ku zage dantse. Duk Ɗan da ka gani yana da iyaye kuma duk iyayen da ka gani suna ƙaunar ƴaƴansu, amma muddin muka bari soyayyarsu ta rufe mana ido dole watarana kwaɓarmu za ta yi ruwa, kuma dama an ce ka so naka duniya ta ƙi shi ka ƙi naka duniya ta so shi. Idan har muna son ƴaƴanmu su taso da tarbiyyar koyarwar gidan Manzo dole mu tsaya kai da fata akan tarbiyya irin wacce addini ya bamu, daga ƙarshe ina mai ƙara jaddada muku da sa ido sosai akan yarinyar nan don kar wannan la'anannan ya sake bijirowa a jikinsa. Ina roƙon Allah ya bata lafiya ya tsare dukkan ƴaƴan musulmi kuma ya fito mata da miji nagari." Mommy da Daddy cikin haɗin baki suka amsa da Amin, suna sake yi masa godiya sannan suka yi sallama suka tafi.
Chapter 45 · 0% Book details