← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 110

Sashe 78

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da ladabi Kabiru ya jinjina kai yana cewa, "Babu komai Daddy na amince duk da ban san akan abin da ka yanke shawara ba, amma ina fatan ya zame min alheri domin na san ba za ka yi min zaɓen tumun dare ba." Murmushi Daddy ya yi saboda nutsuwa da ɗabi'un Kabiru na matuƙar birge shi, dafa kafaɗar Kabiru ya yi sannan ya ce, "Allah ya yi maka albarka na gode da wannan karramawa da ka yi min. Da ma ba wani abu ba ne na yake shawarar canza maka wurin aikine, ina son na kai ka kamfanina ku riƙa aiki da sauran yarana saboda na yaba da ƙwazo, hankali da riƙon amanarka. Tun da nake babu mai gadin da ya jima yana yi min aiki kamar kai, Kabiru jin ka nake tamkar ɗan cikina saboda irin girmamawar da kake yi mini da girman da kake ba ni. Idan baka manta ba na sha gwada ka na zubar da kuɗi a harabar wurin nan don na ga yadda za ka yi da su, amma sai ka yi sallama da ni ka dawo min da abina. Allah ya yi maka albarka Kabiru ya jiƙan mahaifa." Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba har ƙasa ya tsugunna ya fara yi wa Daddy godiya, ɗago shi Daddy ya yi ya ce, "Na hana idan na yi maka wani abu ka fara yi min godiya. Sannan wani hanzari ba gudu ba, na ce mai zai hana ka dawo da ƙaninka autanku ya maye gurbin aikinka idan ya so su Inno wuro sai a gyara musu ɓangaren da yake kallon na su Inno su zauna." Kabiru na jin haka ya fashe da kuka tare da ruƙo hannun Daddy yana cewa, "Ba ni da bakin gode maka Daddy domin ka yi min komai,har na rasa mai zan ce maka Allah ya saka da alheri ya ja ran tsohuwa ya jiƙan mahaifi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alheri duniya da lahira." Daddy ya yi murmushi ya amsa da "Amin." Motarsa ya buɗe ya shiga Kabiru ya buɗe gate sannan Daddy ya fice daga gidan, Kabiru cike da murna ya faɗa ɗakinsa ya ciro wayarsa ya kira Inna wuro ya sanar mata. Ita kanta ba ƙaramin farinciki ta yi ba, Kabiru saboda farinciki haka ya fara kai kawo a ɗaki. Raihan ita ta faɗo masa a rai yake jin ina ma tana cikin ƙoshin lafiya, da bayan Inna wuro ita ce mace ta farko da zai fara sanarwa. Sai kuma ya sauya fuska cikin damuwa domin ya san ba ƙaramin ciwo ne zai sa Raihan ta daina fitowa wurinsa ba, hasalima ya kira wayarta ya fi a irga amma koyaushe zai jita a kashe. Maryama ya kira ya sanar mata hukuncin da Daddy yanke da kuma ci gaban da suka samu, ita ma ba ƙaramin daɗi ta ji amma amma a yadda ya ayyana su Inna wuro ba za su dawo ba har sai Allah ya sauki Maryama lafiya saboda cikinta ya kai kusan wata bakwai. Yana son ya yi sallama da Mommy don ya duba jikin Raihan kuma ya yi mata godiya game da abin da Daddy ya yi masa, amma ya rasa yadda zai yi don haka ya yi ta maza ya yi sallama a ƙofar falon lokacin shiru falon da alama ba bu kowa a wurin, a daidai lokacin Raihan ta ɗauko Apple akan Dianning saboda bata iya cin komai, shi ma sha'awarsa ta yi shi ne ta ɗauko za ta wuce ta ji sallamar Kabiru. Tana tafe tana dafa bango saboda jirin da yake ɗibanta ta ƙarasa muryarta can ƙasa ta amsa masa, da ido ya kafe Raihan saboda tsananin mamakin irin lalacewar da Raihan ta yi lokaci ɗaya. A sanyaye Kabiru ya ƙarasa wurinta ya furta, "Me yake damunki haka Raihan? Kin ga yadda kika koma kuwa?" Kamar ya tunzurata ta ji zuciyarta ta sake rauni hawaye ya ciko idonta, a hankali ta jingina da bango jikinta har rawa yake saboda yadda yunwa ta ci ƙarfinta, ga rashin ƙwarin jiki da tsananin ciwon ƙirji da take fama. Lumshe idanu ta yi ta furta, "Ka ta ya ni addu'a Fillo saboda rayuwata na cikin wani yanayi." Hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya sake yi ba, har ji yake ina ma yana da ikon taɓa wani ɓangare na jikinta da ko ba komai ya ruƙo hannunta ya lallasheta domin ya ji ainihin abin da yake damunta. Takawa ya yi zuwa gabanta ya ce, "Gaya min abin da yake da mun ki ko ina da ikon taimaka miki." Girgiza masa kai ta yi hawaye na zuba ta ce, "Za ka iya taimaka min da addu'a fillo domin ita kaɗai ce abin da za ka iya tallafa min da ita." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Zan yi ƙoƙari matuƙa na yi miki addu'a daidai bakin gwargwadona amma a dukkan lamuranki ki riƙa neman zaɓin ubangiji, domin shi ne zai yi miki zaɓin alkairi. " Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan ta gyaɗa masa kai ba tare da ta iya furta masa komai ba, da ido ya raka ta yana jin zuciyarsa babu daɗi. Kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Kabiru ya wuce ɗakinsa ya zaune haɗe da faɗawa duniyar tunani.

Daddy yana tafiya hanyar office wayar Malam ta shigo masa, sai da suka gaisa sannan Malam ya ce idan ya samu lokaci yana son ganinsa. Jin haka ya sa Daddy ya fasa zuwa office ɗin ya wuce wurin Malam don jin maganar da yake son yi masa, bayan ya ƙarasa cikin girmama juna suka gaisa sannan Malam ya ce, "Alhaji dama na kira ka ne game da maganar hatsabibin Aljanin nan." Daddy ya tattara hankalinsa wurin Malam yana jinjina kai. Malam ya ci gaba da cewa, "Wannan Aljanin na jima ban haɗu da hatsabibin junnu kamar shi ba, ka san ya ci alwashin gujewa kusanci da mu don buƙatar kansa. To na tura wasu aljanu su kawo min shi amma ya yi musu ƙafar rago ya rufta su ciki, intaƙaice maka dai waɗannan aljanun ya yi garkuwa da su. Domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, saboda Huzaifa ya samu ɗaurin matsayi a wurin Kakansa Jabbul-ƙasi don haka sai na tashi sosai na yi shiri kafin na sake tunkararsu. Na san waye Jabbul-ƙasi ina da tarihinsa sama da shekara talatin baya." Zaro ido Daddy ya yi ya ce, "Dama suna garkuwa da junansu?" Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ai Alhaji duk yadda kasan muna mu'amala suma haka suke gudanar da mu'amala a tsakaninsu, na kira ka ne don na sanar da kai ba don ka tada hankalinka ba sai don a ƙara tsayawa tsayin daka dangane da yarinyar nan Raihan. Saboda suna da matuƙar wayo fiye da tunanin mai tunani, sun san hanyar da za su bi su yaudari mutum." Daddy ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Allah ya ƙara tsare mu bakiɗaya." Magunguna kala-kala Malam ya sake haɗa wa Raihan don wannan karon ya ci alwashin sai ya ga bayan Huzaifa ta kowanne hali. Bayaninsu ya yi wa Daddy da yadda za ta yi amfani da shi, godiya Daddy ya yi wa Malam sannan ya tura masa kuɗi masu yawa suka yi sallama ya koma gida. Yana zuwa gida ya yi wa Mommy bayanin abin da yake faruwa tare da yi mata bayanin yadda Raihan za ta gudanar da magungunan. Cikin damuwa Mommy ta sake yi masa zancen halin da Raihan take ciki, shi kansa yana lura da yanayin yarinya, ji ya yi babu daɗi amma babu wani abu da yake ganin zai iya yi saboda da kunya ya tunkari Malam da wannan maganar. Ɗakin Raihan ya shiga a lokacin tana zaune ta tasa laptop a gabanta tana hawaye, sakamakon kallon hoton Al'amin da ta yi a shafinsa na fuskar littafi, (Facebook). Tana ganin shigowar Daddy da sauri ta rufe laptop ɗin tana goge hawaye. Daddy zama ya yi akan kujera ya kalle ta duk sai ya ji ba daɗi saboda lokaci ɗaya ta rame ta lalace, da wata irin murya ya kira sunanta jiki a sanyaye ta amsa sannan Daddy ya ce, "Raihan yanzu wannan rayuwar kika ɗaukarwa kanki, dubi yadda kika rame kika lalace. Raihan me ya sa kike son saka rayuwarki a cikin wani hali, me ya sa ba za ki miƙa wa Allah lamuranki ba ki cire yaron nan daga zuciyarki? Ki yi addu'a Allah ya kawo miki mafi alheri ina ganin haka ya fi da ki saka wa ranki damuwa har wani ciwo ya kama ki." Raihan ta faɗa jikin Daddy tana fashe wa da kuka, sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ɗago ta ce, "Daddy wallahi na kasa cire shi a rana amma kullin ƙaunarsa nake ji a zuciyata, don Allah ka yi wani abu Daddy." Raihan ta ƙarasa magana tana haɗe hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo, hawaye bibbiyu yana zuba. Jikinta ya ji zafi zaau da zazzafi tausayinta ba ƙaramin kama shi ya yi ba, hannuwanta biyu ya kama ya ce, "Ki yi Addu'a Raihan domin babu abin da ya fi ƙarfin addu'a, kuma insha Allah zan san yadda za a yi Allah ya shiga lamuranmu." Cikin kuka Raihan ta amsa da Amin. Sai da Daddy ya jima a wurin yana lallashinta sannan ya fice daga ɗakin, yana fita ya sa Mommy ya haɗa mata ruwan tea ta shiga ɗakin da ƙyar ta matsa mata ta iya sha sannan ta sha maganin ta kwanta. Wannan ciwo na Raihan ba ƙaramin damun su Mommy ya yi ba, ba su kaɗai ba hatta su Inno lamarin Raihan damunsu yake don mommy bata sanar da su takamaimai abin da yake damunta ba, don tana gudun mitar su Inno kuma duk wanda suka haɗu da shi ta san sarai sai sun sanar masa da abin da ake ciki ita kuma tana gudun surutun mutane.
Chapter 78 · 0% Book details