← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 110

Sashe 79

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Na tara ku ne domin na sanar da ku game da hukuncin da na yanke, sanin kanku ne mun ɗauki dogon hutu mai tsayi saboda halin da ƙungiya take ciki. A bisa shawarar da aka ba mu wancen karon za mu kai wa Jabbul-ƙasi ziyara akan buƙatarmu domin matuƙar mu ka ce za mu ɗore a haka tabbas kwaɓarmu za ta yi ruwa kuma ba za mu kai labari ba. Ni da Hatsabibiya da mijinta, sai zaratan Aljanu goma daga jinsin Bil'adam goma za mu shirya mu tafi, dole mu shirya da shirinmu domin tafiya wurin Jabbul-ƙasi ba wasan yara ba ne. Za mu haɗu da ƙalubale a hanyar tafiya domin duk wannan tsawon lokacin na yi bincike negame da yanayin hanyar tsibirin Jabbul-ƙasi. Kuma na tura Aljani Ɓurƙum domin ya karɓo mana izinin zuwa wurinsa, saboda idan ka cire zuri'arsa wato waɗanda suka fito daga tsatsonsa haramun ne ka kai ziyara wurinsa ba tare da ka nemi izini ba. Wannan magana da nake yi muku ba za mu kai labari duka ba, domin ya faɗa wa Aljani Ɓarƙum cewa gabaɗayanmu mu rai goma ne zai tsira domin sauran duka za su halaka. Abin da bai sanar da mu ba su waye za su mutu su waye za su rayu, amma ni na yanke wani hukunci duk wanda aka kashe za mu ɗora zuri'arsa a gurbinsa." Abar bauta ta ƙarasa maganar cike da ƙarfafa musu ƙwarin gwiwa. Da farko jikkunansu ya yi sanyi da jin bayanin Abar bauta amma da suka ji yadda ta ƙarfafa gwiwarsu sai suka saki jikinsu, amsa mata suka yi cike da ladabi sannan ta ɗora da cewa, "Za mu zaɓi waɗanda za mu yi tafiyar da su sannan za mu bar waɗanda za su yi gadin ƙungiya saboda ba zai yuwu mu bar wurin haka sasakai babu kowa ba, sannan abin da zan ja hankulanku da shi wannan sunan na Abar bauta da kuke kirana da shi dole ku daina daga yanzu domin ya bi bakinku, kuma ya zama wajibi ku daina bauta min domin babban zunubin da zai iya kaimu ga hallaka shi ne a yi min bauta a hanyar mu ta zuwa tsibirin Jabbul-ƙasi. Ba wai sai kaɗai hanya ba Jabbul-ƙasi bai amince da wata bautar ba don haka ko da kuskure kar ku sake ku bauta min idan ba haka ba gabaɗaya mun zama halakakku." Cike da gamsuwa suka amsa sannnan Abar bauta ta ci gaba da yi musu bayanin yadda tafiyar su za ta kasance, ta tabbatar musu da cewar za su yi tafiyar cikin kwana Talatin masu zuwa.

Lokacin da Mommy ta ji bayanin Daddy game da Kabiru da ƴan uwansa ta yi farinciki sosai, saboda ita kanta Kabiru na matuƙar birge ta saboda kyawawan ɗabi'unsa. Bayan kwana biyu da faruwar haka Kabiru ya samu Daddy da magana akan yana son sai mai ɗakinsa ta sauka idan ya so sai su dawo gabaɗaya, Daddy ya ji daɗin haka domin shi yake nuna ya san mutumcin mace kuma yana tausayawa matarsa tun da ya yi tunanin haka. Amma sai ya nunawa Daddy ƙaninsa zai zo a cikin satin domin ya kama na shi aikin idan ya so shi kuma ya fara aiki a kamfanin da Daddy ya ce, Daddy da kansa ya bawa Kabiru kuɗi don ya turawa ɗan'uwansa na mota ya taho, cikin jindaɗi Kabiru ya karɓa yana yi wa Daddy godiya. Wata ranar laraba da dare Daddy ya samu Kabiru ya yi masa magana akan ya shirya saboda a washegari zai fara aiki kamar yadda ya gaya masa, ranar Kabiru kusan kwana ya yi bai yi baccin kirki ba saboda murna, gari na waye wa ya shirya yana jiran Daddy bayan wani lokaci ya fito suka tafi. Duk wainar da ake toyawa Raihan bata sani ba sai lokacin da Kabiru ya kusa sati biyu da fara aiki a kamfanin Daddy tukunna, tana daga ɗaki ta ji Daddy na yabon ƙwazo da aikin Kabiru. Raihan ba ƙaramin haushi ta ji ba don gani take a yadda ta ɗauki Kabiru bai kamata ya ɓoye mata wannan ci gaban da ya samu ba, da ta so zuwa ta same shi a ta yi masa tas amma sai wata zuciyar ta hana ta ita ma ta ce ba za ta kula shi da maganar ba. Sannu-sannu ciwo ya fara saka Raihan a gaba tun tana jinyar kanta ita kaɗai har Mommy ta fara fuskantar ciwon Raihan ya fara tsanani. A ranar wata Litinin ne suka wayi gari da tashin hankali sakamakon tashi da suka yi Raihan na wani irin amai mai haɗe da sirkin jini a jiki, kafin suyi wani yunƙuri tuni numfashinta ya ɗauke ta suma a wurin. Hankali a tashe Mommy ta kira Daddy take sanar da shi, da ƙyar ta iya kama Raihan ta saka ta a mota ta wuce da ita asibiti. Tana zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta sai dai har lokacin da Daddy ya ƙarasa ba su shawo kan matsalar ba, sai da suka shafe kusan awa guda da mintuna sannan suka samu damar daidaita numfashinta. Amma lokaci-lokaci wani irin jini na fita daga bakinta, wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankulansu ya yi ba. Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Kaburi yana harabar Asibitin ya haɗa kai da gwiwa ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Bayan Likitoci sun samu komai ya lafa suka samu Daddy Dr Muhammad ya fara yi masa bayani, "Alhaji gaskiya yarinyar nan tana cikin matsananciyar damuwa, wanann damuwar ita ce take barazanar tarwatsa rayuwarta. Kuna ina haka ya faru why? Yarinya ƙarama ta samu irin wannan condition ɗin? Yanzu haka zuciyarta na barazanar fashe wa sai dai wani ikon Allah amma gaskiya akwai gaggarumar matsala." Jiki a sanyaye Daddy ya ce, "Wallahi likita babu abin da yarinyar nan ta nema ta rasa, jarabar soyayyar wani yaro ta ƙwallafawa ranta alhalin shi yaronma bai san tana yi ba." Dr Muhammad ya mayar da glass ɗin idonsa sannan ya ce, "To gaskiya ku tsaya ku duba lamarin nan domin komai zai iya faruwa Allah ya kiyaye." Damuwa goma da ashirin ce ta yi wa su Daddy yawa. Don sai da Raihan ta kwana uku a asibiti ba tare da ta san wanda yake kanta ba, a rana ta huɗu ta fara gane mommy amma bayan ita babu wanda take gane wa kowa sai dai ta bi shi da ido. Ranar da su Inno suka zo duk iya zaman da suka yi bata tanka musu ba, sun yi kuka sosai saboda duk wanda ya ga halin da Raihan take ciki sai ya tausaya mata. A wannan lokacin Daddy ne ya yanke hukuncin sanar wa Malam ainihin abin da yake faruwa don ko kaɗan baya son ya rasa Raihan, lokacin da Malam ya ji wannan batu ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba saboda gani yake ba komai ba ne don Daddy ya yi magana an haɗa Raihan da Al'amin, kuma a wannan lokacin ya tabbatarwa da Daddy Al'amin zai auri Raihan bayan aurensa da sati guda. Wannan magana ba ƙaramim daɗi ta yi wa Daddy ba, sai dai har lokacin ba a sanarwa Al'amin takamaiman abin da yake faruwa ba. Ranar da Raihan ta cika kwana biyar a asibiti Malam ne ya je dubata bayan magariba kamar yadda ya saba. Kabiru na zaune akan kujera ya haɗa mata tea ya bata tana sha, Daddy da Malam ne suka shiga ya dubata. A kunyace Raihan ta amsa sannan Malam ya ce, "Ƴata duk na ji abin da yake faruwa don haka na zo da kaina na yi miki albishir don Allah ki kwantar da hankalinki indai Al'amin ne nan da sati biyu za a ɗaura miki aure da shi. Ni da na san haka ne ai da tuntuni an yi an gama, amma yanzun ma bata ɓaci ba tun da dai saura sati ɗaya bikinsa bayan auransa da sati guda sai a ɗaura naki." Wani irin farinciki ne ya kama ta don duk yanda ta so ɓoye wa sai da ta murmusa, Kabiru miƙe wa ya yi hankali a tashe jiki na rawa saboda ɓacin rai ko gabansa baya gani ya fice daga ɗakin. Daga Daddy har Malam babu wanda ya kawo komai dangane da fitar Kabiru, Daddy ya miƙa wa Malam Hannu suka sake gaisawa yana yi masa godiya. Daga bayan gatangar asibitin Huzaifa da ke laɓe ya furzar da iska mai zafi rai a matuƙar ɓace ya furta, "Tabbas na so ki kuma na ƙaunace ki amma dole zan haƙura da ke, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba domin ba zan juri ganin wani ya same ki bayan ni na rasa ki ba." Rufe bakinsa ke da wuya Raihan da ke shan shayi ta ƙware nan take ta fara tari tun suna ganin kamar ƙwarewa ce har ta fara kyalawa wani irin aman jini ta baki da hanci.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

43
Chapter 79 · 0% Book details