← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 110

Sashe 72

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da matuƙar mamaki Raihan ta dube su a hankali ta riƙa takawa kai ba ɗankwali, ganin suna ci gaba da tsokanarta wasu har da masu jifanta da dutse ya sa Raihan ta fara tunkararsu tana faɗin, "Don Allah kuna ji na kuma kuna ganina." Dariya suka fara yi wasu daga cikin yaran suna jan rigarta ta baya suna faɗin, "Mahaukaciya ƴar macukule." Tafiya Raihan ta fara yi ba tare da ta san wurin da take jefa ƙafarta ba, sai da ta ji zafin wani ƙaton dutse da wani yaro ta jefeta a kanta, sanann ta tabbatar da ba mafarki take yi ba tabbas ita ce Allah ya kuɓuto da ita. Waiga wa ta yi tana ƙare wa mummunar bolar mai ɗauke da caɓalin kayan ƙazanta iri-iri, wani tunani ne ya dirar mata a zuciya. Ta ayyana kada Huzaifa ya sake sace ta, ƙafa ba takalmi kai ba ɗankwali Raihan ta zuba a guje don ta ci alwashin ko a ƙafa ne sai ta koma gidansu. Tana tafe tana gudu yara na biye da ita har ta ƙarasa bakin titi, duk Ɗan adaidaita sahun da ya zo da Raihan ta tsayar da shi idan ya dubi yanayinta da yaran da suke biye da ita sai ya ja mashin ɗin sa ya ƙara gaba. Yaran da suke biye da ita ne suka fara damunta don haka ta fara yi musu magana, daga ƙarshe da abin ya damu Raihan sai kawai ta fashe da kuka. Wani mutum ne da ya je wuce wa ya yi wa yaran tsawa amma suna ganin ya wuce suka ɗora daga in da suka tsaya. Ganin haka ya sa Raihan ta ci gaba da tafiya a ƙasa, nan take yaran suka fara ɗiban ƙasa suna watsa mata sai dai wannan karon bata kula su ba. Ganin abin nasu ya sake yawa suna ta jifanta da manyan duwatsu ya sa Raihan ta ɗiba da gudu za ta tsallaka titi bisa tsautsayi wani mai mota ya zo wuce wa ya make ta. Da sauri yaran suka yi carko-carko, Raihan ta faɗi a can gefe kanta ya fashe yana fara zubda jini. Ban da juyi cikin azaba babu abin da take yi, a rikice Al'amin ya fito daga motar yana sallallami, da taimakon wasu matasa aka saka Raihan a cikin mota wani ɗan sanda na daga gefe ya ƙaraso ya shiga gaban motar suka fara zuwa Police station aka rubuta report sannan suka wuce asibiti. Wani private hospital Al'amin ya kai Raihan da ke unguwar sharaɗa, nan take likitoci suka shiga bata kulawar da ta dace. Al'amin zaune ya yi ya haɗa kai da gwiwa a hankali ya fara ƙare wa Raihan kallo yana son sanin wurin da ya san fuskarta amma ya kasa tunawa, kasancewar yawancin hotunan Raihan da aka watsa duk na bikinta ne kuma da kwalliya a fuskarta shi ya sa farat ɗaya ba za ga ce ita ba ce. Wayar Malam Usman ce ta shiga da sauri Al'amin ya ɗauka bayan ya yi sallama Mahaifinsa ya ce, "Ka ƙarasa ne?" Jiki a sanyaye Al'amin ya gaya wa mahaifinsa abin da yake faruwa a rikice Malam Usman ya furta, "Hasbunallahu Wani'imalwakeel. Yanzu kuna wane asibitin?" Al'amin ya ce, "Health Care Clinic na kan titin mu." Malam Usman bai gama jin abin da Al'amin yake faɗa ba ya katse wayar, ba a ɗauki lokaci ba Malam ya ƙarasa asibitin. Daga harabar asibitin ya kira Al'amin yana tambayar ɓangaren da suke, Malam na shiga ya sauke idonsa akan Raihan yana faɗin, "Garin yaya hatsarin ya faru..." Sauran maganarsa ce ta maƙale jiki na rawa ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "Raihan!" Police ɗin da Al'amin suka juya da sauri suna kallonsa, cikin tsananin mamaki Al'amin ya ce, "Daddy ka santa ne?" Malam ya sake matsa wa gaban gadon da Raihan take bacci saboda allurara baccin da aka yi mata ya yi, ya juyo wurin yana kallon Al'amin ya ce, "Raihan ita ce yarinyar da ta ɓace ranar daren aurenta." Da sauri Al'amin ya ƙarasa gaban gadon yana ƙare mata kallo, sai a lokacin ya tabbatar da kammaninta. Police ɗin da ke gefe ya ƙarasa yana faɗin, "Wallahi Alhaji tun gani na da ita nake wasu-wasi idanuna suke gane min kamar ita ce amma sai na yi tunanin wannan ko masu rangwamen hankali ce." Malam na gama jin sa ya sauke ajiyar zuciya haɗe da zaro waya ya furta, "Ai ta kwana gidan sauƙi. Kai Alhamdulillah Allah shi ne abin godiya." Wayar Daddy ya kira bata daɗe tana shiga ba ya ji an ɗauka, ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Malam ya ce, "Alhaji don Allah ka ƙaraso yanzu ina Health Care Clinic na kan titin sharaɗa." Cikin sauri Daddy ya ce, "Malam Allah ya sa an dace ko an ganta ne." Malam ya yi murmushi mara sauti ya ce, "A'a ba haka ba ne amma ka dai ƙaraso yanzu." Katse wayar Daddy ya yi cikin sauri ya shiga mota kamar Yadda Malam ya gaya masa sunan asibitin sai ga shi bai ɗauki lokaci ba ya ƙaraso, kiran Malam ya yi ya sanar da shi yana harabar asibiti nan take Malam ya tura Al'amin ya taho da shi, sai da Al'amin ya gaishe da Daddy cikin girmamawa sannan ya yi gaba Daddy na biye da shi zuciyarsa sai buga wa take yi. Shigarsa ɗakin ya kusa daskarar da numfashinsa, murza idonsa ya yi ya sake ware su akan Raihan da ke kwance a kan gadon cikin wani irin yanayi, duk wanda ya ganta a wannan lokacin ba zai taɓa tsammanin mai cikakkkiyar lafiya ba ce, kana ganinta za ka yi tunanin ko mahaukaciya ce sabon kamu. Da sauri Daddy matsa gaban gadon sai kawai ya rungumeta haɗe da ruƙo hannunta tsam kamar wani zai ƙwace ta, Malam ne ya riƙo hannunsa ya ɗago Daddy ya nuna masa kujera sannan ya ce, "Godiya za mu yi wa Allah da ya bayyana mana ita, komai ka ga ya faru da bawa yana daga cikin jarrabawarsa don haka sai mutum ya sa hannu bibbiyu ya rugumeta a yadda ta zo masa, kuma ya gode wa Allah." Jinjina kai Daddy ya yi ya ce, "Wannan haka yake sai dai mu ce Alhamdulillah." Nan take Malam ya zayyana wa Daddy duk abin da ya faru, jim Daddy ya yi ya furta: "Shi Huzaifa ba a gan shi ba kenan? Ya Rabbi! Ubangiji ka bayyana wannan yaron cikin ƙoshin lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. Daddy ne ya ciro waya ya kira Mommy ya sanar mata halin da ake ciki, a take ta miƙe ta ce ta warke don duk yadda Likitoci suka so dakatar da ita ƙi ta yi. Ita da Mama Hafsa suka ƙarasa asibitin Mommy na shiga ta saka kuka haɗe da faɗa wa jikin Raihan, a hankali Raihan ta buɗe idonta tana ƙare wa mutanen da ke ɗakin kallo. Karaf idanunta suka sauka akan Al'amin da yake danna waya yana sakin murmushi. Yunƙura wa ta yi za ta tashi zaune Mama Hafsa ta taimaka mata, kallon su Daddy ta fara sai kawai ta saka musu kuka. Duk yadda Daddy ya kai da yin dauriya sai da hawaye ya zubo masa. Ganin haka ya sa Malam ya miƙe yana shirin yi wa Al'amin magana Raihan ta nuna Al'amin ta ce, "Mommy kin gan shi, don Allah kema kina ganinsa." Sai a lokacin Mommy ta kai idonta wurin Al'amin da ya ɗago suka haɗa ido. Ita kanta mommy ta yi mamakin ganinsa tana shirin yin magana Malam ya ce, "Raihan wa kike gani Al'amin ko wani ne daban?" Ya yi mata wannan tambayar ne don ya tabbatar da ba buɗe mata ido suka yi ba. Raihan ta sake nuna Al'amin ta ce, "Abba wannan fa mai baƙaƙen kayan nan wallahi a Harami na taɓa ganinsa." Malam ya yi murmushi ya ce, "Yayanki ne, ai yarona ne sunansa Al'amin." Mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Raihan da jin Al'amin ɗan gidan Malam ne amma ta shafe shakaru tana dakon soyayyarsa, ba su yi aune ba sai gani suka yi murmushi ya kuɓuce mata. Ta koma ta kwanta haɗe da lumshe ido, Malam da Al'amin sallama suka yi wa Daddy suka tafi tare da cewar zai turo wa Raihan waɗansu magunguna a riƙa bata da na turarawa.
Chapter 72 · 0% Book details