← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 110

Sashe 63

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kabiru ɗan asalin garin Shanono ne cikin wani ƙauye mai suna Rigar Arɗo, daga dangin mahaifi da Mahaifiya gabaɗayansu haifaffin garin shanono ne. Mahaifinsa sunansa Musa Balarabe amma an fi saninsa da Baffajo, sai mahaifinyarsa mai suna Karime ana kiranta Inna wuro sakamakon ta ci sunan kakarta ta wurin Mahaifi. Kabiru su biyar ne a wurin iyayensa, shi ne babba sai ƙanwarsa mai bin sa Rahane wacce ake kira Rahe. Tana da aure da ƴaƴa shida, sai mai bin ta Fatsim ita ma tana da aure da ƴaƴa uku, daga ita sai Shatu wacce take da ƴaƴa biyu sai ɗan autansu mai suna Bala wanda yake da shekara goma sha biyu. Baffajo manomi ne kuma makiyayi ne ya riƙi sana'ar noma da kiwo tubalin da yake gina iyalinsa ta hanyar ci da sha, ilimi da tufatarwa. Yana da rufin asiri sosai kasancewar Ubangiji ya yalwata su da arziƙin dabbobi musamman shanu da awaki. Baffajo yana tsayawa ƴaƴansa kai da fata wurin ganin sun samu ilimin addini sai dai basa karatun boko kasancewar basu ɗauke shi da muhimmanci ba. Kabiru tun yana da kimanin shekara goma Mahaifinsa Baffajo ya ɗauke ya kashi almajiranci can garin gombe, sai dai bai bar shi kara zube ba yana shirya wa lokaci-lokaci yana kai masa ziyara haɗe da kai masa kayan abinciki ya damƙa wa Malaminsu Malma Iro. Kasancewar Malam Iro mutane da dama sun shede shi akan kula wa da almajiransa, Mutum ne mai amana da kula wa da haƙƙin da aka ba shi don haka ya sa su Kabiru suke matuƙar ƙaunarsa. A makarantar Malam Iro Kabiru ya haɗu da wani almajiri mai suna Babbale, Babbale nutsattse ne ba shi da hayaniya kamar dai Kabiru don haka ta su ta zo ɗaya suka ci gaba da rayuwa da daɗi babu daɗi har Allah ya kai su lokacin da suka yi saukar alƙur'ani kowa ya kama gabansa. Kabiru ya koma garinsu ko shekara bai yi ba watarana shi da Baffajo sun shiga gona wasu ɓata gari da ake zargin ɓarayi ne suka shiga gonaki suka riƙa illata manoman da makiyaya sannan suka kaɗe duka shanun garin suka yi awon gaba da su. A cikin waɗanda suka jikkata har da Mahaifin Kabiru wanda suka harbe shi har a wuri biyu. Harbin farko a gwiwar ƙafarsa harsashi ya ratsa sai tsakiyar bayansa da nan ma suka sakar masa harbi. Kabiru kuma karaya ɗaya ya yi a ƙafa sakamakon saran da suka riƙa kai masa har suka ci galaba akansa. A wannan lokacin mutanen wannan ƙauyen sun shiga firgici da tashin hankali sakamakon ba su taɓa cin karo da irin wannan ta'addancin a cikin garinsu ba. A haka suka ci ga ba rayuwa waɗanda suka rasu aka yi musu sitira waɗanda suka jikkata aka shiga nema musu magani. Mahaifin Kabiru yana ɗaya daga cikin mutanen da aka yi wa mummunan rauni, saboda da farko maganin hausa ake yi masa sai da suka ga ƙafarsa ta tasamma lalace wa sannan aka fara kai shi cikin gari babban asibiti. Tashin farko likitoci suka tabbatar da yanke ƙafar Baffajo za a yi saboda ta riga da ta lalace ba zai sake morarta ba, a wannan lokacin su Inna wuro ba ƙaramin tashin hanakali suka shiga ba. Amma da yake suna da ragowar ƴan kadarorinsu sai suka ganganɗa suka sayar da aka biya kuɗi aka yanke wa Baffajo ƙafa tun daga wurin gwiwarsa har zuwa idon sawunsa. Sai da likitoci suka sake yin gwaje-gwaje da hotuna aka sake gano babbar matsalar da take tattare da Baffajo domin ƙashin bayansa ya samu matsala, don haka sai an yi masa aiki. Tashin farko kuɗin hoton ƙashin bayansa kusan dubu ɗari biyu da hamsin aka caje su sannan da aka gano ciwon aka tabbatar da za a yi masa aiki amma sai sun zube maƙudan kuɗi naira miliyan ashirin da biyar. Wannan magana ta likitoci ba ƙaramin ɗaga hankulansu ta yi ba, Kabiru da kansa ya riƙa bi cikin rugarsu yana neman taimako koda karo-karo ne amma ko dubu ɗari a cikin ƙauyensu bai samu ba. Ganin ba su da damar waɗannan kuɗaɗen suka tattaro suka dawo gida da Baffajo ya ci gaba da jinyar jikinsa ana yi masa maganin hausa. Sai dai tun da ya kwanta wannan jinyar komai sai an yi masa, sai an ɗaga sa an kwantar hatta fitsari sai dai ya yi a wurin idan kuwa aka zo gyara shi ya rinƙa ihu saboda tsananin azabar da yake ji a jikinsa. Ana cikin haka har duk abin da suke da shi ya ƙare har ya kai Inna Wuro ta fara sayar da sitirar da suke saka wa. Ganin haka ya sa Kabiru ya yi tattaki zuwa gidan kansilan garinsu don ya yi masa hanyar zuwa wurin sanatan yankinsu ko zai samu ya taimaka masa. Amma fir Kansilan ya ƙi daga ƙarshe wani abokinsa Na Sa'ade ya kira bayan ya zauna ya nuna Kabiru sannan ya yi masa bayanin halin da Baffajo yake ciki, Na Sa'ade mazaunin garin ne amma yana zuwa kasuwanci cikin garin Kano don haka ya fi su wayewar kai don haka Kansila yake ji da shi a garin. Na Sa'ade yana gama jin bayanin Kansila cikin yanayin tausayi ya ce, "Taimako ɗaya zan yi maka na haɗa ka da wani mutumi a birni amma shi aikinsa zai nema maka gida ka riƙa gadi amma a ƙa'idarsa albashinka na wata ukun farko shi zai karɓa. Amma fa zai kai ka gidajen masu yatsu da yawa, don ba za ka yi zaɓen tumin dare ba. Ina taƙaice maka wataƙila duk wata ka riƙa samun dubu hamsin."

Jin wannan maganar ya sa Kabiru ya ce zai je ya yi shawara da Mahaifiyarsa idan ta amince, saboda suna fuakantar matsanancin talauci. Lokacin da Kabiru ya sanar wa da Inna wuro ƙin amincewa ta yi saboda tana tsoron kar a tafi da Kabiru birni a sayar da shi, amma da Kabiru ya nuna mata mutumin na hannun daman Kansila ne sai ta amince amma da sharaɗin sai sun je gaban Mai gari an yi maganar a gabansa. Lokacin da Na'sade ya ji wannan maganar ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba har ya nuna ya fasa tafiya da Kabiru, amma da Kabiru ya lallaɓa shi kuma ya nuna masa yanayin rikicin tsofaffi ne sai ya amince. A gaban Mai gari aka yi komai bayan wannan zaman da kwana biyu Kabiru da Na Sa'ade suka taho garin kano. A washegarin ranar da suka sauka Na Sa'ade ya kai Kabiru gidan Malam Haru sannan ya gabatar da Kabiru, cikin mutumci ya tarbe shi sai da suka zauna sannan ya sanar wa da Kabiru sharuɗɗansa nan take ya amsa tun da dama Na Sa'ade ya sanar da shi kafin su zo. Satin Kabiru ɗaya a gidan Malam Haru aka zo masa da maganar samun aiki a gidan Daddy, ba ƙaramin daɗi ya ji ba don haka ya fara aikinsa cikin mutumci da mayar da hankali. Haka Kabiru ya ci gaba da aikin gaidinsa sai dai tun zuwansa yake waɗansu irin miyagun mafarkai masu ban tsoro, a ranar da ya fara cin karo da Mama Uwani ranar kwana ya yi kansa na tsananin yi masa ciwo da mafarkin manyan baƙaƙen shanu suna biye da shi za su halaka shi. Haka kawai ya ji ta su bata zo ɗaya ba don haka ko shiga sabgarta baya yi tun da dama ba fito wa harabar wurinsa take yi ba.
Chapter 63 · 0% Book details