Sashe 39
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ilahirin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ya ƙarasa gaban Inno ya ce, "Don Allah Inno me kuke yi haka wannan abin da kuke yi ko Raihan ba za ta yi shi ba, ba fa mu kaɗai ba ne a gidan nan don Allah ko ma meye ku bari komai ya daidaita." Inno ta saki baki da hanci tana kallon Daddy sai da ya gama magana ta dubi Malam Usman ta ce, "Malam don Allah saboda wa nake haƙiƙance wa?" Malam Usman ya yi shiru don bai fahimci abin da Inno take nufi ba, Inno ganin haka ya sa ta dubi Daddy tana faɗin, "Audullahi saboda ina kare ka za ka ci zarafina?" Kafin Daddy ya yi magana Goggo ta dubi mommy ta ce, "Wai Zainabu duk maganar da nake yi ba ki ji abin da na faɗa ba ne? Na ga ko gezau baki yi ba." Mommy baƙinciki goma da ashirin ya cikata ta dubi Goggo tana faɗin, "Don Allah Goggo yanzu me kike so mu ce, kina gani yanzu haka kaya nake haɗawa za mu tafi nema wa Raihan lafiya, da wanne zan ji?" Goggo ta riƙe haɓa tana cewa, "Wai kina nufin yaron nan bai yi fata-fata da aljanin jikin Raihanu ba." Mommy ta jinjina kai fuska babu walwala ta ce, "Kin san ciwo shi yake shiga farat ɗaya sauƙi sai a hankali, balle irin wannan larurar ta Raihan sai an bi a sannu." Inno ta kalli Daddy rai a ɓace tana faɗin, "Amma dai Audullahi kun shammace ko in ce kun yaudare mu, yanzu a madadin ka gaya mana mu kame bakinmu sai ka bari mu yi ta sakin zance, Allah ya sani idan wani abu ya shafe mu kai da matarka kuna da kamasho a ciki don haƙƙinmu ba zai bar ku ba."Inno ta waiga wurin da Kabiru yake tsaye ta nuna shi da yatsa ta ci gaba da cewa, "Allah dai ya watsa maka albarka ka ji Kabiru, yaron nan bai bari mun furta ko tuf ba bayan ayar Allah, ban da hailala da istigifari babu abin da muke yi don kariya daga kaidin wancen hatsabibin." Malam Usman ya yi murmushi don rikicin tsofaffin ya fara bashi dariya, ya ƙarasa gabansu ya furta, "Mama babu abin da zai faru da ku in sha Allah. Ita ma Raihan za ta samu lafiya da yardar Allah." Cike da gamsuwa Goggo ta matsa gabansa sai da ta kalli hagu da dana cikin raɗa ta ce, "Ka dubi girman Allah malam ka yi min wani abu ɗaya kafin ka ƙone yaron nan." Lokaci ɗaya suka juyo wurinta, Goggo kuwa ko a jikinta ta sake kallon gabas da yamma tana faɗin, "Amma dai ba zai iya jinmu ba ko?" Inno ta ƙarasa wurin ta ce, "Shi wa?" Goggo ta yi mata alamu da hannu a kan ta yi maganar ƙasa-ƙasa sannan ta ce, "Wannan hatsabibin da ya yi rayuwa da a siffar uwani." Inno ta yi kasaƙe ba tare da furta komai ba don ita tsoron magana take akan Huzaifa, tana tsoron kar ya farmaketa a kowanne lokaci. Malam Usman ya gyaɗa kai yana cewa, "Eh ina jin ki Mama." Goggo ta zura hannu cikin kajarta (Siket ɗan ciki na tsofaffi mai aljihu a jiki.) Ƙullin goro ta ciro ta miƙa wa Inno ta ce, "Don Allah ci ki ji daushe ne ko namijin goro." Inno ta karɓa ta wurga a baki ji kake garas, Inno ta miƙa wa Malam Usman guntun wanda ta gutsira ta ce, "Ɗana ci ka ji kamar Daushe." Daddy ya kalli Malam Usman a kunyace ya ce, "Don Allah Malam ka yi haƙuri ka san lamari tsofaffi sai..." Malam Usman ya katse shi da cewar, "Babu komai Alhaji muma muna nan da su." Ya karɓa ya sa a baki yana fara tauna Goggo ta ce, "Don Allah ka taɓa jin goro mai daɗin wannan?" Malam Usman yana ci gaba da tauna yana girgiza kai, ganin haka ya sa Goggo ta washe baki tana faɗin: "Duk faɗin garin nan ban taɓa siyan goro a nan ba sai na niƙi gari na tafi Albasu duk ƙanƙantar wanda zan siya, amma hatsabibin can da ya yaudare mu da siffar Uwani kusan tare muke cinye wa da shi. Kai wallahi ina zargin har satar min yake ban sani ba, don idan na siyo na dubu biyar baya rufa wata biyu don Allah cin wannan goron ai daga ji ba na lafiya ba ne." Inno ta gyaɗa kai ta yi ƙasa da murya ta ce, "Ni nadamar da na yi da muka sakankance shegen nan yake ƙare wa tsirancinmu kallo. Allah ya sani da Alhaji babba zai dawo mai raba Huzaifa da shi sai Allah, don Allah Zinaru baki taɓa sauya kaya a gabansa ba? Ni tsorona Allah da Ma'aiki kar ya sake dawo mana, kuma wallahi da Alhaji babba zai dawo sai ya bi mini haƙƙina saboda Allah ya sani ban yafe ba." Goggo ta yi jim tana nazari sannan ta ci gaba da cewa, "Ki bari a fara sauraron shari'armu da shi tukunna." Malam Usman ya yi dariya mai sauti ya ce, "Mama wannan ai ba abin da damuwa ba ne tun da za a ƙone shi kin ga hukuncin ai ya yi har na cinye goron da ya yi miki." Goggo ta wara hannuwa tana washe baki ta ce, "Shi kenan ma! Amma don Allah ka ƙone shi da manyan ayoyi masu saurin babbake aljanu." Malam Usman ya amsawa Goggo; Inno na shirin magana ya ce, "Alhaji lokaci na tafiya ya kamata ya kintsa sai mu wuce ko?" Inno ta kalli Goggo murya a sanyaye ta ce, "Zinaru ni kam na roƙe ko gafara man." Goggo ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya yi mana aikin gafara, amma ni kam baki taɓa yi min komai ba wanda ya faru ma sharrin shaiɗan ne." Inno ta karɓe zancen da cewa, "Allah na tuba Audullahi da Zainabu ko a lahira na ji za su raba gari ai sai in da ƙarfina ya ƙare, yoo ana zaune ƙalau mu ɗaukar wa kanmu zunubi. Kin san hukuncin wanda ya datse igiyar sunnar Annabi kuwa." Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ai ko yau sai na kwana hailala da istigifari don tun a Albasu ban sake aikata irin wannan zunubin ba, ina ni ina raba auren Zainabu haka kawai na faɗa Sa'ira ko kuma Hawuya, a'a raba ni da wannan lamarin ai ko a Aljanna ma muna sahun masu shiga Firdausi." Mommy da Daddy suka yi murmushi saboda da farko hankalinsa ya tashi don tsofaffin ba ƙaramin rikici gare su ba.
Cikin gida Mommy ta koma ta ci gaba da taimaka wa Raihan ta shirya, sai da ta bata ruwan Tea ta sha sannan ta haɗa musu kayansu a jaka. Daddy ya jima a toilet yana gasa jikinsa sannan ya samu ya ɗan ji daɗin jikinsa dukda raunin da ta yi masa dole sai ya dangana da asibiti. Kafin wani lokaci tuni sun gama shiri tsaf. Inno da Goggo har lokacin ba su fahimci Mommy da Raihan za su koma Waraka da sunan sai Raihan ta samu lafiya za su dawo ba, sai da suka ga Mommy da kaya niƙi-niƙi sannan Inno ta wurga mata tambaya, "Zainabu ni kam wai baki huce ba ne Allah Albasun za ki tafi na ganki da kaya?" Mommy ta manta shaf da maganar tafiya Albasu don haka ta ce, "Inno Waraka za mu je fa, kin san suma Islamic chemist ɗin an ci gaba yanzu har gado ake bawa mara lafiya." A zabure Goggo ta ce, "Mu kuma mu zauna a ina?" Inno ta cafe da cewar, "Taya ni ji kin ji." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke don ita hankalinta ya yi gaba ta manta cewar abin da ya faru ko me za a yi wa su Inno ba za su taɓa kwana a gidan ba. Cikin gida ta koma suka tattauna da Daddy sannan suka fita, yana fitowa ya ce ya kira waya za a kai su Albasu idan ya so bayan Raihan ta dawo sai a dawo da su. Wannan magana ba ƙaramin daɗi ta yi wa su Inno ba, basu ɗauki lokaci ba Direban Daddy ya kwashe su da kayansu, don kayan sawarsu ma sai Mommy ce ta kwaso musu sun ce ba za su taɓa shiga gidan ba. Daddy ya ɗebo kuɗi masu yawa ya basu haɗe da kayan abinci ya zuba musu a boot sannan suka wuce Albasu. Mommy lokacin da ta ce wa Raihan ta fito su tafi da farko ƙi ta yi sai da Malam Usman ya shiga gidan da kansa ta fito, tana tafe tana harare-harare. Ganin haka ya sa Daddy ya fara yin baya-baya da ita saboda dukan da ta yi masa bai gama wartsakewa ba. Kabiru ba karamin tausayin Raihan ya yi ba don lokaci ɗaya gabaɗaya ta fita hayyancinta duk ta yi wani iri ga wata rama da ta yi ta lokaci ɗaya.