Sashe 105
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tallafin da Alhaji Shatima ya samu ne ya bashi damar samun ƙwarin gwiwa har ya rage jin zafin Raihan, saboda ya samu kuɗaɗe masu yawan gaske. Don haka magriba na yi ya fita ya sake yi musu siyayyar kamar yadda Angwaye suke yi idan za su shiga ɗakin amarensu, lokacin da ya dawo Raihan na kwance tana danna wayarta ta yunƙura ta yi masa barka da zuwa sannan ta karɓi ledar hannunsa. Plate ta ɗauko a kitchen ta fara saka musu Alhaji Shatima na tayata, da kansa ya ɗauko musu ƙananan kofuna ya zuba musu lemo suka fara ci yana yi mata hira a hankali. Wannan karon Raihan da kanta take ci sai dai Alhaji Shatima na jikinta tsam kamar wai zai kwaceta. A haka har suka gama ci suka taɓa hira sannan suka ya da zango akan gado, ƙirjin Raihan sai bugawa yake jikinta na rawa don haka Alhaji Shatima ya raɗa mata a kunne, "Karki tsoro haba kamar ba jarumar mata ba." Ajiyar zuciya Raihan ta sauke yana ci gaba da aika mata sakwanni masu zafi, tun tana ɗari-ɗari da shi har ta saki jikinta. Jin yana ƙoƙarin shigarta ya sa ta dube shi duk da tana jin nauyinsa, ta kamo hannunsa ta ɗora akanta sannan ta furta. "Don Allah karka manta da addu'ar da Annabin Rahama ya koyar da mu a wurin kusantar iyali." Saboda ita kaɗai ta san irin abin da ta fara ji a jikinta game da shi, ta tabbata akwai abin da yake shirin faruwa don ko kaɗan bata ji Alhaji Shatima ya ambaci sunan Ubangiji don neman tsari. A kunyace Alhaji Shatima ya furta, "Tabbas ko rannan na ji wani Malami ya karantata amma sam ban iya ba." Raihan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Duk abin da na faɗa ka maimaita, saboda mutane da dama na manta wa da wannan addu'ar kuma tana da muhimmanci domin idan Allah ya ƙaddara za a samu rabo shaiɗan ba zai yi tasiri a rayuwar wannan yaron ba, duk wani sharri da kaidin shaɗan da tawagarsa Ubangiji zai kare ku daga sharrinsu." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ta fara karanta masa kamar haka: "Allahumma Jannibnasshaɗan,Wajannibnasshaiɗana Marazaktana." Sannan ya ci gaba da aikata mata da kalaman soyayya har ya cimma burinsa. A hankali Alhaji Shatima yake sauke ajiyar zuciya, ya yunƙura ya faɗa banɗaki don tsarkake jikinsa sannan ya dawo ya taimakawa Raihan ita ma ta gyara jikinta sannan suka yi addu'a suka koma bacci. Asubar Fari Raihan ce ta fara tashi yana jin motsinta shi ma ya tashi, tare suka shiga toilet suka ɗauro alwala Alhaji Shatima sai nannan yake yi da ita, Raihan har mamaki take yi zuciyarta fes don ko babu komai Alhaji Shatima ya nuna mata kulawa da tsantsar soyayya. Doguwar riga ya zura ya wuce masallaci Raihan ta tayar da sallah bayan ta idar ta ɗaga hannu ta godewa Allah da ya bata miji mai ƙaunarta yake bata kulawa.Tana nan zaune ta ji shigowarsa, shigarsa ta yi daidai da kiran wayarsa. Kallon Raihan ya yi ya sakar mata murmushi sannan ya ɗauki wayarsa, ganin baƙuwar lamba ya sa ya yi zaton ko masu yi masa jaje ne don tun da abin ya faru mutane kala-kala suke kiransa. Yana ɗauka ya ji an ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya, ransa ne ya fara ɓaci a harzuƙe ya ce, "Wa ye haka kamar mara aikin yi?" Daga can ɓangaren aka amsa masa da cewar, "Ni ne kuwa mai aikin yi tun da na fara yi maka ɓarna a daren jiya, bar ganin ka shiga gonar da ba taka ba na rantse da hatsabibancin da kakana ya bar min ba za ka keta haddin Raihan a banza ba, Raihan tawa ce kamar yadda na faɗa ina ƙara nanatawa Idan kuma kana tantama ka buɗe Whatsapp ɗin ka zan turo maka hotunan da muka ɗauka a daren jiya bayan fitarka wurin gidan gonarka da ya babbake. Sai da muka ɓarje amarcinmu sannan kuma muka yi hotuna..." A fusace Alhaji Shatima ya katse shi da cewar, "Kai wai me kake faɗa ne? Wacece matar taka?" Dariya aka sake yi sannan aka ci gaba da cewa, "Saurin me kake yi za ka ga gane ko wanene ai, amma kafin nan ina yi maka albishir da na cinnawa kamfanin shinkafarka da na robobinka wuta sai ka ɗauki duk wani mataki da ka ga damar ɗauka. Amma ka duba Whatsapp ɗin ka za ka gani idan ƙarya na yi maka, kuma wallahi da ni kake zance." Ƙit! Alhaji Shatima ya ji an katse wayar, a rikice hannunsa na rawa ya kunna data saƙonni na fara shigowa ya ga wata lamba an turo masa hotuna rututu, yana shiga ya ga hotunan tsiraici ne na Raihan da wani matashi. Raihan na daga gefe jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, hawaye ne ya taru a idonta don duk hirar da suka yi ta ji ta a kunnenta. Fuskarsa ce ta haɗe murtuk ya kalli Raihan suna haɗa ido ta fara matsawa da baya tana faɗin, "Na rantse da Allah ban san komai ba. Wallahi duk sharri ne ya yi min ni ban san akan me yake magana ba." Miƙe wa ya yi yana huci ya ƙarasa kan Raihan ya daƙumota, yana shirin kai mata mari wayarsa ta sake ringing. Ganin lambar ɗazu ya sa shi ɗauka da sauri yana karawa a kunne aka ce, "Idan ka sake ka taɓa min mata wallahi sai na yi maka kisan da kare ma ba zai ci ba, don yadda na ƙone gidan gonarka da kamfaninka haka zan ƙoneka ƙurmus." Kashe wayar ke da wuya Alhaji Shatima ya wurgar da Raihan a gefe, lambar mai gadin Kamfanin shinkafarsa ce ta shigo yana ɗauka ya furta, "Haladu lafiya kake kirana da asubar fari?" A hargitse ya ji yana faɗin, "Alhaji wuta ta kama a kamfani yanzu haka da fara mamaye ko ina." Alhaji Shatima bai gama jin maganar Haladu ba ya fita da sauri, kai tsaye motarsa ya ɗauka ya fita da gudun gaske da niyyar ya nufi kamfaninsa. Yana tafe a hanya ya kira lambar Fire service yana ji an ɗauka ya kwatanta musu kamfaninsa da abin da yake faruwa. Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama bisa tsautsayi kan motarsa ta ƙwace ta yi wani gidan mai da ke gefen titi, nan take wuta ta tashi gabaɗaya har motar Alhaji Shatima. Duk yadda ya yi ƙoƙarin fitowa ya kasa, kasancewar da sassafe ne ya sa babu mutane a hanyar mutane ba su lura ba sai da wutar ta ruru sosai sannan aka riƙa ɗiban ruwan kwata da ƙasa ana zubawa, daga ƙarshe sai da aka kira ƴan kwana-kwana sannan Allah ya taimaka wutar ta mutu bayan ta ƙone komai ƙurmus, don har ta fara taɓo ƙananan kantunan da ke maƙotaka da gidan man. Rayuka uku aka rasa a wurin daga Alhaji Shatima sai wasu ma'aikatan gidan man mace da namiji, sun ƙone ƙurmus haka aka riƙa ɗaukan hutunansu ana yaɗa wa a shafikan sada zumunta, daga ƙarshe aka samu da ƙyar aka ciro gawar Alhaji Shatima a mota aka haɗa da ta guda biyun aka wuce da su mutuware.
Tun bayan fitarsa Raihan ta kasa zaune ta kasa tsaye don bata san fitarsa me zai yi ba, tana nan zaune har gari ya waye sai dai ko ruwan tea ta kasa sha saboda tashin hankali da fargaba. Ta kira wayarsa ya fi a irga amma shiru ta ƙi shiga, tana nan zaune wajen ƙarfe tara na safe ta ji Mai gadi na ƙwanƙwasa mata ƙofa. Sai da ta yafa mayafi ta buɗe ta ji ya ce, "Ranki ya daɗe wani bawan Allah yana bakin gate ya ce Mahaifinki ne." Da mamaki Raihan ta ce, "Mahaifina kuma." Ya gyaɗa mata kai. Dakatar da shi ta yi ta je ta duba wayarta don ta kira wayar Daddy ta ji, sai a lokacin ta ga misscall ɗin Daddy da yawa, tana shirin kiransa ta ga wani kiran ya shigo wayarta, cikin girmamawa ta ɗauka tana faɗin, "Daddy ina kwana." Bai amsa mata ba ya furta, "Ina ƙofar gidanki ki fito yanzu za mu wuce gida." Rass! Raihan ta ji gabanta ya faɗi, tana shirin yin magana ta ji ya katse idonta ne ya ciko da ƙwallah. A hankali ta furta, "Na shiga uku me Alhaji ya ce wa Daddy ko shi ma sakina ya yi?" Hawaye na zuba ta zura takalminta ta fice, a bakin gate ta samu motar Daddy tana buɗe motar bayan ta dubi Daddy ta ce, "Daddy wallahi ban san komai ba sharri ne aka yi min." Kallonta ya yi ganin tana kuka ya sa ya yi tsammanin ko ta san abin da ya faru, amma daga yanayin maganrta ya fahimci ba abin da yake tsammanin ba ne. Cikin tausayawa Daddy ya ce, "Da aka yi me Raiha? Ki gaya min tsakaninki da Allah Raihan." Raihan bata ɓoye wa Daddy komai ba daga ƙarshe ta fashe masa da kuka tana faɗin, "Don Allah Daddy ka gaya masa ba na son ya sake ni ban san me mutane za su ce ba. Idan ya sake ni mutane za su ci gaba da surutu akaina kamar yadda suke yi a baya." Tausayin Raihan ne ya kama Daddy ya girgiza mata kai sannan ya ce, "Mu wuce gida tukunna." Daga haka Daddy ya tayar da motarsa suka wuce gida.