← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 110

Sashe 27

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Abar bauta na tafiya Raihan ta miƙe tafara zaga lungu da saƙon da ke cikin tsibirin ƙungiya, daga can bayan wani dutse matatar jini ce a daskare. Hannuwan Raihan ne suka fara fidda wasu manyan farata, tana ƙarasawa wurin ta kafa hannuwanta a kan daskararran jinin da ya daske tamkar ƙanƙara, da hannunta ta fara kankararsu tana sakawa a baki tana shanyewa. Sai da ta sha ta yi ƙat sannan ta miƙe daga wurin tana yin gaba ta faɗi a wurin bacci ya yi awon gaba da ita. Raina ba ita ta farka ba sai yamma liƙis tashi ta yi zaune tana mittsika idanu, kai tsaye banɗaki ta faɗa ta fesa wanka sannan ta fito ta zauna a gaban mudubi tana shafa mai. A hankali ta wayarta ta fara ringing, daga ita sai ɗan ƙaramin towel ta ƙarasa ta ɗauki wayar, ganin baƙuwar lamba ya sa ta yi guntun tsaki ba tare da ta ɗauka ba. Ɗauko wayar ta yi ta ajiye a kan mudubi tana ci gaba da gyaran gashi da yake ta wanke kanta, tana tsaka da taje kai ta sake jin wayar ta sake ringing a hankali ta kai hannu ta ɗauka sai da ta yi kamar ba za ta ɗauka wata zuciyar ta bata umarni akan ta ɗauka. Cikin sanyayyar murya ta ɗauka tana furta, "Hello!" Sai da aka ɗauki ƴan sakanni sannan aka amsa da faɗin, "Assalamu alaiki." Taɓe baki ta yi bata amsa ba ta furta, "Da wa nake magana?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewar, "Yin sallama ko amsata samun lada ne ga duk wani musulmi." Raihan ta yi tsaki a fili tana faɗin, "Idan baka da abin yi ni ina da shi." Bata jira cewarsa ba ta katse wayar." Duk da tana cikin ɓacin rai hakan bai hana ta sakin wani malalacin murmushi ba, a fili ta furta: "Wai ni zai nunawa muhimmancin sallama hmmm." Miƙewa ta yi ta ɗauko doguwar rigar atamfa mara nauyi ta saka don ta jima bata saka atamfa ba, haka kawai ta ji tana sha'awar saka su. Kan katifa ta koma ta kwanta ta buɗe Data ta shiga kafofin yanar gizo. Tana nan zaune Mommy ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, murmushi Raihan ta yi mata ba tare da ta amsa sallamarta. Mommy na tsaye daga bakin ƙofa ta ce, "Raihan yau duk wuni guda ban ji motsinki ba, an ya yau ko abinci kin ci kuwa." Raihan ta shafa cikinta tana cewa, "Mommy wannan cikin nawa ai har zuwa gobe ba lallai na buƙaci abinci ba." Hararar wasa ta yi mata ta ce, "Saboda kin cinye abincin gidan?" Raihan ta yi dariya ta ce, "Allah mommy na ƙoshi abincina na musamman ne." Mommy ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya shirya min ke wannan rashin cin abincin nan naki sai na nemar miki magani." Wayar Raihan ce ta sake ringing ta ja guntun tsaki za ta ajiye Mommy ta ce, "Ba kiranki ake yi ba." Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Wallahi mommy wani sakarai ne zai dame ni a waya." Mommy ta yi girgiza kai tana faɗin, "Kika sani ko classmate ɗinki ne ta yuwu ma gaisuwa za su yi miki tun da na san Intisar za ta sanar da su." Ba don son ranta ba Raihan ta ɗauki wayar tana faɗin, "Ya aka yi?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewa, "Ina neman Saleem ya aka yi na ji number sa mace ta ɗauka?" Raihan cire wayar ta yi daga kunnenta ta ƙurawa lambar ido takaici ya rufeta, tana tsaka da nazarin irin baƙar maganar da za ta caɓa masa ta ji ya ci gaba da cewa, "Na rasa rawar kai irin na wasu yaran idan baya kusa in ya zo ki ce masa Salman ya kira, amma don Allah ki ce ya koya miki darasin sallama da amsata." Yana ƙarasa maganar ya katse wayar, cikin masifa Raihan ta dura wani uban ashar. Da sauri Mommy ta kai mata duka tana faɗin, "Wai me yake damunki ne Raihan?" A zafafe Raihan ta sanarwa da Mommy abin da ya gaya mata, Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce: "Hala sakarcin da kika saba kika yi masa." Raihan ta zumɓuri baki gaba ta juya ta yi kwanciyarta, Mommy ta zagayo ta gabanta tana faɗin, "Raihan ki haɗa kayanki idan Allah ya kaimu gobe za mu wuce india akwai wani Dr da za a haɗa mu da shi." Raihan tana daga kwance ta ce, "Tuni na riga da na san da tafiyar, abin da ya rage mu ƙarasa." Mommy bata kawo komai ba ta fice daga ɗakin.

Duk wani shirye-shiryen tafiya da ake yi Huzaifa yana sane da tafiyarsu Raihan, don lokacin da Dr ya yi waya da Daddy waya suna gamawa Huzaifa ya sake shafarsa, a nan take wurin ya faÉ—i bacci ya yi awon gaba da shi. A daren ranar ya dawo gidan su Raihan cikin surara Mama Uwani, Mommy ta yi mamakin ganin Mama Uwani don sun gama magana akan kwana za ta yi amma da ta ce musu mai jiki da sauki duk babu wanda ya kawo komai a ransa.

WASHEGARI.

Tun da safe su Mommy suka kammala shirinsu tsaf, Raihan ma ta shirya cikin riga da wando. Hannunta saƙale da baƙar jaka ba ƙaramin kyau ta yi ba, wayarta ce ta fara ringing tana ɗaukota ta ga number Intisar. Murmushi ta yi ta ɗauka da sallama tana faɗin, "Intisco baby." Daga can ɓangaren Intisar ta amsa mata da cewar, "Besty ya kun tashi ko yaya? Kin san yau muka yi da ƴan Department ɗinmu za su zo miki gaisuwa." Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Yanzu za mu ƙarasa airport ayya ke gaya musu dalilin tafiyata amma ai ina jin bai fi mu yi two weeks ba." Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama.

ƘASAR INDIA

Tun daga Nigeria Daddy ya sanarwa da wani abokinsa da ke aiki a cen maganar zuwanci, da farko sun so sauka a hotel amma Alhaji Yusuf ya nuna sam sai dai su sauka a gidansa. A ranar da suka sauka Daddy na sanarwa da Alhaji Yusuf asibitin za su ziyarta ya yi jim don ko a gidan talabijin bai taɓa cin karo da sunan asibitin ba, da mamaki ya dubi abokin nasa ya ce, "Abokina wai har yanzu wannan matsalar dai ita ce?" Daddy jiki a sanyaye ya ce, "Abu ɗaya muke fama shekara da shekaru." Alhaji Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Shi kenan babu abin da yafi ƙarfin Ubangiji. Zan kira wani abokina don shi ne mai kula da asibitocin kuɗi masu zaman kansu na ƙasarnan, duk yadda muka yi zuwa safiya za ka ji ni amma lamarin ciwon nan nata akwai ɗaure kai."

Duk tattaunawar da ake yi Huzaifa na laɓe a ɓoye yana jinsu, babban kuskuren da ya so aikata wa shi ne na rashin kautar da tunanin Abokin Daddy, lokaci ɗaya dabara ta faɗo masa a daren ranar ya sace abokin Daddy zuwa tsibirinsa tare da buɗe masa ido da sabuwar India a wurin hatta iyalansa duk na bogi ya saka masa.

Abin da Huzaifa bai sani ba tun ranar da su Raihan suka zo ƙasar India aka ajiye masa jabun Raihan, Raihan ta koma cikin ɗakin arziƙi da zama. Duk wannan shirin na abar bauta ne, don ta ci alwashin aiwatar da komai cikin shiri ba tare da Huzaifa ya fahimci wani abu ba. A yanda Huzaifa ya so, ya so ace ya jinkirtar da rahin Raihan dukda Jabbul-ƙasi ya sanar da shi babu wata dabara ko hikima da ta rage masa game da Raihan matuƙar bai kai ziyara ga Burtultika ba, amma kafiya da taurin kai irin nasa ya sa ya jarraba kawo ta ƙasar India domin a nan babbar da'irarsa take. Sai dai duk wannan abin da ake ciki daga Daddy har mommy babu wanda ya fahimci shirin Huzaifa, saboda ya kaisu babban asibitin kuɗi da asibitin da likitocin duk na buɗewar ido ne da Huzaifa ya yi musu, gabaɗaya ba mutane ba ne har suka gama zaryar asibitinsu kuma a ganinsu buƙata ta biya don tun da suka zo babu wani abu da Raihan ta sake yi na tsoratarwa. Kwanansu goma sha biyar suka tarkato suka dawo ƙasar Najeriya zuciyar Mommy da Daddy fes, musamman Daddy da yake jin kamar an yi masa bushara da gidan aljanna.

Kwanansu biyu da dawowa Kabiru ya ƙarasa cikin Falon ya miƙawa Daddy wata farar takarda, a cewar Kabiru Dr Muhsin ne ya kawo masa don ya kira wayar Daddy ta daina shiga. Daddy na karɓa Kabiru ya juya ya fice, don har lokacin jikinsa a naɗe yake saboda baya son ko kaɗan wani ya fahimci halin da yake ciki. Buɗe takardar ya yi cikin mamaki yana faɗin, "Ni fa kaina ya fara kullewa ya za a yi ace min Dr Muhsin ya riƙa zuwa nemana bayan ya san da tafiyarmu." Daddy ya ƙarasa maganar yana buɗe letter hannunsa, a fili ya fara karantawa Mommy na sauroronsa don ita kanta komai ya fara kwnace mata. Takardar ta ƙunshi ban haƙuri da Dr ya ke yi ga Daddy akan ya nemarwa Raihan wani likitan saboda rashin ƙwarin jiki da baya samu, daga ƙarshe ya ƙare maganar da cewar ya yi ta kiran wayarsa baya samunsa. Mommy ce ta riga Daddy maganar da cewar, "Tabbas akwai wani ɓoyayyan al'amari domin lamarin akwia rikitarwa." Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni kaina al'amuran sun fara sha min kai." Sun jima a wurin suna tattaunawa daga ƙarshe Daddy ya yanke shawarar zuwa ya samu Dr Muhsin har Office ɗin sa.

Bayan Wasu Kwanaki.
Chapter 27 · 0% Book details