← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 110

Sashe 34

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mommy ban da sauri babu abin da take yi kamar za ta tashi sama, duk wanda ya ga irin saurin da take yi sai tabbatar da tana cikin halin damuwa. Tana zuwa bakin titi ta fara taron adaidaita sahu don ko kaɗan bata yi tunanin ɗaukan mota ta fito da ita ba, sai da ta tsaida Adaidaita sahu sun fi uku babu wanda yake tsayawa saboda ganin irin yadda take yi musu magana a hargitse. Da ƙyar ta samu wani ya ɗauke ta tiryan-tiryan har Sharaɗa kwanar kasuwa a bakin Waraka Islamic chemist ya sauketa, ko waige mommy bata yi ba da ta sauka sai da ya ƙwalla mata kira tukunna ta waiga, da hannu ta nuna masa alamar ya jirata gata nan zuwa. Mommy tana shiga bakinta ɗauke da sallama ta dubi mutanen wurin tana tambayarsu, "Don Allah ina Malam yake?" Wata mata sanye da hijabi har ƙasa ta ce, "Hajiya lafiya?" Mommy ta ce Malam nake nema yarinyata ce babu lafiya." Matar mai hijabin ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin ce don masu kalar hijabinta kusan su biyar ne a wurin da alama shi ne uniform ɗin su. Kan kujera matar ta nunawa Mommy ta ce, "Ki zauna yanzu Dr ya shigo bari a yi masa magana." Matar na gama magana ta wuce ciki. Bata jima ba ta dawo tama faɗin, "Za ki iya shiga." Tun matar bata rufe baki ba Mommy ta shiga office ɗin, tana shiga ta samu kan kujera ta zauna. A gaggauce mommy ta gaida Malam Usman, yana ganin yanayinta ya tabbatar da tana cikin damuwa. Duk abin da yake faruwa da Raihan da Mama Uwani sai da ta zayyane masa, ko kaɗan bai yi mamaki ba don wannan ba sabon abu bane a wurinsu kasancewar suna samun cases makamantan irin waɗannan har ma da waɗanda suka fi haka." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ɗaukota a wannan halin da take ciki akwai babban hatsari sakamakon halin da take ciki. Amma zan haɗa ki da ɗaya daga cikin ma'aikatanmu..." Da sauri mommy ta haɗa hannuwa biyu tana faɗin, "Don Allah Malam ka taho mu tafi tare." Murmushi Malam Usman ya yi ya ce, "Hajiya don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba wani babban lamari ba ne a wurinmu, ina nufin zan haɗa ki da Malama Nafisa ku tafi zan shiga motata sai na riƙa bin ku a baya." Cikin gamsuwa da maganar Malam Usma Mommy ta miƙe tsaye tana faɗin, "To Malam Allah saka da alheri." Mommy na fitowa Malam Usman na biye da ita nan take ya sanarwa da Malama Nafisa abin da yake tafe da Mommy, Adaidaita sahun da Mommy ta zo a shi suka tafi da ita, motar Malam na biye da su tiryan-tiryan har suka ƙarasa ƙofar gidan Daddy. A kunyace Mommy kalli mai adaidaita sahun ta ce, "Don Allah bari na shiga na ɗauko ma kuɗin." Ganin abin da yake faruwa ya sa Mai ɗan sahun bai damu ba, don ya san lalura bata wuce kan kowa ba. Da ƙarfi mommya ta riƙa bugun ƙofar babu jimawa Kabiru ya buɗe mata, a gaggauce ta karɓi rancen dubu biyu a wurinsa tana miƙawa mai ɗan sahun ta juya suka shiga da Malam, Nafisa da Mommy.

Su Goggo na harabar gidan sun yi carko-carko Goggo na ganin Malam Usman kamar ta sanshi ta rangaɗa kabbara tana ci gaba da cewa, "Ka ga Ulama'u magada Annabawa." Inno ta ƙarasa gabansa ido ɗauke da ƙwalla ta ce, "Yaro ko wata biyu ba a yi da mutuwa Ƴata Hasiya ba yanzu ga Audullahi yana can ina jin tuni Aljanu sun riga da sun jajjage namansa." Malam Usman ya kalli Inno lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, cikin tattausan lafazi ya ce: "Insha Allah babu abin da zai faru da shi sai alkairi, bari na shiga ciki." Malam Usman ya yi gaba Nafisa da Mommy na biye da shi, daga Inno har Goggo babu wacce ta motsa ƙafarta don ta shiga cikin gidan.

Malam har ya je bakin ƙofar ya dubi Mommy ya ce, "Babu Famfo a kusa ina son na yi alwala." Da hannu Mommy ta nuna masa can gefe famfam da Kabiru yake amfani da shi. Sai da ya yi alwala sannan ya tunkari ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a, mommy na biye da shi amma ilahirin jikinta rawa yake tana tsoron abin da Raihan za ta aika da halin da Daddy yake ciki. Tsit cikin falon ya yi kamar babu kowa a ciki, Malam Usman ya kalli Mommy ya ce, "A ina yarinyar take?" Mommy ta fara waige-waige ta ce, "Ga dai ɗakinta can, amma lokacin da ta biyo mu a falon nan na barta." Jinjina kai Malam ya yi yana faɗin, "Za ki iya duba mana cikin sauran ɗakunan don mu san a wanne take?" Da sauri Mommy ta ce, "A'a Malam don Allah ka duba da kanka."

Lokacin da Raihan ta koma cikin ɗakinta wurin da Daddy yake ta tunkara a haukace tana faɗin, "Duk wanda ya nemi raba ni da matata sai na hallaka shi, Raihan matata ce mallakina ce babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da ita." Ilahirin jikin Daddy ban da rawa babu abin da yake yi, ga jinin da yake zuba daga jikinsa na ciwon da ta ji masa ga gumi tuni ya haɗu ya yi sharkaf, ya gama saddaƙar da rayuwarsa don gani yake tashi ta ƙare a kowanne lokaci Raihan za ta iya cimmasa, tun yana kukan zuci har ya fito fili ya fara kuka da hawaye shaɓe-shaɓe. Yana daga cikin banɗaki ya ji muryar mommy da Malam Usman suna magana, da ƙarfi ya ware murya yana faɗin, "Zainabu ku kawo mun ɗauki ina cikin banɗaki." Jin haka ya sa Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam ga Mahaifinta can yana ɗakinta." Da sauri Malam Usman ya nufi hanyar ɗakin sauna zuwa kai tsaye banɗaki suka ƙarasa Mommy ta ce, "Daddyn Raihan buɗe mu ne." Daddy da sauri ya amsa, "Zainabu kin tabbata ku ne kar na buɗe ta hallaka ni." Dariya ce ta so ƙwacewa Malama Nafisa, mommy ta ce, "Mu ne Daddyn Raihan tare muke da Malam." Daddy ya buɗe ƙofar yana zuro kai a hankali, sai da ya tabbatar da su Mommy ne sannan ya buɗe ƙofa. Yana fitowa Raihan ta shiga ɗakin a bakin ƙofa ta tsaya ta riƙe ƙugu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, da sauri Daddy ya juya zai sake faɗawa banɗaki Malam Usman ya fara takawa gaban Raihan, ko motsi Raihan bata yi ba cikib wata irin fusatacciyar murya ta fara magana.
Chapter 34 · 0% Book details