← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 110

Sashe 41

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Malam Usman da Daddy kusan a tare suka yi dirar mikiya a gaban Raihan, da sauri Daddy ya riƙe ta a gigice yana faɗin: "Raihan titi ne fa." Da wata irin murya mai ban tsoro Raihan ta dube shi idanunta suka ƙara firfitowa ta ce, "Ni ba ƴarka Raihan ba ce." Malam Usman ya kama hannun Raihan a fusace ya fisgota gefe, duk yadda Raihan ta so fisge wa ya gagara don haka Malam Usman ya ja hannunta har cikin ɗakin da suke kwantar da marasa lafiya. Kowanne ɗaki mutum biyu ne sai dai akwai ɗakin mutum ɗaya idan kana da buƙata, sai dai kowanne da tsarin yadda kuɗinsa yake. A ɗakin mutum ɗaya aka kwantar da Raihan, Malam Usman ne ya buƙaci a kulle ta a ɗakin ba tare da kowa ya shiga ba saboda gabatowar sallar magriba. Mommy gabaɗaya kuzarinta ya ƙare saboda lamarin ciwon Raihan kullin gaba yake yi, don haka ta jima tana addu'a bayan ta idar da sallar Magriba. Malam Usman bai buɗe ɗakin da Raiha take ciki sai da ya haɗa kayan magungunansa wuri ɗaya tare da ruwan addu'ar da yake ƙone jinnu. Shi da ma'aikatan wurin mata suka shiga wurinta tana zauna a ƙasa ta ɗaga kanta sama Tana ganin Malam Usman ta miƙe tsaye tana wurga masa mugun kallo, Malam Usman turare ya fara yi mata sannan ya ɗauko turaren miski tare da wani garin magani ya sake shaƙa mata sannan ya yi bismillah ya fara yi mata ruƙiyya. Wannan karan Huzaifa ya daɗe bai yi magana ba har sai da Malama Zainab ta ce, "Malam ina ga kamar baya jikinta fa." Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Malama Zainab kenan ya yi lamfa ne don ya shammaci hankulanmu, amma har yanzu yana jikinta. Kin san waye Jinnul-ashiq kuwa? Kin san me ake nufi da Zaijatu Jinnul-ashiq? Kina tunanin matar aljani daidai take da sauran mata? Sam ki sake hankalta domin matuƙar namijin aljanin soyayya ya auri macen bil'adama akwai aiki ja kafin a samu a rabata da shi. Duk wannan abin da yake yi iya taku ne, kuma ba zai yaudare ni ba don na kara da waɗanda suka fi shi saboda haka mu ci gaba da abin da yake gabanmu." Nan take suka ci gaba yi wa Raihan ruƙƙiya sai da suka kusa shafe awa ɗaya da rabi sannan Huzaifa ya fara magana cikin tsananin azaba. "Ya isa haka Malam zan fita daga jikinta wannan karon ba da wasa nake yi maka ba." Malam Usman ya ce, "Huzaifa ka yi mana wasa ka gani ai ga fili ga mai doki, yanzu tun wuri ka fice daga jikinta kafin na ƙarasa babbake ruhinka." Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a wahale ya ce, "Amma matuƙar ka raba ni da ita wallahi ba a yi mini adalci ba domin ba ƙaramar bauta na yi mata ba, yanzu kana nufin ta tashi a banza kenan." Malam Usman ya bashi amsa, "Dama garin banza ai a farau-faraun wofi yake ƙare wa, me ya sa baka zauna ka yi wa matarka wahalar ba? Raihan jinsinka ce da za ka bauta mata da aikin wahala?" Wannan magana ta Malam ba ƙaramin tunzura Huzaifa ta yi ba, a hassale ya dubu malam yana cewa: "Duk duniya babu macen da nake tsananin kishi kamar Raihan don haka ba zan taɓa bari wani ya raɓe ta ba, mahaifinta ma kulawar da yake bata wani lokacin ɓata min rai take don dai kawai na san babu aure a tsakaninsu ya sa ban taka masa burki ba." Daddy da yake ta waje ya ji abin da Huzaifa ya faɗa nan take ya hau raba idanu don ba ƙaramin tsorata ya yi da lamarinsa ba.

Ganin yana ɓata wa Malam lokaci ya sa ya ci gaba da ƙone shi da ayara Allah, faɗuwa Raihan ta yi a can gefe tana sauke ajiyar zuciya. Malam ya ji sautin wani tsoho ya fara magana, "Saboda me za ka riƙa azabtar min da jika babu gaira babu dalili? Da farko na yi kawaici don na san Huzaifa baya jin magana amma azabtarwar ta yi yawa ai. Kana ta iƙirari Huzaifa ya auri bil'adam ko me ya faru ba ku kuke ja ba? Idan matanku sun killace kansu za mu gansu mu yi sha'awa ne? Ko kuwa haka kawai sai mu auri macen da bata burge mu ba? Idan haka ne ai da gabaɗaya mun aure matan bil'adam. Ni na san waye Huzaifa farin sani, kuma ni na haifi mahaifinsa. Ni hatsabibin Aljanine har bil'adam ina basu kariya, amma tun da na ga Huzaifa ya dage akwai dalilinsa na shiga jikinta." Malam Usman ya mayar masa da martani, "Kenan kana ɗaure masa kar ya fita daga jikinta ko?" Kakan Huzaifa ya amsa da cewa, "Ban ɗaure masa komai ba amma ka yi nazari ka duba irin abubuwan da ƴaƴanku na bil'adam suke yi, kai ko a cikinku na san da babu hukunci maza da yawa sai sun riƙa afkawa mata a titina. Ba zan ɓata lokacina a nan ba domin ina da aikin yi yau zan kashe wani babban mutum a duniyarku, amma ka sani matuƙar aka kashe mini jika akwai mummunan mataki da zan ɗauka." Malam Usman na shirin yin magana Kakan Huzaifa ya matsa daga wurin. Malam bai saurara masa ba ya ci gaba da ƙone Huzaifa, cikin galabaita Huzaifa ya furta: "Dakata Malam na yi maka alƙawari matuƙar ka bar ni zan fita daga jikinta amma don Allah ka barni na sanar da kai abin da ya kaini jikinta." Malam Usman banza ya yi da Huzaifa sai da ya ga ya galabaita sannan ya rabu da shi ya ce, "Ina jin ka, a ina ka haɗu da ita?" Huzaifa ya sauke ajiyar zuciya a galabaice sannan ya ce, "Wata rana..."

TARIHIN SU MOMMY.

Malam Bala Shu'aibu shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifin Mommy amma mutane da dama sun fi saninsa da Malam Bala Magini. Asalinsa ɗan garin Albasu ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da suke cikin garin Kano, ya taso su bakwai a gidansu amma shi kaɗai ne namiji a cikin ƴan uwansa duk mata ne. Mahaifinsu Malam Shu'aibu malamin makarantar tsangaya ne yana da almajira da yake koyar da su, wannan dalilin ya sa Mahaifin Mommy ya taso cikin da ilimin addini mai zurfi. Sai dai abu ɗaya mahaifinsu ya gindaya musu karatun boko, don ko kaɗan bai amince da karatun boko ba shi ya sa ƴaƴansa mata suna fara zama ƴan mata yake aurar da su. Malam Bala ya so karatun boko a lokacin da Mai garin Albasu ya kawo musu wannan ci gaban sakamakon gwamnatin jaha da ta gina musu ƙananan makarantun boko a cikin gari, mutane da dama ba su karɓi abin ba amma da Mai gari ya wayar musu da kai sai wasu daga ciki suka amince wasu kuma suka juya wa abin baya aciki har da Mahaifinsu Malam Bala Magini. Dole ƙanwar na ƙi ta sa ya haƙura da karatun ya kama na addini hannu bibbiyu, da ya fara zama saurayi sai ƙanin Mahaifiyarsa yake tafiya da shi wurin aikin leburanci. Tun bai iya ba har ya ƙware ya iya gine-gine kala-kala, a lokacin iya cikin garin Albasu kawai suke yin aiki amma daga baya sai Allah ya sa masa nasibi yake samun aiki har cikin garin kano.

Zinaru Sama'ila Mai kaba shi ne ainihin sunan Goggo ita ma ƴar garin Albasu ce, ita kaɗai ta taso a wurin Mahaifiyarta. Amma a wurin Mahaifinsu su goma ne da yake matan aurensa Uku, Mahaifiyar Goggo ita ce amarya ta yiyyi ɓari kafin cikin Goggo ya zauna sai daga baya Allah ya zaunar mata da cikin Goggo aka haifeta. Mahaifin su Goggo sana'ar Kaba yake a garin Albasu duk garin babu wanda bai san shi ba, ko daga tasha ka tambayi gidansu kai tsaye za a kaika cen. Ta yi karatun addini daidai gwarwado macece mai barkwanci, amma bata da san raini. Mahaifin Mommy ya haɗu da Goggo ne a makarantar mahaifinsa, sakamakon nan ne makarantar allon da Goggo take zuwa ita da sauran ƴan uwanta. Tun suna soyayyarsu a ɓoye har manya suka shiga magana daga ƙarshe aka tsayar da rana aka sha shagalin aurensu. Malam Bala Magini yana matuƙar nuna kulawarsa ga Goggo, haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali, Goggo sai da ta shekara biyu sannan ta samu ciki tana cikin ta uku Allah ya sauke ta lafiya ta haifo Ɗanta namiji. Ba ƙaramin farinciki suka yi ba ranar suna aka saka masa suna Abubakar, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Abubakar na da shekara huɗu Goggo ta haifi ƴarta mai suna Hafsa, sai dai kafin suna Allah ya yi mata rasuwa. Rasuwa Hafsa babu wuya Goggo ta sake samun wani cikin bayan wata tara ta sake haifo ƴa mace aka saka mata suna Zainabu (Mommy) Daga kanta sai da Mommy ta shekara biyar sannan Goggo ta sake haihuwar ƴa mace aka mayar mata da suna Hafsa. Daga kan wannan hafsar Goggo bata sake haihuwa ba, haka suka ci gaba da kula da ƴaƴansu cikin rufin asiri duk da su ba masu kuɗi ba ne.

Bayan Wasu Shekaru.
Chapter 41 · 0% Book details