← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 110

Sashe 77

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mommy da su Inno suna zaune a falo Raihan ta shiga da gudu tana dariya, don haka kawai idan tana tare da Kabiru ko a cikin fushi take sai zuciyarta ta yi wasai. A tsakiyar falon ta tsaya tana mayar da ajiyar zuciya haɗe da riƙe ƙugu, Goggo ta riƙe baki tana cewa, "Kai gaskiya wannan yarinya baki da ɗabi'ar aziƙi saboda Allah baki da aiki sai na gudu kamar kin yi wa sarki ƙarya ya sa a kamo ki?" Mommy ta dubi Raihan ta ce, "Raihan kedai bakya girma, so kike Muhammad ya taso ki koya masa wannan guje-gujen naki?" Zama Raihan ta yi a kujera sannan ta ce, "Wallahi Mommy Fullo ya raini." Mommy ta yi salati haɗe da kai wa Raihan duka a baya ta furta, "Yanzu saboda Rashin kunya Kabirun za ki ce ya rainaki." Inno ta yi guntun tsaki haɗe da banka wa Raihan harara ta ce, "Wannan sakarcin da kike yi ba Kabiru ba nan gaba Muhammadu sai ya rainaki." Raihan ta miƙe tsaye tana murguda musu baki ta wuce ɗakinta haɗe da cewa, "Allah ya kiyaye wallahi duk ranar da ya min fitsara sai na yi masa Walmukalifatu." Mommy ta yi dariya ta ce, "Ji sakarcin banza yanzu MD kike gaya wa haka kamar wani sa'anki." Raihan na shiga ɗakinta ta faɗa gadon haɗe da lumshe ido nan ta tuno fuskar Kabiru ta yi lokacin da ya tsare gida yake tambayarta, murmushi ta yi haɗe da furta: "Fullo! Fullo ka ga makwancina da yawa wallahi " Al'amin shi ne abu na biyu da ya faɗo mata, nan take ranta ya sake ɓaci musamman da ta tuna irin ɗiban karan mahaukaciyar da ya yi mata haɗe da kalaman da ta riske shi yana faɗa a waya. Uwa-uba kuma wayar Malam da ya yi ita ta sake tsinke igiyar da ta yi shanyar kwanciyar hankalinta akai, lumshe ido ta yi tana furzar da iska mai zafi nan take hawaye ya fara bin idonta. Filo ta janyo ta rungume a hankali ta furta, "Ba ni na ɗora wa kaina ba soyayyarka ta dira a zuciyata tamkar dirar mikiya. A duk bugun numfashi wutar ƙaunarka ƙara ruruwa take a cikin raina sai dai ga dukkan alamu babu ni a zuciyarka, don Allah ka so ni ka ƙauna ce ni idan ba haka ba zuciyata za ta iya buga wa a kowanne lokaci." Haka Raihan ta ci gaba da surutai ita kaɗai ganin damuwa ta yi mata yawa ya sa ta ɗauko wayarta ta shiga dandalin sada zumunta.

Washegari da daddare su mommy suna zaune suna hira Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Mommy na ganinsa ta miƙe ta tarbe shi tana cewa, "Daddyn yara yau ka daɗe tun magriba nake saka ido." A gajiye ya zauna Raihan ta yi masa barka da zuwa, su Inno ya fara gaisarwa sannan ya ce, "Wallahi a gajiye nake. Ni ba na manta Malam ya ce za mu kai gaisuwar Al'amin gidansu yarinyar da yake nema ba, wallahi sai ɗazu ya kirani to mun yi niyar zuwa da rana sai kawai muka yanke shawarar zuwa da dare. Mun je an saka ranar yaron wata uku, ashe wai ya jima yana jiran yarinyar sai da ta kammala karatu." Tun da Daddy ya fara maganar Mommy take kallon Raihan ƙasa-ƙada gabanta na faɗuwa, don tun Raihan na ɓoye soyayyar Al'amin har sai da watarana ta sanar wa Mommy, sai dai tun a lokacin mommy ta yi mata nasiha akan ta cire soyayyar Al'amin daga zuciyarta. Mommy na shirin yin magana sai ji suka yi Raihan ta fashe da kuka, ta tashi da gudu ta wuce ɗakinta. Mamaki ne ya kama Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Lafiyar Yarinyar nan ko ciwonta ne ya dawo?" Mommy jiki a sanyaye cike da tausayin Raihan ta ce, "Babu ko ɗaya Daddyn Raihan, wallahi ba tun yanzu ba yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan wannan Al'amin ɗin, ko kwanaki dai da ta yi min maganarsa na ce mata ta fita daga harkarsa amma ta ƙi. An taɓa soyayya dole ne tun da shi bai taɓa nuna yana sonta ba..." Katse ta Daddy ya yi ta hanyar ɗaga hannunsa sama ya ce, "Dakata Zainab! Yaushe aka yi haka ban sani ba? Me ya sa baki gaya min ba tuntuni na yi wa Malam magana?" Ganin Daddy na son rufeta da faɗan da bata da laifi a ciki ya sa ta ce, "Idan ka gaya wa Malam, shi zai aureta ya zauna da ita? Daddyn Raihan kai fa namiji ne ka san yadda halin maza yake mace tana son su ma ya aka cika balle ita ta tsaga billenta ta nuna tana son shi. "Shiru Daddy ya yi ba tare da ya furta komai ba, ya miƙe ya nufi ɗakin Raihan da yake jiyo shasshekar kukanta tun daga waje. Yana shiga ya tsaya daga jikin gadon Raihan ya furta, "Raihan!" Shiru ta yi ta ɗago tana goge ƙwallar idonta, sake ambatar sunanta ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Tun yaushe kike ƙaunar yaron nan baki gaya min ba." Hawaye na zuba Raihan ta ce, "An daɗe amma mommy ce ta hana ni." Daddy ya jinjina kai sannan ya ce, "Kin Makara Raihan saboda Mahaifin yaron nan ya ɗauke tamkar ɗan uwansa yanzu me kike so naje na gaya masa, tun farko da kin gaya min zan iya gaya wa Malam idan ya so sai a gaya wa yaron inkun daidaita shi kenan. Amma gaskiya a yanzu ina jiye miki wulaƙancin namiji saboda yana da wacce yake so, hasalima ya shafe shekara huɗu yana jiranta yanzu kina ganin za ki shiga zuciyarsa kamar waccen ne? Ki yi ta addu'a Raihan har Allah ya canza miki da wanda ya fi shi, a kullin zaɓin Allah shi ne zaɓi." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha sannan ya fito daga ɗakin, ai kuwa yana fita ta sake rushe wa da matsanancin kuka don har ji take zuciyarta na wani irin raɗaɗi kamar za ta hudo ƙirjinta.

Tun bayan faruwar wannan al'amarin Raihan ta yankar wa kanta tikitin zaman ɗaki bata da aiki sai na kuka da tunani, tun Mommy na fushi da ita har ta watsar ta fara rarrashinta amma duk a banza don ko abincin kirki Raihan bata ci. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta yi baƙi idan ka ganta sai ka rantse ta jima tana jinya, Kabiru tun yana saka idon ganinta har ya daina. Kuma a wannan lokacin bikin Al'amin bai fi saura wata ɗaya ba, har lokacih Daddy ya gagara sanar wa Malam halin da ake ciki, dom gani yake kamar ya so kansa da yawa. Wannan lamarin ba ƙaramin damunsa ya yi ba har sai da ya gagara wataran ya tambayi Daddy ita, Daddy shi kansa abin na Raihan ya fara ɗaga masa hankali don ko kaɗan baya ƙaunar wani abu da zai iya salwantar masa da rayuwarta. Sai dai Daddy yana jin daɗin irin kulawar da Kabiru yake bawa Raihan don haka ya ƙara shiga ransa, bayan ya bawa Kabiru amsa yana shirin tafiya Daddy ya kira shi da wata irin mura sannan Kabiru ya dawo. Cikin girmamawa ya russana Daddy ya ce, "Kabiru wani hukunci na yanke amma ban sani ba ko zai yi maka daɗi, amma na ce sai na fara jin ta bakinka duk da harkar ƙaruwa ce...

Eheeeem 🌚 na ce ba! To wai meye harsashenku? Barkanmu da juma'a bayin Allah🌚

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

42
Chapter 77 · 0% Book details