← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 110

Sashe 88

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tun da aka sallami Sumayya Al'amin ya koma ɗakinta da kwana, Raihan ce take komai a gidan ta girka musu abinci ta kai musu wani lokacin ma sai su kusan azahar bata ji motsinsu ba. Ga cin fuska kala-kala da take gani idan ta je kai musu abinci, wannan lamari ba ƙaramin sakata a damuwa ya yi ba ita da Al'amin sai kallo daga nesa, don haka ta ci alwashin samunsa su yi magana don ta gaji da irin zaman gadin da take yi, a ɓangare ɗaya ga wata irin kyara da ta lura yana yi mata abu kaɗan idan ta yi sai faɗa. A ranar wata Juma'a da safe yana shirin fita tana zaune a falo tana jiransa ta ji ƙamshin turarensa ya doki hancinta, muryar Sumayya ta ji cikin shagwaɓa tana faɗin, "Allah sai ka goya ni ka kaini gate haka kawai ka gama gajiyar da ni kuma ban fanshe gajiyata ba."Ji ta yi an buɗe ƙofar tana kallon wurin ta hango Al'amin rungume da Sumayya, ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da idonta haɗe da miƙe wa tsaye. Sai da ta gaishe shi ya amsa sama-sama sannan ta ce, "Dama magana nake son yi da kai." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Sai da kika ga na shirya za ki ɓata min lokaci." Sumayya ta sake maƙale shi tana zira ƙafafuwanta don ta sauka ta ce, "Haba Hubby ka saurareta mana." Al'amin ya dubi Raihan ya ce, "Ina jin ki." Jiki a sanyaye Raihan ta ce, "Mu je ɗaki." Dariyar ƙeta ce ta ƙwace wa Sumayya sai ta maze ta ce, "Hubby bari na shiga ciki don gyaran ɗaki zan yi." Tsaki Al'amin ya yi ya wuce ɗakin Raihan, Sumayya na ganin haka ta faɗa ɗaki tana tsallen murna da sauri ta ɗauki waya ta kira Mami, tana jin ta ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce: "Mami buƙata ta biya lamari na ta ɗaukan zafi fa." Amsa mata Mami ta yi cikin farinciki sannan Sumayya ta ci gaba da yi mata bayanin irin zama da Raihan take yi da Al'amin, cikin jindaɗi Mami ta sake ɗora Sumayya akan miyagun shawarwarinta.

Al'amin na shiga ya dubi Raihan cikin kallon tsana ya furta, "Sauri nake ina jin ki." Ƙwalla ce ta ciko idon Raihan murya na rawa ta ce, "Yau kimanin kusan wata biyu da wani abu kenan da aurenmu amma..." Da sauri Al'amin ya katse ta da cewar, "Dakata don Allah, wai ni da bakina na je gidanku na ce ina sonki ne? Na san maganar da kike shirin yi wato can mazajen da kika aure sun koya miki jaraba da rashin haƙuri har ta kai saboda ina bawa matata kulawa kina baƙinciki ko? Don Allah matsa karki ɓata min lokaci." Fuuuu Al'amin ya saka kai ya fice ya bar Raihan sake da baki, don bata yi tsamanin lamarin Al'amin haka yake ba. Durƙushewa ta yi a wurin tana wani irin kuka mai ban tausayi, ta jima tana abinta sannan ta koma kan gado ta yi kwanciyarta don zuciyarta wani irin turiri take yi mata. Tana cikin wannan yanayin ta ji wayarta na ringing lambar Mama Hafsa ta gani, sai da ta goge hawayenta ta ɗauka amma kalma ɗaya za ta furta ka fahimci yanayin da take ciki ba mai daɗi bane. Sai da suka gama gaisawa Mama hafsa ta tambayeta abin da yake damunta don ta fahimci muryarta, Raihan dama zuciyarta cunkushe take da baƙinciki don haka tana jin tambayar Mama Hafsa ta fashe da kuka, lallashinta Mama Hafsa ta yi sannan Raihan ta sanar da ita gutsire daga cikin irin zaman da suke yi, duk da Raihan bata sanar da ita babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaminta da Al'amin ba ta fahimci duk maganganun Raihan, don haka ta ce mata za ta ƙaraso gidan. Raihan ta ji daɗi sosai ko ba komai ta san Mama Hafsa za ta zo ta tausheta ko zuciyarta za ta yi sanyi. Kamar yadda Mama Hafsa ta faɗa ko awa ɗaya da rabi bata yi ba ta ƙaraso gidan, a lokacin Sumayya na zaune a falo. Cikin mutumci suka gaisa da ita sannan ta wuce ɓangaren Raihan. Haka kawai Sumayya ta ji zuciyarta bata yarda da zuwan Mama Hafsa ba don ta yi zargin Raihan ce ta yi mata waya ta gaya mata wata maganar. Tana shiga ta samu Raihan zaune akan gado ta zabga uban tagumi, murmush Raihan ta yi mata sannan ta ɗebo kayan marmari da ruwan sha ta ajiye mata, ruwa kawai Mama Hafsa ta sha sannan ta dubi Raihan ya furta, "Kin ba ni mamaki Raihan." Gaban Raihan ne ya faɗi don haka ta fara ayyana wataƙila wani faɗan za ta yi mata haka ne ya sa koda wasa bata taɓa gayawa kowa halin da take ciki ba, tana cikin nazari ta riski muryar Mama Hafsa na ci gaba da cewa, "Yanzu kamar ba wayayya wacce take da ilimi ba za ki zauna kina shaƙar takaici da baƙinciki? yaron nan fa mijinki ne kamar yadda take a wurinsa kema haka. Ki riƙe tsafta kwalliya da dressing kala-kala, kuma ki daina cusa kanki wurinsa don wani lokacin namiji da gayya yake wulaƙanta mace musamman idan ya ga ta mutu akansa, duk abin da ya saki ki yi masa biyayya matuƙar ba saɓon Allah ba ne, komai ya yi zafi maganinsa Allah ki riƙe sallar dare kina kaiwa Allah kukanki, sannan ki dage da Azkar babu wanda zai ga kukanki da ikon Allah, kuma karki mayar da kanki sakarai kishiyarki ta rainaki ki ja ajinki da matsayinki." Jinjina kai Raihan ta yi a hankali ta furta, "Na gode Aunty insha Allah zan rinƙa yi." Mama Hafsa ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta ta ce, "Dole ki cire kunya ki ƙwaci kanki don kunyar mara kunya asara ce, ni yanzu zan wuce don wallahi ban yi niyyar zuwa gidanki yanzu ba, kar na zama uwar banza niyyata sai baɗi idan Allah ya sauke ki lafiya." Kunya ce ta kama Raihan har da rufe fuska sannan suka fito ta raka Mama Hafsa, a lokacin da suka fita Sumayya bata falon don haka Mama Hafsa ta wuce.
Chapter 88 · 0% Book details