Sashe 101
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya Kabiru ya warke garau ya koma bakin aikinsa, a hankali ya fahimci duk abin da yake faruwa don a wannan lokacin ya gano auren Raihan ne ya mutu har ta dawo gida da zama. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Al'amin don ji ya yi duniyar ta yi masa zafi ga takurar da Sumayya take masa don daga ƙarshe ma Mahaifinta ne ya kira Al'amin ya ce masa matuƙar yana son ci gaba da zama da Sumayya ya bashi sati guda ya je ya tafi da ita, idan ba haka ba sai dai ya sakar masa saboda ba za ta ci gaba da zama ba tare da ta san matsayinta ba. Tashin hankalin da ya sake zugar da shi har yake tunanin hanyar da zai samu Mahaifinsa da maganar, a ɓangare ɗaya kuma ga tunanin Raihan ya damalmala zuciyarsa har ji yake zuciyarsa na ingiza shi akan ya je ya nemi yafiyarta wataƙila idan ta ce ta yafe masa zai daina jin damuwar da ya yi da ita a zuciyarsa. Da wata safiyar Juma'a ya je gidansu ya samu Mahaifiyarsa ya sanar mata duk abin da yake faruwa dangane da maganar mahaifin Sumayya, Ammi ba ƙaramin tausayinsa ta ji ba sai dai ita kanta tana fargabar samun Malam ta yi masa magana don wancen karon bata ji da daɗi. Kallonsa ta yi ta furta, "Shi kenan ka je Al'amin zan samu Mahaifinka da maganar." Miƙe wa Al'amin ya yi har ya fara tafiya ya juyo ya ce, "Amm dama Ammi na ce..." Kallonsa ta yi ta ce, "Akwai wani abu ne?" Sunne kai ƙasa ya yi ya ce, "Wallahi Ammi na zalinci Raihan, gani nake kamar na je neman yafiyarta..." Da sauri Ammi ta katse shi da cewar, "Kai da bakinka kake faɗin ka zalinci Raihan Al'amin? Tabbas Allah ba azzalumin bawansa ba ne. Shi ya sa ba a wulaƙanta ɗan'adam a rayuwa duk ƙasƙancinsa domin baka san baiwa da martabar da Allah ya yi masa ba. Yarinyar nan ta nuna maka soyayya a duniyar nan amma ka yi amfani da wannan damar ka riƙa cusguna mata, ai shi kenan sai ka je idan ka samu ta saurareka to, idan baka samu wannan damar ba shi kenan. Ka ga wannan sai ya zama izina a gare ka domin ɗan'adam duk yadda yake yana da daraja." A hankali Al'amin ya fara tafiya yana zuwa bakin ƙofa suka haɗu da Malam, gaisawa kawai suka yi Malam ya fahimci yana cikin matsananciyar damuwa. Yana shiga cikin dabara Ammi ta sanar masa abin da yake faruwa da Al'amin, murmushi ya yi ya furta, "Yaro man kaza. Shi kenan Allah ya kaimu ranar Litinin sai ya je ya tafi da ita. Ita kuwa Raihan yanzu ai baida iko da ita ruwanta ne ta saurare shi ko akasin haka. Wallahi ni na san dama haƙƙin yarinyar nan ba zai bar shi ba, Allah ya sa dai ta saurare shi." Ammi ta jinjina kai don ta fahimci kamar Al'amin ya faɗa tarkon son Raihan sai dai bata gaya wa Malam ba don ta san ba ƙaramin faɗa zai yi ba. Da daddare Al'amin ya fi minti talatin a ƙofar gidansu Raihan sai ya yi kamar ya ƙwanƙwasa ƙofa sai ya wata zuciyar ta hana shi daga ƙarshe ya yi ta maza ya ƙwanƙwasa. Yana bugawa Auwalu ya leƙa yana tambayarsa, Al'amin ya aro jarumta ya furta, "Am na ce don Allah Raihan za ka kira min." Da mamaki Auwalu ya ce, "Malam Raihan fa?" Al'amin ya ce, "Eh." Amsa masa ya yi sannan ya wuce cikin gida, a lokacin Raihan ita kaɗai ce a zaune a falo tana shan ruwan tea Auwalu na leƙawa ya ce, "Hajiya yanzu wani ya ce a yi sallama da ke." Da mamaki Raihan ta ce, "Ni kuma?" Aulwalu ya amsa sannan ta ce, "Ka je ka ce bata nan." Kamar yadda ta faɗa haka Auwalu ya koma ya faɗa sam Al'amin bai ji daɗi ba, don haka ya buɗe motarsa ya cito Memo ya yi rubutu ya miƙawa Auwalu ya ce ya bata. Ba musu Auwalu ya karɓa sannan Al'amin ya wuce gidan su Sumayya, yana zuwa kamar yadda ƙannenta suka saba tarbarsa a falonsu haka suka yi masa. Yana nan zaune ya ga wata baƙuwar lamba ta shigo masa har sai da ya ji gabansa ya faɗi, don ya ɗauka Raihan ce ta kira saboda a rubutun da ya yi har da lambar wayarsa a jiki. Da sauri ya fita ya zagaya ta bayan ɗakin su Sumayya ya ɗauka, yana ɗaga wa ya ji an yi sallama da muryar namiji. Guntun tsaki ya yi cikin girmamawa aka gaishe shi bayan sun kasa ya ji an ce, "Malam wallahi dama maganar Assignment ɗin da ka karɓa ranar ban zo ba shi ne..." Cikin takaici Al'amin ya furta, "Ban gaya muku a cikin rules and regulations ɗina ban da kira a min complain ba? Ba na son sakarcin banza da wofi." Bai jira cewarsa ba ya katse wayar. Yana zagayowa ta daidai windon ɗakin Mahaifiyar Sunayya ya ji muryar Mahaifiyar Sumayya na faɗin, "Ki tabbata kin ya sha lemon nan domin maganin da na karɓo a wurin Malam ya tabbatar min matuƙar ya sha lemon nan wallahi ba Raihan ba ko bebyn roba ba zai kalleta da sunan so ba." Sumayya ta shagwaɓe murya ta ce, "Mommy ina gidansa ma fa haka kika ce, wallahi hatta layar da kika ba ni na saka a cikin filonsa da wacce na binne duk babu wanda ya yi aiki. Ita kanta Raihan duk asirin da muke yi mata da banga yana wani tasiri a jikinta ba, har gwara lokacin da aka haɗa mata da jinin Kasa shi ne ta riƙa baccin nan. Ni kuma so nake yanzu na gama da Al'amin ko tsohon nan da yake shiga lamuranmu kar ya ce masa ya bi gabas ya bi." Jikin Al'amin ba ƙaramin sanyi ya yi ba, yana nan tsaye har ya gama jin duk irin hirar da suke yi. Yana jin alamun tahowar Sumayya da sauri ya wuce cikin falon, tana ganinsa ta yi farrr da ido tana faɗin, "Hubby ina ta jiranka ina ka je ko ka je yin waya da Raihan?" Murmushin ƙarfin hali ya ƙirƙiro ya ce, "Haba dai wani ɗalibina ne ya kira ni." Lemo ta tsiyayo masa tana fari ta miƙa masa sai da ya karɓa har ya kai bakinsa sannan ya cire ya ɗago yana kallonta ya ce, "Sumayya ada na ɗauke kina daga cikin sahun mata masu tunani ashe sam ba haka ba ne." Ras gabanta ya faɗi abinka da mara gaskiya a rikice ta furta, "Ni kuma me na yi?" Haɗe fuska ya yi sannan ya ce, "Yau da safe na tsinci layu a ɗakinki, ɗaya a cikin fulo ɗaya kuma a cikin kayana har da wacce aka binne a ɗakin Raihan. Sannan har wani wuri na ga an haƙa rami an binne abu a ɗakinki..." Shiru ya yi sai kuma ya kalli kofin hannunsa ya ce, "Sai kuma wannan lemon da na ji ana ce miki na mallaka ne, ashe dama soyayyar da kike min bata tsakani da Allah ba ce?" Hawaye ne ya fara zuba daga idonta ta furta, "Ka dubi girman Allah ka rufa min asiri Al'amin wallahi ba halina ba ne soyayyarka ce ta sa na kasa haƙuri har nake ganin ba zan iya haɗa ka da wata..." A fusace Al'amin ya furta, "Kin ci amanata kin cuci kanki, na so ki tsakani da Allah amma kike neman shan gaba tsakanina da iyayena, tir da halinki kin ba ni mamaki." Al'amin na gama maganr ya dire mata kofin ya fice a zafafe, don akwai ciwo wanda ka yarda da shi ka aminta da shi kake yi masa so na tsakani da Allah ya nemi cin amanarka har ta kai ga yana son ganin ya raba ka da mahaifanka. Hankali a tashe Sumayya ta bazama cikin ɗakin Mami tana ihu, kamar wacce ake kwarawa ruwan dalma.