← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 110

Sashe 107

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wata hanya da Al'amin zai bi ya samu Raihan ya kasa don haka wata dabara ta faɗo masa, searching ɗin sunanta ya yi ta shafin sada zumunta, nan take sunan da take kasuwanci da shi ya bayyana wato R-Raihan's Investiment. Farinciki ne ya mamaye zuciyarsa tamkar Raihan ɗin ya samu gabaɗaya, lambar da ya gani a jiki ya ɗauka don haka ya yi saving a wata sabuwar lambar wayarsa don ya tabbata idan ya yi mata magana da layinsa ta yuwu ta gano shi, don a sanin da ya yi mata na baya ta haddace lambarsa. Nan take ya yi mata magana ta Whatsapp. A lokacin bata online sai dai yana danna profile ɗin ta ya ga irin kayan da take oder da branches ɗinta, magana ya yi mata a zuwan zai sayi kaya. Ya yi mata maganar da minti goma ya ga ta duba ta yi masa replay wani irin farinciki ne ya kama shi, nan take ya buƙaci Acc number ta akan zai yi siyayya ta dubu ɗari biyar. Raihan ta ji daɗi sosai har sai da ta yi masa discount na 20k amma da ya tashi a madadin ya tura mata iya kuɗin da suka yi ciniki sai ya tura mata kusan ninkin haka. Ganin haka ya sa Raihan ta tambaye shi ko zai ƙara kaya ne amma ya ce a'a. Mai motar da yake kai mata kaya ta kira tare da bashi address ɗin wurin da za kai. A iya bakin titin Sharada Al'amin ya tsaya ya karɓi kayan ya tafi, da haka Al'amin ya samu mazauni a wurin Raihan domin tana girmama duk wani wanda ya sayi abu a wurinta. Don haka suke yawan gaisawa akai-akai da yake ya ci gaba da siyan kaya a wurinta. Ana cikin haka watarana Al'amin ya bijiro mata da maganar aure, ba ƙaramin dariya ya bata ba don a lokacin ta bashi amsa da cewar, "Yanzu kai ba mu taɓa haɗuwa ko waya ba mu taɓa yi ba sai ka ce kana so na." Al'amin ya yi mata replay, "Ai ba wani abu ba ne indai kin amince za ki aure ni a yanzu zan zo na same ki." Alamar dariya ta tura masa ta rubuta, "Ka yi haƙuri domin na riga da na rufe shafin aure a rayuwata." Duk yadda Al'amin ya so shawon kan Rainan fir ta ƙi amince masa daga ƙarshe ma sai ta daina yi masa replay koda ta ga abin da ya rubuto mata. Ganin wannan dabara bata kai shi ba ya sa ya yanke shawarar zuwa ya samu Daddy duk da yana tsanannin jin kunyarsa akan abin da ya yi wa Raihan. Ranar da ya je Office ɗin Daddy bai yi mamaki ba don tuni Malam ya gaya masa komai game da halin da Al'amin yake ciki, sai da Daddy ya gama sauraronsa sannan ya ce, "Insha Allah zan yi wa Raihan magana idan ta amince shi kenan saboda ka ga Raihan ba budurwa ba ce balle mu yi mata zaɓen miji da kanmu. Amma insha Allah za ta amince da buƙatarka, kar ka samu damuwa Allah ya shige mana gaba." Gwiwa a sanyaye Al'amin ya fita yana fita Daddy ya kira Malam bayan sun gaisa ya ce, "Gaskiya wannan abin da ake yi wa yarona ya yi yawa, a zo a mayar da auren nan ko ya samu kwanciyar hankali amma ka zuge yarinyar nan sai ja masa aji take. Wallahi kar na zuciya na nema masa wata tsaleliyar budurwar ya aura masa." Malam ya yi dariya sannan ya ce, "Ai ko ka nema masa ba zai so ta kamar Ƴata ba ka ga kuwa an yi aikin baban giwa." Daddy ya kwantar da murya ya ce, "Don Allah ya isa haka Malam zan je na samu yarinyar nan na yi mata magana." Malam ya ce, "Ai da ka bari an kwana biyu don ban so ya samu Raihan yanzu ba, na so ace sonta ya galabaitar da shi tukunna." Sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Daddy na zuwa gida ya samu Raihan da maganar Al'amin a zaton Raihan Daddy bai san yadda suka yi da Malam ba, sai da ya gaya mata ta yi ta mamaki sannan ya ce, "Ba tilasta ki na zo yi ba Raihan ki zaɓi zaɓin ranki, kin ga yau Alhaji Shatima kusan shekararsa guda da rasuwa. Kina da ƙuruciyarki don haka lokacin aure bai wuce miki ba. A baya Al'amin ya yi kuskure kuma ya gane kuskurensa don haka mai zai hana ba za ki yafe masa ki amshi tayinsa ba? Na san kin fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarki ta fannin auratayya amma haka ba shi zai sa ki ce ba za ki sake yin aure a rayuwarki ba. Ban yi miki dole ba amma ke kanki kin san yadda Al'amin ya haukace a soyayyarki, na sani kin sani ke ma kina ƙaunarsa kin ga tun da ya gane kurensa ki ba shi dama ya gyara, mahaifinsa mutumin kirki ne ya yi mana komai a rayuwa ko don darajarsa ya isa ya sa ki amince masa tun da kina ga da kansa ya baki shawarar irin shan ƙamshin da za ki yi masa. Atoh ni dai babu ruwana don na gayawa Baban naki idan ajin na naku ya tsinke babu ruwana, babu abin da zai hana aura masa tsaleliyar budurwa kina kallo mu sha biki ya tare da abarsa." Murmushi Raihan ta yi a kunyace tana rufe fuska ta ce, "Shi kenan Daddy Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya furta Amin sannan ya wuce part ɗin Mommy, a ranar ya sanar da ita da su Inno, da farko su Inno faɗa suka fara yi sai da Daddy ya nusar da su karamcin Mahaifin Al'amin da abin da ya yi musu dangane da ciwon Rainan sannan suka sauko suka saka wa komen auren albarka.

Daddy da kansa ya kira Al'amin ya gaya masa a kowanne lokaci yana iya zuwa hira wurin Raihan sannan ya tura masa da lambar wayarta, saboda farinciki har sai da Daddy ya fahimci halin da Al'amin yake ciki. Yana kira ya ji tana shiga amma ba a ɗauka ba, sai da ya kira a na biyu sannan ya ji ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta, "Wa'alaikis salam." Shiru ne ya biyo baya sannan ya ce, "Raihan don Allah ka yafe min duka abubuwan da suka faru a baya." Lumshe ido Raihan ta yi tana mamaki wai yau ita ce Al'amin yake bawa haƙuri haka. Murmushi ta yi ta ce, "Allah ya yafe mana bakiɗaya." Kame-kame Al'amin ya fara yin ganin haka ya sa Raihan ta ce masa tana da uzurin da za ta yi duk da ta faɗa masa haka ne kawai ba don tana da wani uzuri ba, kashe wayar ya yi yana jin farinciki a ransa. Ita kanta Raihan ta jima a wurin zuciyarta wasai soyayyar Al'amin na sake dawo mata sabuwa fil a ranta. Amma ta yi wa kanta alƙwarin za ta kiyaye wurin nuna soyayyarsa ba tare da ya fahimci har lokacin tana matuƙar sonsa ba. Sannu a hankali Al'amin ya kuma zaunar da soyayyarsa ɗaram a zuciyar Raihan, tun tana sha masa ƙamshi har ta fara sakin jikinta saboda yadda ta ga yana nuna mata kula da tsantsar soyayya. Duk wannan abin da yake faruwa Sumayya bata sani ba sai dai ta fahimci a ƴan kwnanakin yana cikin farinciki tun da har ita ma yana ɗan sakar mata fuska. Lokacin da Kabiru ya fahimci Al'amin ya koma wurin Raihan ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba amma ya san babu yadda zai yi don haka ya ci gaba da addu'a akan Allah ya cire masa soyayyarta, don ya san da ƙyar idan Raihan rabonsa tun da ga maganar da mahaifiyarsa ta gaya masa. Kuma ya saka wa zuciyarsa a duniya mutum baya taɓa auren matar da ba tashi ba, haka mace ba za ta taɓa auren mijin da Allah bai ƙaddara mijinta ba ne.

Maganar mayar da auren Raihan gabaɗaya sati uku aka saka domin Al'amin ya ce a shirye yake babu abin da ya rage masa, Raihan ta so a ɗaga amma Daddy ya ce su a junansu Manya sun gama magana don haka babu buƙatar sake ɗagawa. Sai a lokacin Al'amin ya sanar da Sumayya maganar mayar da aurensa da Raihan, a lokacin ji ta yi kamar ta yi hauka saboda tashin hankali. Amma har ta gaba surutanta Al'amin bai tanka mata ba, ga shi ya matse mata komai hatta fita sai ta shafe wata guda bata fita ko ina ba. Daga ƙarshe ma tuni ta watsar da huɗubar asire-asire da Mahaifiyarta take ɗora ta akai, wanda ta yi a baya ma ta riƙa neman yafiyar Ubangiji domin Al'amin ba ƙaramar nasiha ya yi mata akan haka ba. Shirye-shirye sun yi nisa daga ɓangarori guda biyun, Mommy da Mama Hafsa suka dage sosai wurin gyaran Raihan. Al'amin har tambayar Raihan ya yi ko akwai wani abu da take buƙata ta ce masa babu, saboda wannan ma ta ce babu abin da za ta yi don har aka ɗaura aure gani take zamanta kamar ba me daɗe wa a gidansa ba ne, tun da a baya ma haka duka aurenta ya kasance. A wannan karonma Daddy da kansa ya ɗauki Raihan ya kaita ɗakin mijinta don dama ba wani taron mutane da yawa suka yi ba, sai ƴan uwa na jiki da abokan arziƙi. Sai dai mutane da dama na tofa albarkacin bakinsu akan auren nata ba wani ƙarko zai yi ba saboda abubuwan da suka faru da ita a baya.
Chapter 107 · 0% Book details