Sashe 37
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗan jim Mahaifiyar Huzaifa ta yi ganin haka ya sa Malam Usman ya ce, "Idan baki da abin faɗa ki bani wuri na kammala abin da nake kai." Mahaifiyar Huzaifa ta numfasa sannan ta ce, "Malam ban jinkirta don gaza abin faɗa ba sai dai na rasa da bakin da zan yi maka magana, Ɗa ne ka haife shi baka haifi halinsa ba. Huzaifa tun yana ƙaraminsa baya ji ko kaɗan, ni mahaifiyarsa amma duk abin da zan gaya masa baya amfani da shi hasalima tuni ya yi hannun riga da mahallina, Malam ya gujewa addinina ya kama addinin kafirci wanda a kullin idan na tuna makomar kafiri na tuna addinin da Huzaifa yake bi zuciyata takanyi ƙuna, mahaifinsa ya cutar da ni ya ha'ince ni, domin shi ne silar duk abin da Huzaifa yake shukawa. Tabbas Huzaifa ya cutar musu da yarinya tun da jin kunnena na ji yana ambatar sama da shekara goma sha a jikinta, don Allah Malam ka yi masa afuwa saboda darajata, kada ka hallaka shi wallahi duk cikin ƴaƴana babu wanda Allah ya jarabce ni da tsananin ƙaunarsa sama da shi..." Tun bata rufe baki ba Malam ya katseta da cewar, "Akan soyayyar ɗanki sai na ƙyale shi ya dakusar da rayuwar yarinyar ƙarama, kina ganin adalci kenan." Murya na rawa Mahaifiyar Huzaifa ta ce, "Allah ya gafarta Malam ba manufata kenan ba, ina nufin ka jinkirta min zuwa wani lokaci zan tattauna da shi zan nemi ya fita daga jikinta amma don girman Allah karka ƙone shi." Shiru ne ya biyo baya Malam na shirin yin magana ya riski muryar Huzaifa yana faɗin, "Ba sai kin nemi wata alfarma a wurinsa ba, har kike zuwa kike kwaye min baya a gaban mutane. Sai me don kin gaya musu ni arne ne meye a ciki? Ni arne ne kuma mahaifina ma haka sannan ina alfari da kasancewata haka, amma ba ke ba kowa za a tara ba zan taɓa fita daga jikinta ba." A zafafe Malam Usman ya ce, "Kin ji abin da yake faɗa Malama Fatima ki ba ni wuri na babbake shi da ayar Allah." Mahaifiyar Huzaifa ta fashe da kuka sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Malam ka yi mini wannan alfarmar karka dubi baƙaƙen maganganun da yake faɗa, dukda dai na san Huzaifa ba lallai ya ji maganata ba domin nima rashin bibiya ga iyaye ne ya ɗora ni a wannan turbar. Tun Muna saurayi da budurwa ni da Mahaifinsa iyayena suka nuna basason alaƙata da Mahaifinsa Ibrahim, sakamakon sun ga take-taken tarbiyyarsa bata masu kirki bace duk da yana ƙoƙarin kwatantawa a zahiri amma a baɗini ba haka yake ba, amma zaƙin soyayya ya rufe min ido haka na watsawa iyayena ƙasa a ido har sai da aka aura min shi amma ba tare da yarjewar mahaifana ba. Ban taɓa sanin ƙasurgumin arne ba ne sai da zamanmu ya yi nisa da shi, mafi yawa daga cikin ɗabi'u da halaye bashi da su masu kyau. Ban taɓa sani ba ashe bakinsu ɗaya da wani hatsabibin aljani MARWAN, Wannan aljanin ko a cikin jinsinmu suna shakku da shayinsa saboda hatsabibancinsa. Sannu a hankali muka fara haihuwa sai muka samu yara uku Huzaifa ne babba, Hafsa ta biyu sai ƴar autata Nabila. Huzaifa tun yana ƙarami shi ne mai ɗauke da siffar mahaifinsu har halayya wannan dalilin ya sa tun yana ƙarami mahaifinsa ya tabbatar mini da tabbas Huzaifa tun da namiji ne addininsa zai bi. A lokacin hankalina ba ƙaramin tashi ya yi amma ganin bani da kowa sai Allah sai shi ya sa dole na amince da buƙatarsa, saboda iyayena suna aura min shi suka zame hannuwansu daga kaina. Haka na ci gaba da mummunar rayuwa a tare da shi, ban taɓa shiga tashin hankali ba sai lokacin da san waye mahaifin mijina wato kakan Huzaifa. A ranar da muka kai masa ziyara ina ɗauke da ciki amma yana tozali da ni nan take ya ce zai yi sihiri da abin ciki sakamakon jinin da wani bokan bil'adam ya zubar masa a kan wani babban aiki da zai yi wa ɗan siyasa. Amma babban abin da ya fi ɗaga min hankali gani yadda Ibrahim ya bashi goyon baya ɗari bisa ɗari, tun basu gama magana ba nan take na ji naƙuda ta kamani amma daga lokacin ban sake sanin wurin da kaina yake ba, sai farfaɗowa na yi na ganni a makwancina. Sannu a hankali na shafa cikina sai dai wayam na ji babu komai amma tsoro, firgici da tashin hankali suka hana ni furta ko da kalma ɗaya ne akan ɗan cikina. Tun daga lokacin duk cikin da zan samu baya zuwa ko'ina sai ya lalace, haka na ci gaba da rayuwar ƙunci har Ibrahim ya fara bijiro min akan dole na yanke alaƙa da addinin musulunci, a nan ne ni kuma na bijire masa muna tsaka da wannan turka-turkar Mahaifana suka rasu. Wannan lamarin ya sake ɗugunzuma mini hankali domin a wannan lokacin ne nake da niyyar zuwa neman yafiyar Mahaifana, amma kash sai rai ya yi halinsa. Haka muka ci gaba da cuɗawa da shi daga ƙarshe har muka rabu domin alwashi na ci akan ba zan taɓa barin addinina ba, da farko ya so ɗauke mini yara gabaɗaya amma na jajirce akan na bar masa Huzaifa domin tun yana ƙaramin ba ya jin maganata sai ta mahaifinsa, ƴan uwansa mata sun fi ƙaunata da tausaya min. Haka na rungumi ƴaƴana na ci gaba da basu tarbiyya, mahaifinsu shi da Huzaifa suka watsar da lamurammu ko waiwaiyarmu basa yi. Sai ni ce nake kaiwa Huzaifa ziyara idan kewa da begensa sun dame ni. Na san duk abin da ya faru da ni ta silar rashin biyayyar iyaye ne kuma na yi nadama har gobe ban daina neman gafara wurin ubangiji akan laifin da na yi wa iyayena ba. Amma duk wasu miyagun ɗabi'u da Huzaifa yake aikawa da sa hannun Mahaifinsa, shi ya gurɓata shi da miyagun ɗabi'unsa. Amma don Allah Malam ka ba ni dama domin na na yi tattaunarwar sirri da shi ko zai fahimci abin da nake nufi ya haƙura da yarinyar nan." Ilahirin jikin mutanen ɗakin ba ƙaramin sanyi ya yi, Mommy tuni ƙwalla ta ciko idonta Daddy jikinsa ya yi sanyi tausayin Mahaifiyar Huzaifa ya kama shi. Hatta shi kansa Malam Usman sai da ya ji wani iri a jikinsa amma hakan bai sa zai sararawa Huzufa ba. Ya kalli Raihan da ke zaune cikin yanayin tausayi sakamakon Mahaifiyar Huzaifa da ke kanta ya ce:
"Yaron da tun yana ƙarami bai ji maganarki ba bana jin yanzu zai tasirantu da abin da za ki faɗa masa, ki sani Huzaifa yana da kunnen ƙashi ba baki na yi miki amma babu yadda za a yi ya ji maganarki tun da bai ɗauke ki da muhimmanci ba, ya kamata ki cire ranki da kika ƙwallafa akansa domin ba shi kaɗai gare ki ba. Ki nunawa masu nuna miki kulawa domin sune za ki amfana ba wannan ba, Huzaifa yana ɗaya daga cikin JINNUL-ASHIQ kuma ba a wanyewa lafiya da su. Maganar iyayenki kuma kin matuƙar tafka kuskure sai dai kamar yadda kika faɗa ko ci gaba da yin addu'a komai ya yi tsanani maganinsa Allah, amma ki bar ɗauka ɗanki zai fita daga jikin yarinyar nan ta daɗin rai." Mahaifiyar Huzaifa na jin haka ta rushe da kuka, mommy ta sauke ajiyar zuciya don duk wata uwa sai ta fahimci abin da Mahaifiyar Huzaifa take ji. Tana tsaka da kuka ta kalli Malam Usman ta ce, "Na fahimci abin da kake nufi malama, shi kenan na gode matuƙa da shwararka a gare ni. Haka Huzaifa ya ga ya fiye masa don haka duk abin da ya faru da shi don kansa, ina mata fatan samun lafiya mai amfani na barku lafiya." Malam Usman na yin sallama ya yi bismillah ya ci gaba da yi wa Raihan Ruƙiyya, Huzaifa shiru ya yi don ya gama zuciya da abin da Mahaifiyarsa ta gama zayyanewa Malam Usman, sai da ya ji wuya ta yi wuya sannan ya gudu daga jikinta. Yaraf can gefe Raihan ta faɗi jiki a mace kamar mara numfashi, ban da ajiyar zuciya babu abin da take yi. A galabaice ta ɗago tana kallon mutanen ɗakin da yanayin mamaki, Malam Usman ya ƙarasa wurin Daddy ya ce, "Zo mu je falo ina son magana da kai." Daddy na jin haka ya bi bayan Malam, suna zuwa falo Malam Usman ya ci gaba da cewa:
"Huzaifa ya gudu daga jikinta amma fa ba tafiya ya yi gabaɗaya ba, mafi yawanci dama haka suke yi idan azaba ta ishe su. Ya kuke gani maganar gaskiya wannan aljanin yana da matuƙar hatsari domin a kowanne lokaci zai iya dawowa kuma a fusace yake komai zai iya faruwa." Da sauri Daddy ya zaro ido yana faɗin, "Malam babu wata mafita?" Yadda Daddy yake magana ne zai tabbatar maka da ya ji jiki iya jiki. Malam Usman ya yi murmushi ya ce, "Akwai mafita, mafitar kuwa ita ce muna da gadaje a ɗakuna da muke kwantar da masu wannan larura idan kuka ganin za a bata gado babu damuwa idan kuma a barta a nan ana zuwa dubata shi kenan..." Tun Malam bai gama magana ba Daddy ya yi karaf ya ce, "A tafi da ita salamun ƙaulan Malam don matuƙar Aljanin nan yana jikim yarinyar nan, wallahi za a wayi gari ta yi daga-daga da namanmu ta cinye." A wannan karan Malam Usman murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Alhaji kuma kuna tsoronsu ne?" Daddy ya dubi hagu da dama sannan ya ce, "Allah ya gafarta malam wane mutum baka ga jikina ba." Nan Malam Usman ya ci gaba da gayawa Daddy irin abubuwan da za su yi wa Raihan idan aka kaita wurinsu.