← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 110

Sashe 76

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar wacce aka watsa wa ruwan zafi haka Raihan ta ji kalaman Al'amin a cikin zuciyarta, ƙwallah ce ta ciko idonta zuciyarta na tururi. Tana cikin wannan yanayin riski muryar Al'amin yana faɗin, "Take care Hayaty" Sai da ya saka wayar a aljihunsa sannan ya kalli Raihan ya furta, "Wa'alaikis salam." Murmushin yaƙe Raihan ta yi ta ce, "Abba fa?" Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Daddy bai shigo ba sai an jima." Raihan duk ji ta yi zuciyarta babu daɗi saboda yadda Al'amin ya tarbe ta tamkar bai taɓa saninta ba, duk da sun jima ba su haɗu ba amma a ganinta ba zai ce bai gane ta. Tana nan tsaye Jamila ɗaya daga cikin ma'aikanta Malam ta ƙaraso ganin Raihan ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Raihan yau ke ce da kanki." Raihan ta sakar mata murmushi sannan ta ce, "Wallahi na zo karɓar turare wurin Abba ashe baya nan." Kasancewar ma'aikanta wurin duka sun san Raihan ya sa Jamila ta furta, "Ai kuwa bai ƙaraso ba sai zuwa anjima bari na baki kujera ko za ki shigo ciki?" Murmushi Raihan ta yi ta ce, "A'a Aunty Jamila nan ma ya isa." Kujera Jamila ta kawo wa Raihan ta zauna, sai da suka shafe wasu mintuna a zaune ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ya jiki?" Sai da ta kalli hagu da dama ta juya bayanta don neman da wanda yake maganar amma bata ga kowa, saboda a ƙalla sun shafe kusan minti goma sha biyar ba tare da ya furta mata komai ba, kuma a yananyin yadda ya yi maganar sai ka rantse ba da ita yake ba. Murya a sanyaye Raihan ta furta, "Da sauƙi na gode." Bai tanka mata ba kuma bai sake ɗago wa ya kalleta ba, sai dai tun zaman Raihan gabanta yake faɗuwa har ta gagara saita kanta ban da kallonsa babu abin da take yi tana jin zuciyarta na yi mata zillo a kansa. Babban abin da ya fi ɓata mata rai jin yadda yake gaya wa wata macen kalamai masu daɗi, saɓanin ita da kallon arziƙi bata samu a wurinsa ba. Tana cikin wannan nazarin ta riski motar Daddy ta ƙaraso harabar wurin, miƙe wa ta ga Al'amin ya yi ya ƙarasa wurin Motar Malam sannan ya karɓo jakar hannunsa, tun daga wurin motarsa ya hango Raihan a zaune tana ganin sun nufo wurinta ta miƙe tana yi wa Malam murmushi, yana ƙaraso wa ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin, "Ƴar gidan Abba ba dai tun ɗazu kike nan a zaune ba." Sai da ta russuna har ƙasa ta gaida Malam sannan ta amsa masa, "Eh to zan kai minti Arba'in zuwa hamsin Abba." Kallon Al'amin ya yi ya ce , "Amma dai ka fiye sakarci Aminu a madadin ka tambayeta maganin da ta zo karɓa amma sai kawai ka barta a zaune, da ban ƙaraso da wuri ba fa?" Al'amin ya sosa kai sannan ya ce, "Daddy ai bata ce min magani ta zo karɓa ba na ji dai tana gayawa Jamila." Takaici ne ya kama Malam don haka ya yi tsaki yana faɗin, "Allah ya kyauta Raihan mu je ciki kin ji." Ba musu Raihan ta bi bayan Malam suka shiga ciki, wayar Malam ta fara ringing sai da ta zauna sannan ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa aka yi; Raihan ta ji Malam ya ci gaba da cewa, "Insha Allah a gobe ne Yaya da kimanin ƙarfe biyun rana, a'a gidansu yarinyar a unguwar Karkasara yake. Ai idan mun je bai fi a tsayar da ranar auren nasu wata huɗu zuwa biyar ba, sai dai gobe insha Allah ma ƙarasa maganar." Gaban Raihan ne ya ci gaba da lugude jikinta har rawa yake don ita kanta ba ta san abin da yake damunta ba. Ji take kamar ta tambayi Malam auren wa za a saka amma ko kaɗan ba za ta iya ba, yawun bakinta ne ya yi mata ɗaci ga wani irin sarawa da kanta yake yi. Ba ta yi aune ba ta riski muryar Malam na yi mata magana, "Ƴar gidan Abba me kika zo karɓa maganin sha ne ko turare, sai da ta mayar da ƙwallar idonta kai a ƙasa ta furta, "Abba turare da garin habbatussaauda ne babu." A jikin wani ƙaramin kati ya rubuta mata da yake Raihan ba baƙuwa ba ce a wurinsa ya sa ya rubuta suna da shekarunta ba tare da ya tambayeta ba, miƙa mata ya yi ta yi masa godiya har ta miƙe ya kira sunanta. Cak ta tsaya wuri ɗaya jiki ba ƙwari ta juya tare da amsawa, kujera ya nuna masa ya ce: "Zauna!" Ba musu Raihan ta zauna tana sake sauke kanta ƙasa don bata son ya fahimci halin da take ciki, sunanta ya sake kira sannan ya ci gaba da cewa, "Me yake damunki? Ko akwai wata matsalar ne Raihan?" Kamar mai jira sai kawai Raihan ta fashe da kuka, shiru ya yi sai da ta yi mai isarta sannan Malam ya miƙa mata wani hankici ta karɓa ta goge hawayenta. Ido ya zuba mata yana sake karantar yanayinta ya ce, "Me yake damunki?" Raihan ta sake goge hawayen da ya zubo mata sannan ta furta, "Babu abin da yake damuna Abba, haka kawai nake jin ɓacin rai sai na yi kuka nake jin daɗi." Jinjina kai Malam ya yi ya ce, "Yaushe kika fara jin haka?" Shiru Raihan ta yi kamar mai nazari ta ce, "Na ɗan kwana biyu." Karɓar katin hannun Raihan ya yi da kansa ya wuce ya haɗo wa Raihan magunguna masu yawa ya dawo ciki ya bata, kowanne sai da ya yi mata bayaninsa dalla-dalla. Godiya Raihan ta yi har ta sake miƙe wa ta zauna ta ce, "Daddy babu teller..." Katse ta ya yi da cewar, "Gidanku kin ji Raihan, fice ki bani wuri kar na karye ƙafarki." Dariya Raihan ta yi sosai ta fice daga office ɗin don babu yadda za a yi ka haɗu da Malam baka yi dariya ba saboda shi mutum ne mai barkwanci. Tana fito wa ta ji shi ma ya fito yana ƙwala wa Al'amin kira, ƙarasowa ya yi wurinsu Raihan. Malam ya dubi Raihan ya ce, "Za ka raka ta gida duk da a motarta ta zo, amma ban lamunce ta tafi ita kaɗai va saboda bata jin daɗi. Idan za ka dawo sai ka hau Napep." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Daddy da wuce wa gida zan yi fa." Malam ya wuce ƙofar Office ɗin sa sannan ya ce, "Ni dai na ce ka raka ta gida. Dududu minti nawa ne ka kaita gida ka dawo." Al'amin wuce wa ya yi wurin motar ba tare da ya furta komai ba, a sanyaye Raihan ta ƙarasa wurinsa. Hannu ya miƙa mata sai kawai ta tsaya tana kallonsa don bata fahimci abin da yake nufi ba. Ganin ta yi shiru ya sake harzuƙa shi ya dube ta ya ce, "Ko ba da key kika tuƙo motar ba?" A duburburce Raihan ta fara duba jakarta hannu na rawa ta miƙa masa key, da sauri ya buɗe motar ya shiga. Jikin Raihan na rawa ta buɗe motar ita ma ta shiga, da gudun gaske ya figi motar suka fice daga harabar wurin. Gaban Raihan ban da faɗu wa babu abin da yake yi, sai dai duk abin da Al'amin yake yi ko kaɗan bata ji haushinsa ba hasalima sai ta riƙa jin haushin kanta don gani take kamar ita ta yi abin da ya harzuƙa shi. Suna hawa kan titi ta ji ya furta, "Ta ina za mu bi?" A rikice Raihan ta riƙa kwatanta masa saboda muryarsa ba ƙaramin rikita masa lissafi ba, suna zuwa ƙofar gidansu Raihan ya faka motar ya fito ba tare da ya furta mota komai ba. A tunanin Raihan ko fita yin wani abu zai yi, jin shirun ya yi yawa ya sa Raihan fitowa daga motar sai dai tana fito wa ta hango Al'amin a can ƙarshen layinsu har ya kusa zuwa titi. Wani irin gwauron kuka ne ya zo mata ta kafa kanta a jikin motarta tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kabiru na daga cikin ɗakinsa da farko ya ji tsayiwar mota a tunaninsa Raihan ce ko Daddy, amma jin shirun ya yi ya wa ya sa ya yi tsammanin ko wuce wa aka zo yi. Jin kuka sama-sama ya sa ya tako a hankali ya zare sakatar gidan, turus ya yi yana kallon Raihan sannan ya fito yana waige-waige jiki na rawa ya furta, "Waye ya taɓa ki?" Sai a lokacin Raihah ta ɗago fuskarta har ta yi jawur saboda kuka, ganin yanayin da Raihan take ciki ya sake ɗaga hankalin Kabiru. Jin irin tambayar da ya yi mata ya sa ta sake rushe wa da kuka, takawa Kabiru ya fara yi yana dube-dube amma unguwar shiru take ko tsuntsaye babu. Dawo wa ya yi gabanta a fusace ya buga mata tsawa yana faɗin, "Na ce miki waye? Wanene ya taɓa ki." Zaro ido Raihan ta yi don tun da take da Kabiru abin da bai taɓa yi ba kenan, ko magana mai ƙarfi baya yi mata balle ya buga mata tsawa. Tsoro ne ya kamata don haka lokaci ɗaya ta haɗiye kukanta, ajiyar zuciya Kabiru ya sauke don ya lura da halin da take ciki. Tausasa murya ya yi ya buɗe mata murfin motar ya ce, "Shiga!" Ba musu Raihan ta shiga ya rufe motar, ya ƙarasa ya buɗe mata gate ɗin gidan ta shige da motarta. Yana ganin ta shiga ya rufe ƙofar ya ƙarasa bakin motarta, Raihan na fito wa daga motar da sauri za ta wuce Kabiru ya sha gabanta fuska a haɗe ya sake tambayarta, "Waye ya saka ki kuka?" Wani hawayen ne ya ziraro mata sai dai bata jin za ta iya gaya wa Kabiru saboda ta lura ko hirar mijinta na baya son ta riƙa yi masa. Cikin muryar kuka ta ce, "Babu komai kaina ne yake ciwo." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Ƙarya ba halinki ba ne tabbas akwai wani abu da yake damunki daga ina kike?" Harara ta watsa masa ita ma ta haɗe fuska ta ce, "Fillo wai me ya sa ka raina ni ne?" Bai tanka mata komai ba ya kafe ta da ido, ganin haka ya sa Raihan ta shammace shi ta yi cikin gida a guje. Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don har sai da ya murmusa sannan ya wuce ɗakinsa, amma kukanta ya tsaya masa a rai saboda ya tabbata ruwa baya tsami banza.
Chapter 76 · 0% Book details