← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 110

Sashe 85

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tana shiga kitchen ɗinta babu abin da babu don haka kai tsaye ruwan tea ta fara dafa musu ta zuba a flask, sannan ta fere dankali ta soya musu sai kuma ta soya ƙwai daban don ta so soya kayan miya ko miyar jajjage ta yi musu, bayan ta haɗa komai tunani ta fara yi a wurin da za ta ajiye musu abinci. Nata ta haɗa daban sannan ta haɗa musu na su a tire ta saka komai ta ɗauka ta nufi ɗakin Sumayya. Da sallama ta shiga a lokacin tuni Sumayya ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando, kanta a ƙasa ta shiga da shi ta jiye musu sannan ta koma ta ɗauki nata ta wuce Main falonsu ta zauna tana karyawa. Ƙarar turo ƙafa ta ji tana kai idonta ta ga Al'amin ɗauke da tiren ya fito da shi ya kawo falon da take zaune, da ido ta bishi har ya koma ya riƙo hannun Sumayya suka dawo cikin falon. Tana zaune ta ci gaba da cin abincinta kamar ma bata gansu ba haka ta ɗauke kanta sai dai gabaɗaya ta daina jin daɗin abincin, turawa kawai take yi don kar su fahimci halin da take ciki. Akan idonta suka riƙa ciyar da juna cikin shauƙin so da ƙauna, suna gamawa Al'amin ya kwashe kayan ya kai su kitchen. Dawo wa ya yi ya zauna Sumayya ta kwantar da kanta a jikinsa cikin shagwaɓa ta furta, "Darling don Allah ka roƙi alfarmar Aunty Raihan ta taimaka t gyara mana ɗaki wallahi zan ji kunya idan baƙin gidanmu suka zo, ka ga a gabanka Mami ta kira ni wai baƙi za su zo ganin ɗaki." Jim Al'amin ya yi yana ganin kamar saka Raihan gyran ɗakin baccinsu bai dace ba, kamar ta san abin da yake nazari ta tashi zaune tana marairaice murya ta ce, "Wallahi ko yatsana da ƙyar nake iya ɗagawa, ka ga ita ma lokacin da za ka koma ɗakinta duk abin da ya dace na gida ai ni zan yi. Amma ka yi haƙuri idan baka so haka ba." Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin kujera. Miƙe wa ya yi cike da jin daɗi don gani yake kamar Sumayya ta sauko don su haɗa kansu da Raihan ne ya nufi ɗakin Raihan yana faɗin, "Menene amfanin zaman tare My baby? Bari na yi mata magana." Tura ƙofar ɗakin ya yi a lokacij Raihan na waya da Inno don ta yi kewarsu, tsaye ya yi yana kallonta babu laifi tana da kyau daidai gwargwado gata da gashi irin na fulani har baya. Yana son mace mai tsayin gashi duk da Raihan ba fara ba ce kuma bata da wani jiki amma bata da muni a fuska, tana gama waya ta juyo tana kallonsa. Ɗauke kai ya yi kamar bai ganta ba sannan ya ce, "Am dama cewa na yi ki ɗan gyarawa Sumayya ɗaki ba za ta iya ba." Ɓata fuska ta yi har bata san lokacin da ra furta, "Gyaran ɗaki?" Gyaɗa mata kai ya yi ya ce, "Eh saboda baƙi za su zo ita kuma kin ga yadda jikin nata yake." Raihan bata tanka masa ba zuciyarta na suya ta wuce ta nufi ɗakin Sumayya don ta manta ko ɗankwalinta bata saka balle hijabi. Daga iya sai doguwar rigar leshi, kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Sumayya na ganin Raihan sai da gabanta ya faɗi, saboda koda ta san Raihan bata fita kyau ba amma babu wanda zai kalli Raihan bai ce ta yi masa kyau ba. Kai tsaye ɗakin ta shiga ta fara kaɗe gadon cikin takaici, kayan Raihan duk a warwatse har da ƙananan kayanta na ciki. Sai da ta kwashe su da cusa mata a drower sannan ta gyara gadon ta mayar da komai yadda yake ta wuce ɗakinta. Hankalin Sumayya bai kwanta ba sai da ta ga Raihan ta shiga ɗaki, amma abin da ya ɓata ranta yadda ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa kan Raihan. Idan ka kalli Sumayya tashin farko za ka fahimci ta fi Raihan kyau sai dai Raihan ta nuna mata dirin jiki da tsayin gashi domin Sumayya fara ce kyakkyawa, ita ma doguwa ce amma tafi faɗi daga sama. Shigar Raihan ɗaki babu wuya suka ji bugun gida, ta window Raihan take kallon hanya Al'amin na buɗe wa ta hango su Mama Hafsa da sauran baƙin da ba su gano ɗaki ba. Mamaki ne ya kama ta ganin yadda Al'amin yake gaida su cikin mutumci fa girmamawa yana sunne kai ƙasa, suna shigo wa da sauri ta ɗane Mama Hafsa tana murna. Ita ma rungumeta ta yi cikin farinciki don ta ji daɗin ganin Ƴar ƴar'uwarta cikin ƙoshin lafiya, sai a lokacin ta baje musu kajin da Al'amin ya kawo mata, kaɗan suka yi suka saka mata sauran a firji. Babu ƙofa ɗaya da Raihan ta buɗe musu da take nuna tana cikin damuwa don haka sai santin ɗakinta suke yi, sai da suka leƙa sashen Sumayya suka gaisa ta amsa musu cikin mutumci sai yabon sauƙin kanta suke Raihan ban da murmushi babu abin da take yi, daga ƙarshe suka koma ɗakin Raihan suka yi mata nasiha mai ratsa jiki, akan ladabi da biyayya sai juriya da haƙuri. Sun yi mata nasiha sosai akan yadda za ta kula da mijinta ta ɓangaren kissa da tarairaya Mama Hafsa na gaya mata har kunya take ji, ba su wani daɗe a gidan ba suka yi mata sallama suka tafi. Lokacin da za su tafi har da ƙwallarta ta raka su bakin gate tana ɗaga musu hannu, ɗakinta ta koma ta ɗauki waya ta kira wayar mommy. Sun jima suna hira da mommy duk a game da baƙi ne da sauran ƴan biki, bayan sun gama ta kira Daddy cikin farinciki ya amsa mata bayan sun gaisa suka taɓa hira sannan suka yi sallama.
Chapter 85 · 0% Book details