← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 110

Sashe 90

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Tun bayan tafiyar Mama Hafsa Raihan take saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa lamarin dangane da shawarwarin da ta bata, gani take kamar ba za ta iya wasu abubuwan ba don sai ta ga kamar kunyar Al'amin za ta ji. Amma da wata zuciyar ta sake tuno mata da irin shawarwarin da Mama Hafsa ta bata sai ta ayyana za ta fara gwada wasu ko babu komai ta fahimci yanayin yadda zai karɓi abin. Sai da yamma ta ƙarato ta fesa wanka ta ɗauko wani ƙananan kaya riga da wando, farar riga ce kar da jan wando sai kuma wata jar hula da ta saka mai baƙaƙen duwatsu. Har ta saka ta sai kuma ta cire ta dubo wani ƙaramin jan mayafinta saboda tunowa ta yi da yadda gashinta yake ɗauke masa hankali. Ɗaura shi ta yi ta bazo gashin ta baya sannan ta fara gwada irin tafiyar da za ta yi idan Al'amin ya dawo. Tuwon shinkafa miyar agushi ta dafa musu sai lemon abarba da ta yi mai daɗi ta saka shi a firji, tun da ta shirya bata fita waje ba don ta ci alwashin Al'amin ne zai fara ganin wankan da ta yi ba Sumayya ba, saboda ta fahimci wani abun tana kwakwaiyarta. Tana zaune a ɗaki ta ji muryar Al'amin da alama dawowarsa kenan, don haka ta tura ƙofar a hankali wani irin ƙamshinta ya doki hancinsa, a hankali ya ɗago yana kallon wurinta ta yi kamar bata gan shi ba saɓanin lokacin baya da idan ta gan shi jikinta na rawa take zuwa tana yi masa sannu da zuwa. Kai tsaye firji ta wuce ta ɗauko lemon da ta yi sai da ta zo gabansa ta tsiyaya ta miƙa masa sannan ta furta, "Barka da dawowa." Tun da ta shiga falon yake bin ta kallo don haka bai san lokacin da ta yi masa barka da zuwa ba sai da ta sake maimaitawa, a kunyace Al'amin ya sosa kai haɗe da faɗin, "Yauwa barka." Kan kujera Raihan ta koma ta zauna ta ɗauki wayarta tana dannawa ɗaiɗai kamar ba ta san yana falon ba. Cikin takun isa Sumayya ta turo ƙofa tana tafe ƙamshi na biye da ita, doguwar rigar shadda ta saka ta ɗaura ɗankwalinta ita ma ba ƙaramin kyau ta yi ba. Tana ganin Raihan ta haɗe girar sama da ƙada, da gayya ta ƙarasa wurin Al'amin ta zaune haɗe da cewar, "Barka da zuwa Husbee." Murmushi ya yi ya amsa mata da cewar, "Barka dai Wifey ya gida." Wani ɗaci Raihan ta ji a ranta amma sai ta ci gaba da taunar cingam ɗinta tana karkaɗa ƙafa tana danna waya, harara Sumayya ta wurga mata sannan ta furta, "Hubby an kawo maka ruwan wankin hannu da abinci kuwa?" Sumayya ta faɗi haka ne don ta san Al'amin zai sake aiken Raihan kuma ta san ba zai yi mata daɗi ba. Tana tsaka da tunanin ta riski muryar Al'amin yana faɗin, "Ke! Tashi ki miƙo min abinci." Shiru Raihan ta yi tana kallon waya, yana rufe baki ta kishingiɗa ta ci gaba da abin da take yi. Kallonta ya sake ya furta, "Ke Raihan ba magana nake yi miki ba." Murmushi Raihan ta sakar masa sannan ta furta, "Ban yi tsammanin da ni kake ba na ji kana kiran matarka da ke Daz why ban kawo da ni kake ba." Daga Al'amin har Sumayya ido suka bi Raihan da shi don tun da ta zo gidan wannan ce doguwar maganar da ta yi. Cikin wani irin taku ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗebo ruwa ta dawo ta ajiye ta sake komawa ta ɗaukon abincinsa sannan ta koma kwanta, sannu a hankali Sumayya ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa Raihan. Cike da ɓacin rai ta dubi Al'amin tana cewa, "Hubby mu wuce ɗaki mu ci a can." Sam ba shi da sha'awar tafiya don ko babu komai Raihan ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, musamman gashinta da yake ta sheƙi da ya zubo har baya. Abincin hannunsa ya cinye sannan ya furta, "Am comportable a nan, bayan na gama cin abinci ma ina da aikin da zan yi." Ganin babu wasa a fuskar Al'amin ya sa Sumayya ta yi shiru sai dai gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi saboda babban tashin hankalinta kar Al'amin ya faɗa ƙaunar Raihan don kallon da yake yi mata mai ɗauke da ma'anoni ne. Wurgawa Raihan mugun kallo ta fara yi cike da jin haushi ta tashi fuuuu ta shige ɗaki. Zuciyar Raihan fes don har sai da ta murmusa ta ci gaba da danna wayarta, a lokacin Al'amin ya samu damar more wa Raihan kallo haka kawai ya ji tana birge shi uwa-uba ga girkin da ta dafa ba ƙarmin daɗi ya yi masa ba, kasancewar ba zai tantance girkin Sumayya ba don tun da suka yi aure bai fi sau uku ta yi girki ba, yau ta ce nan na ciwo gobe ta ce can. Don haka Raihan ta karɓi ragamar gyaran gidan gabaɗaya, sai dai koyaushe idan ta tuna bata da wata fada a wurin mijinsu abin yana yi mata ciwo. Bayan Al'amin ya gama cin abinci Raihan ce ta kwashe kayan gabaɗaya tana yin aikin idon Al'amin na kanta, tana sane da shi don haka ta riƙa taku ɗaiɗai har ta gama kwashewa gabaɗaya. Tana gamawa ta wuce ɗakinta bakinta ɗauke da dariya don ta lura da yadda yake shan magani a duk lokacin da ta ɗago suka haɗa ido da shi, kwanciya ta yi tana murmushin farinciki don ko babu komai ta san yau rana ɗaya ya yi mata kallon ƴa mace saɓanin lokacin baya da baya ɗaukanta a komai. Bai gaji da kallonta ba don haka kai tsaye ya nufi ɗakin Raihan sai da ya je bakin ƙofa sai kuma ya ja guntun tsaki don bai san abin da zai ce ya zo yi ɗakin ba. Ɗakin Sumayya ya shiga don ya lura sarai haushinsa ta ji din haka ta wuce ɗakinta a fusace, yana zuwa ya same ta tana ƙwallah nan ya shiga rarrashinta daga ƙarshe ta sauko suka dawo falo. Zaman Raihan da Al'amin haka ya fara ɗaukan sabon salo, don yanzu ta rage rawar jiki akansa sosai dukda a koyaushe tana jin soyayyarsa da kewarsa a zuciyarta. Girki kuwa tuni Sumayya ta karɓi abinta don tuni Mahaifiyarta ta yi mata faɗa akan wannan wautar da ta yi, don haka suke girkin kwana bibbiyyu amma duk ranar Raihan bata da kwana sakamakon duk ranar girkinta tun magriba take kwanciya wani irin bacci mai nauyi ba ita za ta farka ba sai bayan sallar asuba, lamarin wannan bacci nata ba ƙaramin damunta ya yi ba akwai ranar da ta zauna a falo tana jiran dawowar Al'amin ana yin sallar Isha'i bacci ya yi awon gaba da ita ba ita ta farka ba sai da ana kiran sallar asuba. Tun abin bai ɗaga hankalin Raihan ba har ya fara damunta don haka ta dage da nafilfili tana kaiwa Allah kukanta. Sai da ta shafe sati biyu cikin wannan yanayin sannan Allah ya yaye mata, ana cikin haka har ranar girkinta ta zagayo tun ana gobe za ta karɓi girki ta sa Al'amin ya yi mata cefanen dambu, tun bayan azahar ta shiga kitchen ta fara haɗa kayan dambu wurin bayan sallar la'asar ta gama dambun shinkafarta ban da ƙamshi babu abin da yake yi. Tun lokacin da Dambun ya turaro Sumayya ta kasa zaune ta kasa tsaye, yawunta ba ƙaramin tsinkewa ya yi ba amma faɗin rai ya hanata zuwa ɓangaren Raihan. Ganin ta kasa daurewa ya sa ta taka har ɓangarenta fuska ɗauke da murmushi ta ce, "Aunty Raihan na zo cin dambu wallahi Ɗan baba nake ji kamar zai fito." Ras gaban Raihan ya faɗi don saboda a ƴan kwanakin nan ta lura da sauye-sauyen da take gani a tattare da Sumayya, murmushin ta yi mata sannan ta ce, "Dama yanzu nake shirin kai miki don gaskiya karki haifo min Ɗa da rowa, na zo na ji kunya ace uwa ta yi wa Ɗanta rowa ai ba kanta." Sumayya ba haka ta so ba don ta so maganar da ta faɗa ta ɓata wa Raihan rai amma sam bata lura da haka ba." A wani food flask Raihan ta zuba wa Sumayya ta miƙa mata sannan ta fice, jin ƙamshin na bugarta ya sa tun a hanya ta ɓuɗe ta damƙi loma ɗaya ta ci tana lumshe ido. Tun bayan fitar Sumayya jikin Raihan sanyi ya yi, ƙwallah ta ciko mata ido don a yanzu ta yadda da zarginta Sumayya wani cikin gare ta, hawaye ne ya zubo mata da ta kalli yadda ta shirga kwanukan Al'amin ta ƙarewa kanta kallo sannan ta tuno yau kusan watansu huɗu da aure amma babu wani abu da ya taɓa shiga tsakaninta da shi. Jiki a sanyaye ta ƙarasa aikinta ta koma Falo ta zauna tana ɗan danne-danne a wayarta. Har aka yi sallar magriba Al'amin bai dawo ba sai gabannin isha'i ta ji alamun shigowarsa, tana nan zaune ya shigo ƙamshin turarenta ya doki hancinsa har sai da lumshe ido, kallonta ya yi tana sanye da riga da sike na leshi ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Murmushi ta yi masa ta ƙarasa ta karɓi jakarsa, wannan karon ta yi mamaki da har ya mayar mata da martanin murmushi. Al'amin ji yake kamar ta rungume ta saboda yadda ya ga ta yi masa kyau, ita kanta Raihan ta lura da irin kallon da yake yi mata don haka take cikin farinciki haɗe da fatan ta samu babban matsayi a zuciyarsa. Sai da ya yi wanka a ɓangare Sumayya ya sako ƙananan kaya ya fita sallar isha'i ya dawo sannan ya ci abinci, yana cin dambu yana lumshe ido don ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ita kuwa Sumayya a daddafe ta yi sallar Isha'i kasancewar wannan laulayin nata shi ma ba ƙaramin bacci yake saka ta ba. Lura da yanayinta da Al'amin ya yi kama ya sa idan ya dawo ko ranar girkinta ne idan ya ga tana bacci baya tashinta, don haka a wannan lokacin ma Al'amin ya ke ta kallon Raihan yana jin wani baƙon yanayi a tattare da ita. A zuciyarsa ya ƙudurce a ranar sai ya sauke mata nauyinta da yake kansa don ba ƙaramin nadama ya yi ba saboda tuna hukuncin da Ubangiji ya hukunta akansa, tausayi ta bashi da ya tuna tsawon watannin da suka ɗauka ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, har zuciyarsa ta fara ayyana masa da a ce ba mai tsoron Allah ba ce tuni ta nemar wa kanta mafita.
Chapter 90 · 0% Book details