Sashe 100
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Watan Kabiru guda da dawowa gidan Daddy Ibrahim ya dawo jikinsa, yanayinsa da maganganunsa ya sa Maryama ta fahimci haka don haka ta sanarwa da Inna wuro, ita kuma Inna wuro ta sanar da Mommy. Nan take Mommy ta kira Daddy ta gaya masa don tuni ya fita aiki, da yake har lokacin Kabiru bai koma bakin aiki ba. Daddy na kiran Malam ya sa motar office ɗin su ta zo har gida, wasu daga cikin ma'aikatansa suka tafi da shi har office ɗin Malam. Kusan tare suka ƙarasa da Motar Daddy don yana gama waya da Malam shi ma ya ɗauko hanya, a galabaice Ibrahim ya fara magana."Alhamdulillah Malam mun yi nasara, sai dai ba mu samu damar kama Huzaifa ba don tun kafin zuwanmu Kakansa ya sa shi ya tsere. Amma mun kamo Kakansa kuma mun baje tsibirinsa mun hukunta na hukuntawa mun kashe na kashewa, sai tsiraru da suka karɓi kalmar shahada." Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillah." Ibrahim ya ci gaba da cewa, "Yanzu haka muna tare da Kakansa da wata mace wacce ta roƙi alfarmar mu kawota za ta roƙi gafarar Raihan."Malam ya ce, "Ikon Allah muna ji." Murya na rawa Mugaza ta ce, "Ni dai sunana Mugaza amma Raihan da iyayenta sun fi sanina da Intisar..." Nan take Mugaza ta zayyane musu duk wata alaƙarta da Raihan da yaudararta da yi har zuwa lokacin da Huzaifa ya gano sannan ta ɗora da cewa, "Na kai Raihan Ƙungiyar tsafinmu ne don na bayar da jininta saboda mijina na mutuwar sonta ni kuma kishi ya rufe min ido, saboda matan bil'adam sun fi mu kyau da kyawun siffa nesa ba kusa ba. Da na kaita ashe sa'a ce tare da ita kuma da yake da sauran kwananta a gaba sai su Abar bauta suka gano tana da muhimmanci a cikin ƙungiya. Yanzu haka Huzaifa ya kashe mini ƴaƴana duka saboda na gano maɓoyar ɗan da Raihan ta haifa masa na kashe shi, kuma ya kashe su abar bauta ni ma yana ƙoƙarin kashe ni muka ji alamun zuwan baƙin nan, to da yake dama Jabbul-ƙasi ya san da labarin zuwansa kuma ya ba shi ɓoyayyayun sirrika sai ya ɓace daga wurin mu." Gaɓoɓin jikin Daddy ba ƙaramin sanyi suka yi ba, kusan mutuwar zaune ya yi yana mamakin maganganun da Intisar ta faɗa. Jabbul-Ƙasi ne ya fara magana shi ma cikin gadara duk da a wahale yake ya furta, "Jikana ba zai taɓa kamuwa ba a wurinku don haka na bada kaina koma meye ku yi min domin kuwa dama tsufa ya cimmi ni mutuwata ta kusa." Takaici ya saka Malam ya sa aka yi turare Habbatussauda sannan ya fara yi musu ruƙiyya, ganin sun galabaita ya sa Malam ya tambayi ta ko za ta musulunta amma dukkansu suka ƙeƙashe ƙasa suka nuna matuƙar suka karɓi addinin musulunci sun zubda ƙimarsu. Ita kuma Mugaza ta ɗora da faɗin gara ma Malam ya ƙoneta don ta tsani musulunci kuma gara kisan da Malam zai yi mata akan na Huzaifa. Malam bai saurara musu ba ya ci gaba da karatu duk yadda suka kai ga taurin kai sai da suka galabaita suka fara roƙon Malam cikin ɗimuwa. Bai saurara musu ba ya ci gaba da yi har sai da ya ƙone su ƙurmus. Cike da farinciki Malam ya furta, "Alhamdulillahi." Sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Su Daddy ba ƙaramin farinciki suka yi da jin an ƙone su Mugaza don haka suka ci gaba fatan shi ma Huzaifa Allah ya ba su sa'ar kamo shi a ƙone shi kowa ya huta.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
50
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
50