Sashe 17
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hankali a tashe mommy ta nufi sashen Daddy tana ƙwala masa kira. A bakin ƙofa ta ci karo da shi tana ganinsa ta fara nuna masa hanya tana faɗin, "Alhaji Raihan ce..." Maganarta ta maƙale saboda yadda take sauke ajiyar zuciya. A zabure Daddy ya kama kafaɗarta yana jijjigawa yana faɗin, "Me ya samu Raihan ɗin ki faɗa min tana ina?" Hanya ta riƙa nuna masa tana faɗin, "Tana can ta tsintsinka ƙadangare da haƙoranta." Da gudu ya nufi hanyar ɗakin Raihan hankali a tashe. Nan take ragowar mutanen da ke cikin gidan suka yi tsilli-tsilli, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci tana cikin matsanancin tashin hankali.
Daddy kai tsaye ɗakin da Raihan take ciki ya tunkara yana shiga ya same ta a cen gefe ta faɗi da alama bata numfashi. Kallon ɗakin ya fara yi saboda yadda jinin ƙadangaren ya ɓata saman carpet ɗin ɗakin, daga gefen hannunta ya hangi gangar jikin ƙadangaren hannunta ya jiƙe sharkaf da jini. A hankali ya ƙarasa wurin ya mirgino da ita yana ambatar sunanta muryarsa a raunace, shiru ne ya ratso a ɗakin babu abin da yake tashi sai karar AC da saukar numfashin Daddy. Tsugunnawa ya yi a gabanta ya tallafo da kanta zuwa kan cinyarsa, murya na rawa ya furta: "Me yake samunki ne Raiha? Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da ke?" Kuka ne ya ci ƙarfinsa ya kafa kansa a jikinta yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Daga bakin ƙofa Mommy ce ta shiga jiki a sanyaye, ita kanta lamarin Raihan ya fara bata tsoro. Kusan shekara goma sha biyar kenan suna fama da abu ɗaya, babban tashin hankalin da ciwon kullin gaba yake yi baya raguwa. A sanyaye ta zauna a gefen Daddy ta ce, "Daddyn Raihan." Ɗagowa ya yi ya dube ta idonsa na ci gaba da zubda ƙwallah, ita ma hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta sa hannu ta share sannan ta ci gaba da cewa, "Ka daina kuka don yanzu babu buƙatarsa a gurbin halin da muke ciki..." Tun bata rufe baki ba Daddy ya katseta da cewar, "Ido yana zubda hawaye ne ba don gangar jiki da ruhi suna buƙata ba, sai don samun sauƙi ga raɗaɗin ƙunan zuciya. A da na ɗauka rashin haihuwa babban masifa ne a gare ni sai ga shi a yau na wayi gari Allah ya bani gudan jinina ga kuma masifar da tafi min rashin haihuwar..." Da sauri Mommy ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce, "Bai kamata ka riƙa furta irin kalmomin nan ba, domin duk abin da ya samu bawa yana daga Ubangiji shi ya fi mu sanin dalilinsa na yin haka." Mommy ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa, "Ya zama wajibi ciwon yarinyar nan a koma yin da Islamic don wannan yana da alaƙa da shafar aljanu..." A razane ya katse ta yana faɗin, "Kina hauka ne? Na gargaɗe ki da ki daina danganta jinina da jinsin aljanu." Wanna karon mommy ita ma hassala ta yi ta ci gaba da cewa, "Kar ka sake furta kalma ta ƙasƙanci a kaina, don duk taƙamar da kake yi ba kai kaɗai ka haifeta. Raihan ƴata ce idan kai ba za ka nema mata maganin Islamic ba dole ni zan nema mata." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Daddy ko a jikinsa tana fita ya ɗauki waya ya kira likitan da ke duba Raihan, zayyana masa komai ya yi sannan suka yi sallama ya ci gaba da zubawa Raihan ido yana tunane-tunane a zuciyarsa.
Lokacin da Macijiyar ta É“ace daga É—akin Kabiru, daga gefen hagunsa ya fara jin wani irin gurnani irin na riÆ™aƙƙun kumurcin maciji, a hargitse ya sake miÆ™ewa yana kalle-kalle bakinsa na furta Amanarrasulu don a tunaninsa macijin ne zai sake bayyanar masa. Ya jima yana jin wannan gurnanin daga baya ya ji shiru komai ya É—auke daga dodon kunnensa, daga jikin hannun rigarsa wata fata ya ga ta kwakkwaÉ“o irin saÉ“ar fatar maciji wacce yake yi. Da sauri ya É—ago ta cikin tashin hankali don lamari ya fi Æ™arfin tunaninsa, ido ya zurawa gwiwar hannunsa ta wurin da fatar ta faÉ—o ya ga wurin ya sake yin sheÆ™i tamkar bayan maciji. Kwalla ce ya ji ta zubo masa saboda duk wanda ya lura da halin da yake ciki ba zai taÉ“a zama a kusa da shi ba, kallo É—aya za ka yi wa jikinsa ya firgita ka don bambamcinsa da maciji kai, hannu da Æ™afafuwa. A hankali ya Æ™arasa wurin buhun kayansa, nan take ya fara zazzagewa yana birkito kayan da zai saka don ya rufe jikinsa. Sanin kansa ne ko masu aikin gidan suka fahimci halin da yake ciki zamansa a cikin gidan ya Æ™are balle kuma a ce Alhaji ya lura da yadda surar jikinsa ta koma. Sai da ya tura Æ™ofarsa ya rufeta ruf don kar wani ya turo, sannan ya tuÉ“e rigar jikinsa da yake mai gajeren hannu ce. A jikin mudubin ya tsaya yana Æ™arewa jikinsa kallo fatar jikinsa ta koma sak irin ta maciji, wani hawayen ne ya sake gangaro masa ya sa hannu ya share sannan ya É—auko wata tsohuwar rigar shadda mai dogon hannu, ya É—auko wani tsohon mayafinsa da wanda ya gada a wurin mahaifiyarsa ya naÉ—e wuyansa da shi. A jikin bango ya jingina a fili ya fara magana cikin karyewar zuciya, "Allah sarki Baffajo ba don rashin lafiyarka ba, da babu abin da zai hanani barin wannan gidan, don da alama wannan ba wurin zama ba ne." Kabiru ya É—aga hannu sama ya ci gaba da cewa, "Allah ka bawa Baffajo lafiya, da yardar Allah sai na bar gidan nan don na nemawa kaina lafiya." Daga gefensa ya ji an bushe da dariya, yana juyawa ya hangi matashiyar budurwa tana tsaye tsirara babu kaya a jikinta. Hannuwa biyu ta wara masa tana faÉ—in, "Ina da hanyar da zan kawo maka mafita matuÆ™ar za ka bani dama." Kabiru ya kauda kansa gefe yana faÉ—in, "Wa'iyazubillah." Æangaren da ya juya fuskarsa ta sake komawa tana faÉ—in, "Indai akan matsalar abin da ya faru da jikinka ne zan warkar maka da shi matsawar za ka bani haÉ—in kai." Kabiru ya É—ago da kansa yana shirin yi mata magana, karaf idonsu suka haÉ—u wuri É—aya nan take ya ji tsigar jikinsa na tashi. Da Æ™yar ya iya saita kansa sannan ya furta, "Ki taimaka min ki raba ni da wannan fatar macijin, ki gaya min me kike buÆ™ata daga wurina yanzu na aiwatar miki?"
Duk wani shige da fice da su Mommy suke yi akan idon Mama Uwani, lokacin da ta ji labarin abin da ya faru ta shiga tashin hankali don ta san wannan abin da Raihan ta aikata baya daga cikin abubuwan da take saka Raihan tana aikatawa. Fitowa ta yi ta fara kaiwa da kawowa nan take wata dabara ta faɗo mata, sai da ta shige ɗakinta da yake babu kowa a ciki sannan ta ɓace daga ɗakin. A lokacin da ta ɓace Dr Hamza yana gidansa ya gama shiri don zuwa gidansu Raihan, Huzaifa na zuwa da ya ga haka don kar ya kawi masa matsala ya bige shi a kan gado nan take bacci ya yi gaba da Dr Hamza. Cikin siffar Dr Hamza ya kira lambar Daddy bugu ɗaya kawai ya yi ya ɗauka, a gaggauce Daddy ya furta, "Dr ka ƙaraso ne?" Huzaifa da ke ɗauke da surar Dr Hamza ya amsa masa, nan take Daddy ya bashi umarni da ya shiga. Daddy da Huzaifa a harabar gidan suka haɗu, Huzaifa sai murmushi yake ƙasa-ƙasa don ko ba komai ya samu damar da zai aiwatar da abin da yake ransa. Suna shiga Raihan tana nan kwance kamar gawa bata numfashi ko hannunta baya motsawa, ido ya zura mata yana son sanin musababbin abin da ya sa ta tsinka ƙadangare gida biyu don ko kaɗan babu sa hannunsa a ciki. Yana tsaka da nazari ya riski muryar Daddy yana faɗin, "Dr don Allah ayi wani abu ciwon nan sai ƙara gaba yake yi." Huzaifa ya miƙe tsaye yana zare gilashin idonsa, ya yi jim kamar wanda yake damuwa sannan ya fara magana, "Gaskiya yanayin ciwonta ya fara bani tsoro Alhaji, amma abin da ya fi akwai wani abokina a India ina tunanin sai an fita da ita, amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama."
Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi: