← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 110

Sashe 59

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Raihan ta yi saboda ba ƙaramin kunya ta ji ba, amma don kar ta nuna masa yanayinta sai ta ɗauke kai gefe ta ce, "Tun da kai ka iya ya wadatar ba sai na koyo ba don Allah ka matsa ka ba ni wuri." Kafin ya bata amsa daga bayanta ta ji an furta, "Barista Huzaifa! A sanyaye ya ɗago ya kalli mai kiran nasa don suna haɗa ido ya faɗaɗa fara'arsa da cewar, "Likita bokan turai." Mamaki ne ya kama Raihan don yanayin fuskar wanda aka kira da Barista Huzaifa bata taɓa nuna mata alamar ya taɓa dariya ba. Dr Hussain ne ya ƙarasa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Raihan kar dai kuna da relation Barista?" Ya yi tambayar cikin fara'a don duk wanda ya ga irin tsayuwar da su Raihan suka yi zai ɗauka suna da wata alaƙa. Dr Hussain na gama magana Raihan ta taɓe baki ta ce, "Dr wallahi bansan shi ba, don Allah ka ce ya matsa min zan je gida na kawowa mommy ruwan zafi." Jikin Barista Huzaifa ne ya yi sanyi don yadda Raihan ta yi maganar ya nuna masa a ƙagauce take, don alamu sun nuna Mahaifiyarta ce babu lafiya. Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Barista abokina ne." Ya juya ya kalli Barista Huzaifa ya ce, "Barista kun yi shiru kamar bakwa duniyar, saboda kun danne manya kaya sai ku yi wa talaka nisa." Barista Huzaifa ya matsa daga jikin motar Raihan ya ce, "Wallahi ba haka ba ne, ka san yanayin aikinmu sai a slow. Yanzu haka na shigo gari wani abokina ne aka kwantar da shi da babu lafiya." Dr Hussain ya ce, "Subhanallah ya sunan patient ɗin?" Barista ya waiga yana kallon motar Raihan da ta fice daga harabar asibitin, sannan ya juyo ya ce, " Sunansa Barista Sani ƙofar nasarawa. Amma mun fi kirsansa da ƙofar nasarawa." Da yanayin mamaki Dr Hussain ya ce, "Kar dai shi ne mai matsalar ciwon siga?" Barista Huzaifa ya jinjina kai yana faɗin, "Exertly, and yana jin jiki sai dai mu yi fatan Allah ya bashi lafiya." Gabaɗaya suka amsa da amin. A hankali suka fara takawa Dr Hussain ya ce, "Yanzu za ka wuce ne Barista?" Barista Huzaifa ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Gaskiya wuce wa zan yi dama akwai wani abokina da nake jira but ina da uzuri a waje saboda akwai case ɗin wata yarinya da aka yi rapping ɗinta da nake bincike akai." Dr Hussain cikin jimami ya ce, "Ai dama kuna ganin cases kala-kala Allah ya sa mu dace." Suka amsa da amin har sun je wurin motar Barista za su yi sallama Barista Huzaifa ya ce, "Dr wannan yarinyar da ta wuce fa?" Dr Hussain irin mutannan masu surutu yana jin haka ya washe baki ya ce, "Wai Raihan?" Barista Huzaifa ya gyaɗa masa kai. Nan take Dr Hussain ya zayyane masa komai akan Raihan na haihuwar Mommy, da yake shi ne likitan da ya yi mata Cs. Cikin gamsuwa Barista ya jinjina kai ya ce, "Tsiwarta ta birge ni." Dr Hussain ya yi dariya ya ce, "Mutumina ka rufta dai kawai. Yanzu sai wacce shekarar za mu sake haɗuwa?" Barista ya yi murmushi mai sauti haɗe da faɗin, "Zan ɗan kwana biyu a Kano insha Allah saboda mun samu hutu, zan iya kai kwana huɗu kafin na wuce Kaduna." Sun jima suna tattaunawa daga ƙarshe suka yi sallam Barista ya shiga motarsa ya wuce, Dr Hussain ya koma cikin asibitin.

Raihan tun da ta shiga motarta lokaci-lokaci take zabga tsaki don mutumin ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba, tana zuwa gida ta shiga zabga horn kamar mai shirin tashi sama. A hargitse Kabiru ya leƙa don ganin mai wannan horn ɗin don a iya saninsa mutanen gidan ba sa irin haka. Ganin Raihan ce ya sa shi faɗaɗa fara'arsa, tsayuwarsa a wurin ya dulmiya shi cikin kogin tunani don zuciyarsa ta jima tana yaudararsa akanta. Shi kansa ya san ko a cikin mafarki Raihan ta yi masa nisa kwatankwacin yadda sararin samaniya ta yi hannun riga da ƙasa. Bai yi aune ba ya sake jin ta danna wani horn ɗin da ƙarfi, jiki babu kuzari ya fara jan gate ɗin a hankali ya buɗe yana tsaye wuri ɗaya yana bin ta da wani irin sassanyan kallo. Tana shigo wa tun bata ƙarasa wurin parking ba ta faka motarta a wurin ta sauko, wurin Kabiru ta sake koma wa ta riƙe ƙugu tana kallonsa. Ganin har lokacin bai san tana yi ba ya sa ta ƙarasa wa wurinsa tana tafa hannuwa ta ce, "Filloooo!" A firgice ya ɗago yana sauke ajiyar zuciya suna haɗe ido ya sakar mata wani ni'imtaccen murmushi. Ba ƙaramin kyau ta yi masa ba kasancewar tana sanke da doguwar rigar leshi kafaɗarta maƙale da ƙaramin mayafi. Da ido ta kafe shi tana karantar yanayinsa tamkar wata uwarsa ta haɗe fuska tana faɗin, "Kwana biyu na ga kana cikin damuwa me yake damun ka?" Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don yadda ta yi maganar kamar wata uwarsa ko yayarsa, dariya ya yi mai sauti sannan ya ce, "Hai kai yanzu sai na gaya maka abin da yake damuna?" Raihan ta sake haɗe fuska ta ce, "Ban isa ba ne wai me ya sa fillo ka raina ni da yawa?" Kabiru ya jingine sandar hannunsa ya ce, "Don Allah shekara nawa na baki? A ƙalla na baki kusan shekara bakwai." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wallahi na ɗauka ka fi haka don wannan manyancen naka sai kace ka haife ni." Dariya Kabiru ya yi Raihan ta ce, "Da gaske kana cikin damuwa me yake damunka ko jikin Baba?" Raihan ta faɗa a sanyaye da yake daga baya da zama ya yi zama Kabiru ya sanarwa da Raihan rashin lafiyar da Mahaifinsa yake yi, kuma Daddy ba ƙaramin taimaka masa yake yi ba. Wannan kalma ta Raihan na ɗaya daga cikin abin da ya sa ta sace zuciyarsa saboda tana matuƙar ambatar iyayensa da nuna muhimmancinta akansu. Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Idan jikin nasa ne ya yi tsanani ya kamata ka sanarwa da Daddy a yi wani abu, idan kuma zuwa kake son yi sai ka saka rana ka tafi." Murmushi ya sakar mata ya ce, "Duk ba wannan ba ne wata yarinya nake so amma na san zuciyata yaudarata take yi, don na san ko a mafarki ta min nisa." Tsaki Raihan ta yi haɗe da yin wata irin dariya ta ce, "Don Allah da akan tunanin wata yarinyar har ka shanya ni a ƙofar gida?" Kabiru ya marairaice murya ya ce, "Kin san tasirin soyayya kuwa? Kin sa yadda zuciyata take lugude a kanta? Don Allah kar ki ce haka don na yi nisa a soyayyarta." Jikin Raihan ba ƙaramin sanyi ya yi ba musamman da ta tuna tata tsohuwar soyayyar, don haka ta ɗago ta ce masa. "Lallai su fillo a faɗa ruwa tsamo-tsamo, kasan dai ni ce babar aminiyarka yanzu dai ka bari na je na dawo sai mu yi magana ko ƴar gidan waye zan je nema maka soyayyarta." Kabiru ya yi murmushi don ba ƙaramin jin daɗin bayanin Raihan ya yi ba. Cikin gida ta wuce tana kwaɗa sallama, a hakimce ta samu su Inno sun zabga kwalliya kowacce ta saka sabuwar atamfa hannu ɗauke da hijabi, Raihan na ganinsu tun daga bakin ƙofa ta ce, "Inno ina za ku ne haka?" Inno ta kalli ƙofar da Raihan ta shigo ta ce, "Ke ina Audullahi?" Raihan ta ƙarasa tana ajiye mayafinta ta ce, "Yana wurin matarsa." Goggo ta ce, "Mu fa shirya wa muka yi ya kai mu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ya kai ku ina? Don Allah ina ruwan zafin da zan tafi da shi don sauri nake ina koma wa Daddy zai tafi uzurin gabansa." Ta yi maganar a gaggauce don ta fahimci su Inno asibiti za su ce za su je. Inno ta miƙe tsaye ta ce, "Ai sai dai mu tafi tare amma Allah ya sani yau sai na je na gano jikana duk baƙincikin ki." Raihan ta wara hannu alamun rashin damuwa ta ce, "Na hana ku tafiya ne? Amma gaskiya babu wacce za ta shigar min mota ta riƙa yi min ihu. Na ga jiya ma kun je asibitin nan ya ilahi wurin nan fa ba biki ake yi ba, ina jin ma da yamma Dr zai iya sallamarta." Goggo ta miƙe tsaye a fusace ta ce, "Ki gode wa Allah ba a Albasu nake da zama ba wallahi da kullin sai an yo mota guda daga can an zo duba ta, a farke cikin mai rai sannan ace ba za ka je ka yi masa sannu ba. Ƴar nan kina cikin hayyacinki kuwa." Raihan ta nufi hanyar kitchen tana faɗin, "Ku faɗi duk abin da za ku faɗa amma babu wacce za ta shigar min mota." Flask ɗin shayi ta ɗauko har ta nufi hanyar fita wani tunani ya faɗo mata don ta san sarai idan ta fita su Inno suna iya cewa za su fita su tafi da kansu, juyo wa ta yi ta: "Ku taso mu tafi. Amma wallahi kuka nemi tara min mutane Allah a titi zan zube ku." Ba musu su Inno suka taso suka biyo bayan Raihan suna zuwa Raihan ta buɗe musu suka shiga baya. Kabiru na ganin fitowarsu ya ce, "Su Hajiya Inno yau ma fita za a yi?" Inno ta ce, "Bari Kabiru za mu koma dubo jikin Zainabu kaima ba don tsaron gida ba ai da mun je tare." Kabiru ya ce, "Sai kun dawo a yi mata sannu." Ya ƙarasa maganar yana buɗe musu ƙofa sannan suka fice.
Chapter 59 · 0% Book details