← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 110

Sashe 66

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin zagayen da suke yi ya yi ya wa ya sa Safna ta dubi Dr Hussain ta furta, "Dr ni fa kaina ya kulle, wai da za mu taho ba ta wancan layin muka biyo amma na ga mun yi zagaye ya kai sau huɗu ban ga gidan ba." Dr Hussain tuni shi ma kansa ya ɗaure a cikin zuciyarsa ya furta abin da Safna ta faɗa a don shi ma ba ƙaramin mamaki ya yi ba, yana jin ta yi magana cikin sauri ya ce: "Wallahi kin rigani a fili na riga ki a zuci." Munira da ke kujerar baya ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ya kamata mu wuce gida idan ya so gobe in Allah ya kaimu ba sai mu dawo ba, tun da yanzu fa dare ya fara yi kar a ga mun daɗe..." Maganarta ce ta maƙale sakamakon wayarta da ta fara ringing ganin lambar Mama Hafsa ya sa ta ɗago fuskar wayarta tana faɗin, "Kun ga abin da nake gudu ko? Safna ga Mommynku tana kira." Miƙa wa Safna wayar ta yi jiki a sanyaye Safna ta ɗaga tana faɗin, "Mommy muna hanya wallahi wayata na manta..." Daga can ɓangaren Mama Hafsa ta katse Safna da cewar, "Ba na son sakarcin banza kin san ƙarfe nawa yanzu? Maza ku dawo gidan idan har ba ranki kika manta a gidan ba ai kya bari da safe ki koma ki ɗauko." Mama Hafsa na gama maganar ta katse wayar, jin irin faɗan da aka yi wa Safna ya sa Dr Hussain ya ja akalar motarsa ya juya hanyar gidan mommy. Ba su jima ba suka ƙarasa gidan, tare da yi wa Dr godiya sannan suka buga gida Kabiru ya buɗe musu.

A lokacin da Huzaifa ya tafi raka su Dr sauke ajiyar zuciya Raihan ta yi tana jin wani irin farinciki yana ratsata, ƙaunar Huzaifa ta ji na ratsa cikin zuciyarta ita kaɗai ta saki wani malalacin murmushi. Tana jin alamar shigowarsa ta ƙara jan mayafinta ta rufe fuskarta, lokaci ɗaya ta ji gabanta na tsananin faɗuwa ga wata irin matsananciyar kunyarsa da take ji. Wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta faɗawa duniyar tunani don ta tabbata rashin saboda tun da hakan bai taɓa kasancewa da ita ba ne, ya sa take jin gabanta na faɗuwa. Tana nan zauna ta ji shigowarsa ras! Ta sake ji gabanta ya sake faɗuwa har sai da ta sauke ajiyar zuwa. Babbar rigarsa ya cire haɗe da ajiye wa akan gado sannan ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "My happiness bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Murmushi ta yi ba tare da ta furta komai ba, a hankali ya zame mata mayafin kanra haɗe da rungumota jikinsa. Shiru Raihan ta yi tsigar jikinta na tashi sakamakon jin sabon lamarin da take fuskanta daga wurinsa. Ledojin da ya ajiye ya ɗauko ya buɗe a ƙasa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Sauko my baby." A kunyace Raihan ta ce, "Na ƙoshi." Murmushi Huzaifa ya yi ya furta, "Ashe kuwa zan ɗauko ki cak daga wurin nan." Da sauri Raihan ta sauka ƙasa ai kuwa me zai yi mata ba dariya ba, ya lukuce kumatunta tare da faɗin, "Baby kin fiye tsoro why?" Shiru Raihan ta yi tana murmushi, a hankali Huzaifa ya riƙa yagar naman kazar yana saka mata a baki. Raihan tun tana jin kunya har ta fara sakin jikinta tana karɓa suna ci Huzaifa na sake janta da hirar soyayya. Huzaifa ya iya sace zuciyar mace da kalamai don haka suka ƙara tasiri a zuciyarta Raihan ta ƙara jin wata matsananciyar ƙaunarsa ta malale birnin zuciyarta. Sai da suka ci suka yi ƙat sannan Huzaifa ya kwashe kayan wurin ya kai su cikin kitchen, Raihan na rakuɓe a gefe fargaba fal cikin zuciyarta Huzaifa ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi ya riƙo hannunta. A sanyaye ta bishi ya zauna akan gado ya tallafota jikinsa haɗe da fara shafa jikinta yana faɗin, "I really miss you wifee." Murmushin yaƙe Raihan ta yi don har lokacin gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, tun tana ɓoye tsoronta har ya bayyana a fili don saƙwanni Huzaifa yake aikawa Raihan zafafa. Ganin duk ta firgice ya sa Huzaifa ya ja ta har tsakiyar gado, tana biye da shi tamkar raƙumi da akala. Sauka ya yi ya kashe ƙwan fitilar da ke cikin ɗakin sannan ya kunnawa musu night lamp, kallon Raihan ya yi ya fara ƙoƙarin cire rigarsa. Raihan na ganin haka ta runtse idonta jikinta na karkarwa, tana cikin wannan yanayin bata yi aune ba ta ji Huzaifa a gefenta yana yunƙurin rabata da kayan jikinta. Muryarta na rawa ta dube shi ta ce, "Hubby ba mu yi sallar nafila ba." Cikin wata irin kasalalliyar murya ya furta, "Wacce irin sallah kuma?" Huzaifa bai san ya yi wannan maganar ba domin tuni ya fara fita daga hayyacinsa. Raihan ta fara ƙoƙarin kare jikinta ta ce, "Sallar Nafila." Huzaifa ya saka hannunsa cikin jikinta haɗe yawo da su cikin sassan jikinta. Yarrr ta ji tisgar jikinta na tashi, shi kuwa Huzaifa tuni ya yi nisa gabaɗaya ya fita a hayyacinsa saboda ƙamshinta da yake sake rikita tunaninsa. Kai hannunsa kan ƙirjinta ya sake ruɗar masa da lissafi haɗe da sauke ajiyar zuciya akai-akai. Jikin Raihan sai rawa yake don haka ta kai hannunta da niyyar dakatar da shi cikin yanayin fitar hayyaci ya furta, "Kar ki dakatar da ni don Allah, domin ke mallakina ce." Hawaye Raihan ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah ka bari sai gobe."Sannu a hankali Huzaifa ya fara neman kusantar Raiha nan take ta ji wani irin abu yana sukarta, tun bata tanka ba har ta ji ba za ta iya shiru ba domin abin na ƙoƙarin illatar da ita. Cikin tsananin azaba Raihan ta fara ja da baya a firgice tana faɗin, "Hubby don Allah ka bari wallahi ciwo nake ji me ye a jikinsa yake sukata." Huzaifa bai bi ta kanta ta sake fisgota da ƙarfi don babban burinsa ya ga ya cimma manufarsa. Wata irin azaba ce ta riƙa ratsa cikin jikinta da sauri ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, ta tattare ƙarfinta wuri ɗaya ta hankaɗe shi tana ja da baya haɗe da takurewa wuri ɗaya. Ta dishi-dishin hasken da bai gama garwaye ɗakin ba ta hango wasu irin gajerun gashi masu kaifi kamar ƙayoyi na tsirowa daga jikinsa. Ƙirjinta ne ya buga tsoro ya fara kamata, tana cikin wannan halin ta riski muryarsa yana faɗin: "Me ya sa kike son hana ni halalina?" Raihan na daga gefe a zaune ta ce, "Wallahi wani abu ne yake fitowa a jikinka sukata yake yi." Hannunsa ya kai ya kunna ƙwan lantarkin ɗakin, nan take haske ya garwaye ko ina. Ganin haka ya sa Raihan ta fisgo mayafinta ta rufe jikinta a kunya ce. Kawar da kanta ta yi daga kallonsa don kunyarsa take ji. Tana zaune bata yi aune ba sai jin ta, ta yi tana yawo a sama mayafin jikinta ya faɗo ƙasa. Dariya Huzaifa ya saka ba shiri Raihan ta dubi wurinsa tana faɗin, "Hubby mai yake faruwa wayyo Allah na." Suna haɗa ido gabanta ya faɗi ganin waɗansu irin baƙaƙen gashi masu tsini suna tsirowa daga jikinsa, tana shirin yin magana ta ji ya sake cewa, "Ke matata ce don haka a yadda kike haka nake son ganinki." Yana rufe bakinsa waɗansu irin Manyan ƙaho ƙwaya biyu suka fara hudowa ta tsakiyar kansa, runtse ido Raihan ta yi a firgice tana cewa, "Waye kai Dama kai matsafi ne ka aure ni ban sani ba." Tana rufe baki ta bayanta ta ji an fara shinshinarta, a hargitse ta juya baya nan take ta ci karo da shi. Wata irin gigitacciyar ƙara ta ƙwalla jikinta na rawa ta fashe da wani irin matsanancin Kuka, dafe kansa ya yi da hannu biyu sannan ya furta: "Ba na son ki riƙa dagula lissafin rayuwarki, don ko kaɗan ba zan cutar da ke ba. Ni mai ƙaunarki ne har abada don haka ki kwantar da hankalinki mu yi rayuwar farinciki." Cikin kuka Raihan ta ce, "Ni wallahi na fasa aurenka don Allah ka mayar da ni wurinsu Daddy." Huzaifa ya bushe da wata irin dariya mai haɗe da kuka, sai da ya jima yana yi sannan ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce, "Idan kina wannan mafarkin tun wuri ki daina domin ni da ke mutu ka raba, babu wurin da ya fi miki cancanta da zama kamar nan don haka ki daina tunanin akwai ranar da za ki koma wurinsu." Wannan magana ta sake ɗugunzuma hankalin Raihan a firgice ta sake fashe wa da kuka, luuuuu ta ji ta faɗa kan katifa tana kwanciya babu jima wa ta ga Huzaifa ya faɗo gefenta cikin wannan mummunar surar.
Chapter 66 · 0% Book details