← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 110

Sashe 25

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Huzaifa ya furzar da iska mai zafi cikin ƙunan rai ya dubi sauran sakarun aljanun da suka riƙe su, yana shirin fusgewa ya ruski muryar Dattijon na ci gaba da cewa, "Da ace wannan alƙaryar tana magana tabbas da ita da kaina za ta shaide ni akanka, idan baka manta ba shekaru ɗari huɗu da suka wuce ka yi bankwana da ni da alƙaryata. Kamar yadda nake zaune a wurin nan ranar da za ka tafi sai da na tabbatar maka ko ba daɗe ko ba jima za ka dawo gare ni, kuma sai da na jaddada maka za ka dawo gare ni kana mai neman buƙata a wurin shin akwai abin da na ƙaga na faɗa sabanin abubuwan da suka gabata?" Huzaifa ya murtuke fuska rai a ɓace ya dubi kakansa yana faɗin, "Ka zartar da umarni a sake ni domin wannan ƙasƙanci ne a wurina a ce ina jininka hadima su dakatar da ni."Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni sannan ya ce, "Kowa ya ƙona rumbunsa ya san a inda toka take kuɗi, Huzaifa ka ɓarar da damarka a lokacin da kake tsaka da iko da ita, karka ji haushin kowa ko ka ƙullaci kowa domin duk abin da ya fi kaine sanadi." Jabbul-ƙasi ya tsahirta da zancensa yana kallon Dakarun da ke riƙe da huzaifa ya ce, "Ku sake shi ya ku masu biyayya." Tun bai rufe baki ba suka saki Huzaifa, Huzaifa ya kalle su cikin jin haushi sannan ya fara takawa zuwa mazaunin kakansa. Tsugunne ya yi a gaban Jabbul-ƙasi sannan ya fara da cewa, "Na zo ne domin wata buƙata amma sai ka sallami waɗancan." Huzaifa ya yi maganar cikin isa da ƙasaita. Jabbul-ƙasi ya bushe da wata irin dariya, nan take jaririn aljanu suka firgice domin basu taɓa jin irin wannan dariyar ta sa ba, ƙananan dabbobin da ke kusa da tsibirin suka faɗi matattu wasu daga cikinsu suka bazama, hatta dakarun da ke tsaron tsibirin sai da wani irin matsanancin tsoro ya kama su. Huzaifa yana zaune ƙyam ko motsi bai yi ba, saboda ƙarfin zuciya irin tashi. Jabbul-ƙasi ya jinjina kai yana kallon Huzaifa ya ce, "Idan za mu ninka shekarun da muka yi a baya sau ɗari tabbas halinka ba zai taɓa sauyawa ba Huzaifa, ko ɓata ka yi a cikin dubbanin jinnu wannan ƙarfin izzar taka ita za ta sa na gane kai ɗin jinina ne. Ka aikata min babban laifi sama da shekara ɗari biyu ban sa ka a idona ba, amma yau ka zo da buƙatarka wurina sai dai maganganunka suna nuna min tamkar umarni kake bani." Huzaifa ya ɗago yana yi masa wani irin kallo ba tare da ya furta komai ba, Jabbul-ƙasi ya zurawa Jikan nasa ido yana jiran cewarsa. Sun jima a haka ba tare da Huzaifa ya ce uffan ba sannan Jabbul-ƙasi ya fahimci abin da ya sa Huzaifa ba yi magana ba, ɗaga ido ya yi ya kalli dakarun dake wurin tun bai yi magana ba suka ɓace daga wurin kamar yadda Huzaifa ya buƙata.

Jabbul-ƙasi ya dube shi don jin abin da Huzaifa zai faɗa ba don ba shi da masaniya dangane da abin da yake tafe da shi ba. Huzaifa ya sake ɗaure fuska tamau ya ce, "Matata ce take cikin wani yanayi, duk bincikena na rasa gane inda ta dosa." Jabbul-ƙasi ya yi murmushin dattijantaka sannan ya ce, "Zaujinka wacce kana nufin Mugaza? Domin idan ita ko wata biyar da suka gabata ta kawo mana ziyara ba mu ga wani saɓanin lamari a tattare da ita ba." Huzaifa ya kauda kansa gefe cikin takaici sannan ya ce, "Matata Raihan nake nufi, na aureta tsawon shekarun baya. A da babu abin da yake mini shamaki da ita, ina kusantarta a duk lokacin da na yi niyya. Ta haifa mini ƴaƴa takwas amma duka Mugaza ta salwantar mini da su sai na ƙarshen nan ne ya tsaya. Yanzu haka ita nake zargi akan rikicewar al'amuranta don haka nake son ka yi mini wani abun a kai." Jabbul-ƙasi ya sauke ajiyar zuciya bayan ya gama sauraron Huzaifa ya ce, "Ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma." Huzaifa ya dube shi cikin rashin fahimta ya yana shirin tambayarsa Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa, "Raihan matarka ce amma kana tafe da gingimemen ƙalubale a gabanka, ta yi maka nisa mai tazarar gaske don yanzu baka da ikon da za ka sarrafata a ƙarƙashin ikonka." A firgice Huzaifa ya ɗago a firgice don jin abin da Jabbul-ƙasi ya faɗa, hankali a tashe ya furta, "Ka yi mini bayanin da zai gamsar da gangar jiki da ruhina."Jabbul-ƙasi ya kishingiɗa daga wurin da yake ya ci gaba da cewa, "Raihan har gobe matarka ce matuƙar za ka jajirce tsayin daka akan soyayyar da kake mata. Amma batun ka sarrafa ko ka kaita duk wurin da kake buƙa bai taso ba, baka da ikon sarrafata domin tana tare da ruhin Gurzuzu jinnu-nariy.

A firgice Huzaifa ya miƙe tsaye jikinsa na karkarwa ya furta, "Ya aka yi ruhin Gurzuzu ya kai ga Raihan? Waye ya haɗa ta da shi wanene ya tari aradu da ka?" Jabbul-ƙasi ya tashi zaune ya ƙurawa Huzaifa ido yana kallo, kamar ba zai tanka masa ba sai daga baya ya ce, "Ni kaina bansan waɗannan amsoshin ba domin Gurzuzu ya wuce tunanin mai tunani balle ruhinsa. Matsawar tana tare da ruhin Gurzuzu duk wani bincike da zan yi aikin banza ne, a dul faɗin duniya babu wanda zai iya karya alƙadarin ruhin Gurzuzu mutum ɗaya ce tal, kuma a halin da ke ciki ba ni da yaƙinin har yanzu tana doro ƙasa domin tun ina ina goyon mahaifiyarka rabona da ita..." Cikin sauri Huzaifa ya katse Jabbul-ƙasi da cewar, "Wacece ita? A ina take? Wacce alaƙa gare ta da Gurzuzu da har za ta iya karya alƙadarinsa? Ya za a yi na ganta?" Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai sauti yana shirin magana wasu baƙaƙen aljanu suka shiga wurinsa suna sauke ajiyar zuciya, na farkonsu ya fara cewa: "Boka Iliyasu ya sadaukar maka da baƙaƙen raguna biyu tare da zakaru jajaye uku sakamakon aikin matar nan da aka kashe uwar mijinta wacce ka tallafa masa." Jabbul-ƙasi ya jinjina yana murmushi, na biyu ya ce: "Boka Harisu na saman tsauni ya baka kyauta mushen jaki da maguna biyar akan aikin mijin matar nan da ka taimaka masa wacce ta rufe bakin mijinta a kan dukiyarsa." A wannan karonma Jabbul-ƙasi ya sake yin murmushi, suna shirin tashi daga wurin ya dakatar da su da cewa: Yanzu aiki huɗu ne a gabanmu. Na ɗaya akan ɗan Kasuwan nan da za a haukatar da shi kai Bilgilu kaine zaka zartar da wannan aikin. Aiki na biyu akan ma'aikacin kwanstom ne wanda za mu cire masa ƙaunar aiki domin mataimakinsa ya samu nasarar ɗarewa kujerara, kai Billu kai ne da wannan aiki. Sai sauran ayyukan biyun da suka rage na macen nan da zamu sakawa warin jaɓa ne da saurayin nan da zamu kashe shi a kan budurwar nan. Cikin girnamawa suka jinjina kai, Jabbul-ƙasi ya ci gaba da cewa: "Za mu fara aiki daga gobe." Suna amsa masa suka ɓace daga wurin.

Huzaifa da yake cike da ƙaguwa da jin amsar tambayoyinsa ya kalli kakansa yana cewa, "Ina ƙaugauce da jin amsar tambayata." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa yana faɗin, "Duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, Huzaifa daɗina da kai gaggawa shi ya sa saurari lamuranka suke chaɓewa. Burtultika ita ce macen da za ta iya sarrafa ruhin Gurzuzu, a ƙalla ta bani shekari dubu ɗaya da ɗari biyu. Tana rayuwa ne a dajin KALULLUƁU da ke ƙarƙashin Tsauni Zukkin. Daga wannan tsaunin nawa tafiya ce ta shekara ɗaya da rabi, idan har ka same ta da rai za ka yi zaman watannin biyar a fadarta kafin ka samu ganawa da ita. Idan ka sadu da ita tamkar buƙatarka ta biya, ita ɗin tsohuwar budurwar Gurzuzu ce. Labari ya same ni cewar Gurzuzu ya mutu ne saboda tsananin kishinta, ko uwarsa baya jin maganarta kamar yadda yake jin maganar Burtiltika." Jabbul-ƙasi ya kalli Huzaifa cikin rashin damuwa ya ce, "Dabara ta ragewa mai shiga rijiya zaɓi ya rage naka, idan za ka juri wannan tafiyar zan iya taimaka maka da dakarun aljanu masu yi maka rakiya. Idan kuma ba za ka iya ba shi kenan ka ƙyale yarinyar mutane ta ci gaba da rayuwa, kaima ka ci gaba da rayuwarka da Mugaza.

"Koda nisan tafiyar ta yi nisan zai ƙare numfashina zan hallici wurin domin zan iya sadaukar fa komai don ganin jindaɗi, walwalar Raihan sun dawo. Taimako ɗaya na ce ka yi min domin neman hanyar mafita, amma ba na buƙatar agajin dakarunka. Raihan tawa ce ni kaɗai don haka wannan yaƙim nawa ba na neman sa hannun kowa, zan koma gida domin na ɗaura ɗamarar zuwa ga dajin KALULLUƁU." Zumbur Huzaifa ya miƙe yana shirin tafiya Jabbul-ƙasi ya katse shi da cewar, "Ina alfahari da samun nagartacen jika tamkar ka, amma ka sani akwai ƙura a tatattare da yarinyar nan bincike na yana nuna wata baƙar ƙura na bibiye da inuwa yarinyar. Zan yi maka fatan nasara domin duk lalacewa kai ɗim jinina ne, dukda kai mai bijirewa umarnina ne zan fi son ka yi nasara ko ba komai za ka shiga kundun tarihi na wanda suka ziyarci Burtultika." Huzaifa har ya je bakin ƙofa ua waiga ya ce, "Ka riƙe fatan nasararka domin ni dama can ɓai nasara ne." Yana gama maganar ya fice daga tsaunin, Jabbul-ƙasi ya yi murmushi mai ɗauke da ma'anoni a fili ya furta, "Yaro kenan man kaza."
Chapter 25 · 0% Book details