Sashe 54
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sannu a hankali duk wasu abubuwa da Raihan take ji sai suka fara ja baya, Mommy na bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta kawar wa da Raihan damuwa. Inno da Goggo kowaccensu sai da ta karɓo wa Raihan turare da maganin sha da wanka. Sai da Mommy ta yi da gaske sannan Raihan ta karɓa don ba ƙaramin haushin su Inno take ji ba, musamman idan ta tuna zancen sake wani auren da suke yi mata. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa kwanaki suka riƙa wucewa watanni suka shuɗe, Raihan ta rage damuwar da take ciki sosai tana walwalarta kamar kowa sai dai lokaci-lokaci Salim yana faɗo mata a rai. A duk lokacin da ta tuna shi tana jin ba daɗi sai dai ta yi masa addu'a, amma har lokacin gani take babu wani namiji da zai iya maye gurbin Salim don haka ko maganar yin aure bata son ji. Zumunci mai ƙarfi ne ya sake shiga tsakanin gidansu Raihan da gidansu Salim, ƙannensa na matuƙar ganin girmanta suna ganin mutumcinta. Lokaci-lokaci sukan kai mata ziyara musamman Farida da ta ƙwallafa ranta a kan Kabiru mai gadi.
Bayan shekara biyu.
Abubuwa da dama sun faru ciki har da auren Fatima ƙanwar Salim, Raihan ta haɗa mata sha tara ta arziƙi don su Fatima ba su yarda ita ba. Ranar da suka je Dinner bikin su Fatima ita kaɗai ta riƙa kallonsu tana tuna lokacin ta su dinner, hawaye ta ji ya zubo mata a fakaici ta goge idonta jiki babu ƙwari ta miƙe ta je ta yi wa su Fatima liƙi sannan ta wuce gida. A ƴan kwanankin haka ta yi ta fama da tunanin Salim sai daga baya ta watsar da komai ta fauwala wa Allah lamuranta. Azumi saura sati ɗaya Daddy ya biya musu zuwa Dubai daga nan za su wuce umara ƙasa mai tsarki, don Raihan da kanta ta yi wa Daddy magana akan za ta fara sarin kaya daga Dubai zuwa Nigeria, bai hanata ba don ta nuna masa zamanta haka ba daɗi kuma aikin gwamnatin da ta ci buri a baya duk ya fice mata a ka. Tare da su Inno suka tafi gidan sai Kabiru kadai suka bari, kwanansu biyu a ƙasar Dubai da daddare Raihan da Mommy sun fita zuwa wani store don yin siyayyar abin da ba a rasa ba, kwatsam suna gabda fitowa kamar almara Raihan ta ganta hannunta ɗauke da wasu ƙananan yara biyu mace da namiji. Cikin tsananin mamaki ta furta, "Intisar!" Ke nake gani ko idona ne?" Intisar cike da mamaki ita ma ta dubi Raihan ta ce, "Raihan ke ce?" Rungume juna suka yi Mommy ta ja hannun yaran wanda da alama ƴan biyu ne mace ba za su wuce shekara ɗaya da rabi-rabi ba. Raihan ce ta fara ɗagowa ta dubi Intisar ta ce, "Yanzu Intisar kina duniyar kika guje ni an ya amintaka ta ce haka?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Raihan ba za ki gane ba, abubuwa da dama sun faru bayan rabuwarmu labari ba zai yuwu a nan ba sai mun zauna." Raihan ta juya wurin yaran Intisar ta rungumo su tana jin wata irin ƙaunarsu, ido ta ƙura musu tana son sanin inda ta san fuskarsu amma ta kasa. Ɗaukan macen ta yi ta ce, "Amma twins ne ko Intisar?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Su uku ne Salma na hannun Daddynta." Kafin Raihan ta yi magana wani sihirtacen ƙamshinsa ya doki hancinta, waigawa ta yi don ganin mai wannan ƙamshin da ko a mafarki ta ji shi ba za ta manta ba. Karaf idonta ya sauka akansa wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta har ya sa jikinta ya ɗauki tsuma kamar mazari. Bakinta na rawa ta furta, "Salim! Don Allah kai ne?" A lokacin Mommy ta kai idon wurin cikin tsananin mamaki take bin sa da kallo don ko makaho ya shafa zai tabbatar da wannan Salim ne ko tantama babu.
Salma da ke hannunsa ya miƙawa Intisar ba tare da dubi wurin da Raihan take ba ya ce, "Cutie kin san Salma ta fi kowa rigima kika haɗa ni da ita." Intisar karɓar Salma ta yi tana murmushi ta ce, "Hubby ga aminiyata Raihan da nake gaya maka, yau Allah ya yi mun sake haɗuwa." Da murmushi ya dubi Raihan wacce ta kafe shi da ido ya ce, "Hey Aminiyarmu ina kika shiga kullin Cutie sai ta min hirarki." Hawaye ne ya fara zarya a fuskar Raihan ta furta, "Salim baka gane ni ba ne?" Da mamaki ya dube ta Intisar ma ta kalle ta sannan ta ce, "Salim kuma? Waye kuma Salim? Daddynsu Salma ne fa Raihan ko kin san shi ne." Kuka ne ya kwace wa Raihan ta ce, "Wallahi mijina, don Allah Salim ka gaya mata."
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
30
Mijin Intisar da ke tsaye cikin mamaki ya ce, "Mijinki kuma? Cutie kin ji me take faɗa kuwa?" Da sauri Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Raihan ki nutsu me yake damunki kina hauka ne?" Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Don Allah mommy kin gani ko maganaina ne suke yi mini gozo? Kina ganin abin da nake gani ke ma kin ga Salim ko?" Intisar fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Mommy don Allah me yake faruwa waye kuma Salim." Ganin mutane sun fara kallonsu saboda hayaniyar da Raihan ta fara yi ya sa mommy ta ce, "Mu fita waje don kar idon mutane ya yi mana yawa." Ba musu Intisar ta riƙe hannun yaranta Maigidanta ya riƙo mata ɗaya Raihan kuma tana riƙe a hannun mommy. A wurin motarsu Intisar suka tsaya har lokacin Raihan bata daina kallon Mijin Intisar ba, Mommy ta ciro wayarta ta nunawa Intisar hotunan auren Raihan ta ce, "Salim da kika ji Raihan tana faɗa yana tsananin kama da mijinki amma suna da bambamci saboda Salim yana da siririn tsagu a goshinsa. Haka Allah yake lamarinsa ya yi mutane masu kamanni iri ɗaya kuma mazauna wuri mabambamta." Tun daga farko har ƙarshe sai da Mommy ta bawa Intisar labarin abin da ya faru a auren Raihan, Intisar na gama jin labarin ta fara ruwan hawaye. Intisar ta dubi Raihan fuska ɗauke da hawaye ta ce, "Bestie a ranar da abin nan ya faru da ke a ranar na samu waya daga gida cewar Mahaifina ba shi da lafiya. Ban yi ƙasa a gwiwa ba na wuce garinmu don yananyin ciwonsa ance yana jin jiki. A ranar sa na je a ranar Allah ya yi masa rasuwa nan muka shiga tashin hankali, Mahaifinmu shi ne komai namu kuma ya rasu dama duk abin da yake yi mana ƙarfin hali ne. A kan dole muka shiga gwagwarmayar rayuwa don dangin mahaifinmu ba sa taimaka mana da komai. Kwatsam bayan wasu watanni aka yi wa Mahaifiyata shawarar tafiya saudiya yin aikatau, don haka muka shirya mahaifiyarmu ta sayar da duk wani abu da ta mallaka muka tafi ni da ita. Zuwanmu ƙasar babu wuya sai Allah ya haɗa ni sa Salman, shi ma asalinsa ɗan Najeriya ne amma shi da iyayensa duk mazauna saudiya ne. A ganina ya yi min nisa saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma ya nuna ni yake so don haka zai iya rayuwa da ni, yanzu haka shekararmu biyu da rabi da aure kuma yaranmu uku ga su, Salma, Salim Suhaima. Haihuwar fari na haife su ƴan uku yanzu haka jiya muka zo ƙasar nan jibi za mu wuce Spain." Intisar ta ƙarasa bayaninta tana kallon Raihan.