← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 110

Sashe 84

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Al'amin shi ya taimakawa Sumayya ta gyara kanta ban da raki babu abin da take yi, duk ta cika ɗakin da ihu don ma Al'amin yana nuna mata ta yi shiru kar maƙota su ji abin da yake faruwa, ita kuwa Sumayya da biyu take ihun don Raihan ta ji ta tabbatar da wani abu ya faru a tsakaninsu. Ya rakata toilet suka gyara jikinsu sannan ya ɗauro alwala yana fito wa ya zura jallabiyarsa ya ɗauko dadduba ya fita, ɗakin Raihan ya wuce ya tura ƙofa har a lokacin bacci take yi. Amma kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci baccin da take yi ba na daɗi ba ne, a takure ya ganta wuri ɗaya ya sa hannu ya fara buga ƙafarta. Buɗe ido ta yi yana ganin haka ya furta, "Ki tashi ki yi sallah." Jiki ba ƙwari Raihan ta miƙe ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah. Tana zaune tana lazumi bacci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta sani ba, don bacci ne sosai akanta tun da bata samu yin bacci da wuri ba. Cikin baccinta ta ji ana kiran sunanta, tashi ta yi tana murtsika ido sai a lokacin ta fahimci a wurin da take kwance. Ganinsa ta yi cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau ya yi mata ba har bata san lokacin da ta shagala da kallonsa ba, iska ta ji ya hura mata a fuska sannan ya ce, "Ki zo ki taimakawa Sumayya ta gyara jikinta daga nan sai ki girka mana breakfast, saboda gari ya waye almost nine thirty yanzu." Raihan ji ta yi kamar an kwaɗa mata guduma akanta don ta fahimci abin da Al'amin yake nufi, haɗiyar yawu mai ɗaci ta yi ta miƙe jiki ba ƙwari ta furta: "Ok bari na yi wanka na zo." Guntun tsaki Al'amin ya yi ya ce, "Na saka ki abu yanzu jira zan yi sa kin yi wanka, jiranki za ta yi tana fama da kanta har sai kin shirya." Ajiye daddumar hannunta ta yi ta wuce sum sum sum ba tare da ta iya furta masa komai ba saboda yadda zuciyarta take zafi. Tana tafe gabanta na faɗuwa har ta tura ƙofar ɗakin sumayya ta shiga, daga falo ta riƙa sallama sai da ta yi kusan sau uku sannan ta ji Sumayya ta amsa ta kuma ce mata ta shiga. Raihan na shiga ƙirjinta ya buga ganin yadda Sumayya ta yi ɗaiɗai daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga kayanan kayanta na ciki duk a warwatse a ƙasa. Daga bakin ƙofa Raihan ta tsaya ta ce, "Ina kwana?" Sumayya ta taɓe baki da kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta amsa sannan ta ɗora da cewa, "Na tura Hayati don ya kira ki, ki zo ki taya ni gyara jikina saboda da asuba shi ya gyara ni so kuma na ga ya gaji da yawa. Amma na ga ke bazawara ce kin san komai wannan ba baƙonki ba ne, sai kuma na ga kin yi min ƙerere aka." Zuciyar Raihan ce ta fara tafasa wani irin abu ya tokare maƙoshinta, bata furta mata komai ba ta ƙarasa bakin gadon ta ce, "Ai da asubar ma da kin turo shi sai na zo na gyara ki, ai duk yi wa kaine." Sumayya ta fahimci baƙar magana Raihan ta caka mata don haka ta yi murmushi tana faɗin, "Na so tura shi amma yadda ya liƙe min ya sa dole na haƙura saboda kin san irin wannan daren sai ana yi wa Angwaye uzuri." Maganar Sumayya ba ƙaramin ɓata ran Raihan ta yi ba, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe zuciyarta. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla da ƙyar ta samu damar mayar da su ba tare da Sumayya ta gani ba. Amma yanayinta kaɗai zai nuna alamar bata ji daɗin maganar ba, miƙa mata hannu Sumayya ta yi ta ce: "Riƙe ni mu shiga toilet ki sirka min ruwa." Babu yanda ta iya don ta ji takun Al'amin ya nufo ɗakin, Raihan na ruƙo sumayya ta zuba wata uwar ƙara tana yarfe hannu. Da sauri Al'amin ya ƙaraso yana cewa, "Baby lafiya? Jikin ne?" Girgiza kai ta fara yi tana cije baki, tsaye ya yi a gabanta ya dubi Raihan yana faɗin: "Kamata ya yi ki yi mata a hankali bata da lafiya fa, bakya ganin yanayinta.." Da ido Raihan ta bishi don ranta ba ƙaramun ɓaci ya yi ba, bayan cin kashi da cin fuskar da aka yi mata amma ya zo ƙoƙarin rufeta da faɗa yake akan abin da bata da hurumi da shi. Sumayya ce ta riƙo hannunsa tana cewa, "Hubby ka ɗaga ni ba zan iya tashi ba." Jiki na rawa Al'amin ya ƙarasa bakin gadon yana shirin ɗaukan Sumayya da gayya ta saki zanin jikinta tana faɗin, "Hubby ba haka ba wallahi ciwo nake ji kamar yadda ka ɗauke ni da Asuba." Jin zuciyar Raihan na neman tarwatse wa ya sa ta fice daga ɗakin idonta na zubda hawaye, tana shiga ɗakinta ta faɗa kan gado haɗe da fashewa da matsanancin kuka. A baya ta ɗauka idan ta samu Al'amin ta gama maraicin soyayyarsa, tana yi masa soyayyar da take jin ba za ta iya sharing ɗinsa da wata ba amma sai ga shi akan idonta yana rungume da wata, ta ɗauka zama da shi a inuwa ɗaya shi ne gushewar baƙincikinta amma alamu sun nuna sabon babi ta buɗe na ƙunci da matsin rayuwa. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta ta faɗa toilet ta yi wanka bayan ta shirya ta fita kitchen don girka musu abinci kamar yadda Al'amin ya ce.
Chapter 84 · 0% Book details