Sashe 65
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda ta saba masa a duk lokacin da ta fahimci yana cikin damuwa haka ya yi mata, miƙe wa ya yi tsam ya shiga ɗakinsa ya buɗe ɗan ƙaramin firjinsa ya ɗebo mata ruwa mai sanyi, har lokacin da ya koma bata motsa daga yadda ya bar ta ba. Sai da ya tsiyaya mata ruwa a kofi ya miƙa mata sannan ya zauna a kan kujera ya furta, "Fillo!" Ɗago wa ta yi ta kalle shi bata san dalili ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Kawar da kansa gefe ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa miƙe wa tsaye ya yi ya bata baya sannan ya ce, "Idan kina son mu yi magana don Allah ki daina barin hawaye na zuba daga idonki." A hankali ta sa hannu ta goge ƙwallar idonta, juyo wa ya yi mata hararar wasa ya ce, "Ga wata nan a gefe." Ya faɗa yana nuna gefen fuskarta. Ita ma harar wasa ta sakar masa ta ce, "Ai dole ka ga makwancina Fillo tun da ina hawaye a gabanka." Kabiru yana shirin yin magana suka ji ana buga gida. Da sauri Kabiru ya ƙarasa wurin ya leƙa don ganin mai buga wa nan take ransa ya yi mummuna ɓaci, sai da furzar da iska mai zafi sannan ya dubi Raihan murya a daƙile ya ce, "Kin yi baƙo!" Da mamaki ta dubi Kabiru ta ce, "Baƙo kuma? Waye haka?" Ta yi maganar cikin mamaki don ko kaɗan ba su yi hirar zuwan Barista Kano ba. A hankali Kabiru ya zare sakatar ƙofar Barista Huzaifa ya shiga yana watsa wa Kabiru kallo, haka shi ma daga ɓangaren Kabiru wani ƙasƙantaccen kallo ya watsa wa Barista sannan ya shige ɗakinsa ba tare da ya tanka masa komai. Raihan na ganin Barista ta faɗaɗa fara'arta haɗe da faɗin, "Amini kai ne a gari? Gaskiya ka iya suprise me ya sa baka gaya min ba?" Fuska babu walwala Barista Huzaifa ya ce, "Dole ki ce haka tun da kina wurin mai gadi kuna hira, na kira ki ya fi sau shurin masaƙi baki ɗauka ba." Raihan ko kaɗan bata ji daɗin kalmar da ya gayawa Kabiru ba don haka ta nuna masa kujerar da Kabiru ya tashi, yamutsa fuska ya yi ya ce: "Wannan ba mahallina ba ne ki bari wanda ya fi cancanta da ya zauna idan na baku wuri sai ya zauna, ku ci gaba da hirarku. Amma fa ki yi haƙuri na katse muku jin daɗi don na san ba haka kuka so ba..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta katse shi da cewar, "Haba Barista me kake faɗa haka ne, wai baka san waye Kabiru ba?" Tana rufe baki Barista ya rufe ta da faɗa Raihan tun tana kare kanta har ta ja bakinta ta yi shiru, duk da ta san Barista na nuna kishinsa akan Kabiru bata taɓa tsammanin abin nasa ya kai haka ba. Kabiru na daga ɗaki ya ji ba zai kasa daure ba don haka ya fito a zafafe ya kalli Barista ya nuna masa ƙofa haɗe faɗin, "Malam zo ka fice idan ka gama." Da mamaki Barista ya kalli Kabiru sai ya saki dariyar takaici ya ce, "Lallai mai gadi ya samu wuri..." Raihan ta ƙarasa gaban Kabiru ta furta, "Me kake yi haka Fillo ka na cikinn hayyacinka kuwa? Mijin da zan aura ne fa me ye naka a ciki?" A hargitse ya ɗago ya kalli Raina don maganganunta ba ƙaramin ƙara masa ɗaci a zuciya suka yi ba, Barista ta naɗe hannunsa sannan ya ce: "Da baki ba shi damar ya min haka babu yadda za a mai gadi ya raina mijin da za ki aura." Raihan ta dubi Kabiru ta ce, "Fillo ka bashi haƙuri." Wannan karonma kallonta ya yi ba tare da ya furta komai ba, sai da ta sake maimaita abin da ta faɗa yana shirin yin magana ta katse shi da cewar, "Ba na buƙatar jin komai ka bashi haƙuri na ce." Kabiru ya ƙarasa gaban Barista suka yi ido biyu sannan ya waiga ya kalli Raihan ya ce, "Komai zan yi saboda ke ne don kina ɗaya daga cikin mutane masu muhimmanci a gare ni." Babu musu ya bashi haƙuri sannan ya koma ɗakinsa. Barista ya jima Raihan tana bashi haƙuri sai daga baya ya sauko sannan suka ci gaba da tattauna akan lamuran da ya shafi bikinsu. Duk yadda Raihan ta so kauce wa yin wata bidi'a a bikin sai da Barista Huzaifa ya shawo kanta ta aminci, za su yi Dinner da Kamu amma daga haka sai ɗaurin aure. Duk abin da yake faruwa Kabiru yana daga ɗaki yana jin su, sai dai gabaɗaya zuciyarsa a dagule take. Sun jima suna hira sannan Barista ya yi mata sallama ya wuce gida, Raihan duk da yadda zuciyarta ta kai ga azalzalarta yi wa Kabiru magana haka ta danne don ta san kowaye aka yi masa abin da Kabiru ya yi ba zai ji daɗi ba, don haka tana raka Barista ta wuce gida.
Sannu a hankali haka suka ci gana da rayuwa Kabiru na fushi da Raihan ita ma tana yi don ko fita wurinsa ta daina yi, Raihan tuni aka shiga yi mata gyaran jiki kala-kala ban da ƙamshi babu abin da take yi. Hatta kaya idan ta cire ƙamshi suke yi saboda yadda turare ya ratsa jikinta. Ranar laraba aka yi kamun amarya a cikin gidansu Raihan, wani ɗinki aka yi mata da atamfa ba ƙaramin kyau ta yi ba. Kowa ya ganta sai dai ya ce masha Allah saboda yadda aka zane hannunta da ƙafarta da jan lalle, ga kwalliyar da aka yi mata daidai misali ta yi mata kyau. Washegari Alhamis aka yi dinner ɗin Raihan da Barista a Nihal Event center, wurin ba ƙaramin ƙayatuwa ya yi ba. Haka aka yi dinner aka tashi wannan karon su Inno ba su je ba, a cewarsu wurin zuwan yara ne ba na su ba. A haka aka tashi daga taro gwanin birge wa, don sun yi taro lafiya sun tashi lafiya kowa yana santin yanayin bikinsu.
Ranar Juma'a kamar yadda sanarwa ta gabata aka ɗaura auren Raihan da Barista Huzaifa akan sadaki dubu Ɗari, saboda tun kafin lokacin bikin Daddy ya nuna baya buƙatar kuɗin sadaki masu matsanancin yawa, ya fi buƙatar albarkar abin musamman da ya ga irin manyan akwatunan da Barista ya dire wa Raihan har saiti biyu. Wannan karon su Goggo har mai kiɗan ƙwarya suka ɗauko, haka mata suka cashe su kaɗai Raihan kuwa tana ɗaki tana tunanin lokacin bikinta Salim da irin shagulgulan da aka sha. Zuciyarta ce ta karye, a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi sashen Mommy kai tsaye ɗakinta ta nufa ta ci sa'a babu mutane da yawa tana shiga ta faɗa jikin mommy ta saka kuka. Mommy bata hana ta ba don ta lura tun da bikin Raihan ya matso take cikin damuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta: "Mommy tsoro nake ji kar wani abu ya faru an jima ba na son na rasa Barista ina ji..." Da sauri Mommy ta rufe mata baki haɗe da cewar, "Ki sawa zuciyarki kin yi aure ne na tsakani da Allah, don Salim ya rasu a daren aurenki bashi yake nuna Barista zai tafi ba." Mommy ta jima tana yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kimanin ƙarfe takwas saura motocin ɗaukan amarya suka kafa da'ira a ƙofar gidansu Raihan. Sai da aka yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan aka damƙata a hannun Goggo da Inno suka shiga mota da ita, kamar wancen karon sai da aka fara kai Raihan gidan Iyayen Barista sannan aka wuce da ita katafaren gidanta da ke unguwar Maidile, kasancewar Barista ya ɗauki hutun wata biyu don haka za su zauna Kano bayan sun cinye hutun su wuce garin Kaduna. Dr Hussain shi ne babban abokin ango duk wani shige da fice da shi ake yi, don haka baya zaune baya tsaye. Bayan an kai Raihan gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don ta gama saddaƙarwa jira take ta ji wani labarin daban. Tana nan zaune ita da su Safna ta ji muryar su Barista da abokansa suna yi masa tsiya irin ta abokan angwaye. Bayan sun shigo sai da aka yi siyan baki sannan su Dr Hussain suka ɗauki su Safna za su mayar da su gida. Barista Huzaifa har bakin gate ya raka su sai da ya ga fitarsu sannan ya tura ƙofar haɗe da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci ɗaya ya murtuke fuska sannan ya furta, "Alƙawari na ɗaukar wa kaina Raihan tawa ce ni kaɗai, ni ne mallakinta daga ni babu wani Namiji da zan lamunce ya mallaketa bayan ni. Ni Huzaifa duk wata hanya da zan bi na faɗa sai na bi ta don ganin na Mallaki matata." Huzaifa yana gama maganar ya wuce cikin gida wurin Raihan. Su Dr Hussain har sun fara tafiya Safna ta ce, "Kai! Dr wallahi na yi babbar mantuwa." Da mamaki ya tambaye ta nan take ta gaya masa wayarta ta manta a kan gadon Raihan. Dr Hussain magana ya yi wa sauran Abokan tafiyarsa da farko har sun ce ya je ya rakata su ɗauko, kasancewar dare ya fara yi ya ce su bari ya kira wayar Barista amma ɗif ya ji ta a kashe. Juya motar ya yi zuwa hanyar gidan Raihan amma duk yadda suka kai ga dube-duben su sun nemi gidan Raihan sama ko ƙasa sun rasa.
🤣 Ina masu cewa suna Allah-Allah Barista ya mutu🤣🤣🤣 To dai yanzu how market?🤣 Mu je zuwa Huzaifa kana wuta ina bin ka da fetir💃ðŸ¼
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624
36