Sashe 53
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannu a hankali kwanaki suka riƙa shuɗewa har aka yi sadakar bakwai ɗin Salim, Sai dai har a lokacin Raihan bata daina zubar hawaye akan mutuwar Salim ba. Ta rame sosai idan ka ganta sai ka rantse kwanciya ta yi matsananciyar jinya, hatta abinci sai da Mommy ta yi mata da gaske sannan Raihan take ɗaukan ruwan tea ta sha. Bata da aiki sai zaman ɗaki don kodayaushe tana ɗaki a kwance, sai dai idan mommy ta ji shirun ya yi yawa sai ta shiga ɗakin ta riƙa janta da hira don kore mata damuwa. Kamar kullin tana zaune a ɗaki ta idar da sallar Azahar tana zaune tana jan lazumi wayarta ta fara ringing. Kallon lambar take don bata san da ita ba, amma sai ta yi tunanin ko masu yi mata gaisuwa ne. Murya ba kuzari ta furta, "Salamu alaikum." Sautin muryar da ta ji an amsa mata ne ya sa ta sakin carbin hannunta, zumbur ta miƙe tsaye baki na rawa ta ce, "Don Allah kaine? Salim muryarka nake ji." Daga can ɓangare aka yi dariya kamar yadda salim yake ma'abocin fara'a sannan ya ce, "Kina mamaki ne Cutie ni ne man ko baki yarda ba." Jiki na rawa ta ciro wayar daga jikin kunnenta tana kallon lambar sannan ta fita da gudu tana ƙwala wa Mommy kira. A lokacin Mommy na kan dianning tana cin abinci jin kiran Raihan ya sa ta miƙe wa tana faɗin, "Lafiya Raihan?" Da sauri Raihan ta miƙa wa Mommy wayar ta ce, "Salim ne ya kira ni wallahi Mommy muryarsa na ji." Rass gaban Mommy ya faɗi, don ta san duk wanda ya mutu ya mutu har abada ba zai sake dawo wa ba, ganin har lokacin wayar na harbawa ba a katse ba ya sa mommy ta karɓi wayar jiki a sanyaye ta kanga a kunnenta. Kai wayar kunnenta ya yi daidai da ta ji muryarsa ta ce, "Cutie ba na jin ki sosai bari na sake kira." Gabanta ne ya sake tsinkewa ya faɗi sakamakon jin muryar Salim raɗau a dodon kunnenta, hannun Raihan har rawa yake ta fisgi wayar a hannun Mommy ta sake kira ta kara a kunne amma fir wayar ta ƙi shiga. Da sauri ta kalli mommy ta ce, "Don Allah mommy muryar wa kika ji idan ba Salim?" Hawaye ne ya fara zubo mata ta ci gaba da cewa, "Wallahi dama na faɗa muku Salim bai mutu ba Allah muryarsa ce." Lokaci ɗaya Raihan ta rikice wa Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Mommy daskare wa ta yi a wurin saboda ita kanta abin ya girmewa tunaninta. A jiyar zuciya ta sauke ta ja hannun Raihan zuwa Falo ta zaunar da ita, sai ta da kalli Raihan sannan ta ce: "Raihan ki kwantar da hankalinki. Na fahimce ki amma ki bari Daddynki ya dawo za mu yi magana da shi, tabbas ni ma muryar Salim na ji." Da sauri Raihan ta fara gyaɗa kai tana faɗin, "Mommy kin dai yadda da magana ta ko?" Mommy ta bi Raihan da kallon tausayi don ta kwantar da hankalinta ya sa Mommy ta gyaɗa mata kai haɗe da cewar, "Na yadda Raihan shi ya sa na ce ki kwantar da hankalinki." Inno da take gefe ta kalli Mommy ta riƙe haɓa ta ce, "Alkazzibu ƙarya dai haramun ne." Lokaci ɗaya Mommy da Raihan suka waigo wurin Inno, Inno ko a jikinta ta watsa musu harara ta ce, "Gaskiya Zainabu kin ba ni kunya. Yanzu saboda Allah ki zauna ki jirkice wa yarinya ƙarya, ta ina matacce yake iya dawowa? Ni kam ko lokacin da Alhaji Babba ya rasu na kusa shekara kullin sai na yi mafarkinsa amma ko kaɗan ban taɓa tunanin zai dawo ba." Raihan wani ƙululun baƙin ciki ya kamata ta dubi Inno a ƙufule ta ce, "Don Allah Inno ki fita a harkata, yanzu dai ban sa da ke ba." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Ko ki sa da ni ko karki sa da ni ke kika sani, amma ni da kika ganni babu abin da zai hana ni nema miki magani don na lura mutuwar yaron nan so take ta zautar da ke. Saboda Allah mutuwar miji bata da daɗi amma keda ma baku shaƙu ba, ko zaman dare fa baku yi ba ni da nake miki fatan nan da wasu ƴan watanni Allah ya kawo miki wani mijin ki yi aurenki." Raihan na jin haka ta fashe da kuka cikin ɓacin rai ta ce, "Wallahi ba zan sake aure ba kuma wallahi kika kawo min wani maganin sai na matse ki kin shanye shi tass." Mommy ta rufe mata baki cikin raɗa ta ce, "Don Allah ki daina biye maganganun tsofaffin nan kamar ba ki san halinsu ba?" Raihan ta share hawayenta tana shirin yin magana suka riski muryar Goggo tana faɗin, "A yau ba sai gobe ba dama na yi niyyar zuwa Albasu don na karɓo wa Yarinyar nan taimako, tsorona Allah tsorona kar yarinyar nan ta fara gane-gane na shiga uku." Shiru ne ya biyo baya mommy ta faɗa nazari don ita kanta ta fara zargin akwai lauje cikin naɗi, don babu tantama mutuwar Salim na son jefa Raihan cikin wani yanayi. Miƙe wa ta yi ita da Raihan suka wuce suka bar su Inno suna ta zancen su akan nema wa Raihan magani.
Da daddare bayan Daddy ya dawo yana tsaka da cin abinci ya dubi Mommy ya ce, "Mommyn Raihan na fahimci akwai abin da yake damunki tunanin me kike yi haka?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Daddyn Raihan ka gama cin abinci magana nake son mu yi." Ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya zuba mata ido a nan ya sake karantar irin damuwar da take ciki, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta saki murmushin yaƙe don ta san matuƙar ta sanar da shi abin da yake faruwa ya bar cin abincin kenan. Tana tsaka da tunani ta riski muryarsa na cewa, "Me yake faruwa Zainab?" Murmushi ta sake yi a karo na biyu ta ce, "Alƙwari na ɗauka sai ka kammala komai zan sanar da kai, kuma karka ɗaga hankalinka don ba wani abin damuwa ba ne." Daddy har lokacin kallon Mommy yake don kar ya yi mata musu sai kawai ya ci gaba da cin abincin ba don yana jin daɗinsa ba saboda yanayin da ya gani a tattare da ita. Bayan ya kammala cin abinci Mommy ta dube shi ta ce, "Daddyn Raihan! Don Allah Salim yana da ɗan uwa ne?" Da mamaki Daddy ya dube ta ya ce, "Kamar yaya ɗan uwa?" Mommy ta gyaɗa masa kai tana kallonsa. Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce, "A iya sanina Salim shi kaɗai ne namiji a wurin Mahaifinsa amma me ya sa kika yi wannan tambayar." Wayar Raihan da ke gefe ta ɗauko ta fara dubo lamabar da aka kira Raihan da ita ta miƙa masa ta ɗora da cewa, "Ɗazu wani ya kira Raihan a wayarta mai irin muryar Salim kai hatta irin kalaman da Salim yake mata sai da ya furta." Murmushi Daddy ya yi ya ajiye wayar Raihan ba tare da ya kalli lambar ya ce, "Haba Zainab na ɗauka ke za ki riƙa kwantar wa yarinyar nan hankalinta amma sai kike ƙara ɓullo hanyar da za ki tayar mata da hankali."
"Ba da wasa nake ba Daddyn Raihan saboda tun ina ƙarama na san mutuwa na san zafinta, duk wanda ya mutu ya tafi kenan har abada ba dawowa. Da kunne na ji abin da nake gaya maka ba Raihan ce ta sanar da ni ba, da ita ce kasan ba zan taɓa yadda ba." Da sauri Daddy ya ɗauki wayar Raihan ya ƙurawa lambar ido yana kallo, lokaci ɗaya ya danna kira amma fir taƙi shiga. Miƙe wa ya yi tsaye ya fara kaiwa da kawowa a dakin, Mommy ta ƙarasa wurinsa ta riƙo hannunsa sannan ta ce, "Ni ina ganin mai zai hana ka yi report wa ƴan sanda idan ya so sai su bibiyi layin don ganin wanda yake aikata haka." Lokaci ɗaya ya aminta da maganar Mommy har ya ciro waya zai kira D.P.O. abokinsa, sai kuma Malam Usman ya faɗo masa, don tun ranar da za a sallami Raihan ya ke sanar da su duk wani abu da za su gani na almara ko ɗaure kai su sanar da shi. Lambar Malam Usman ya kira ba a jima ba aka ɗauka, sai da Malam ya sake yi masa gaisuwar rashin Salim sannan Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa. Malam Usman jim ya yi sannan ya ce, "Tun bayan rasuwar yaron shin tana yin wasu abubuwa ko tana ganin wasu abubuwa na ban al'ajabi." Daddy ya yi shiru yana nazari sannan ya ce, "Eh to, tana yawan ce mana tana jin muryar Salim ya yi mata magana amma bayan haka babu wani abu da take gani ko ji sai yau da wannan kiran ya shigo cikin wayarta." Malam Usman ya ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji, insha Allah akwai magungunan da zan sake haɗa mata, amma duk da haka sai ta sake dage wa da Addu'a kuma a daina barinta a cikin kaɗaici ko ta riƙa keɓewa wuri ɗaya. Idan da hali a riƙa yawan zama da ita kuma tana yawaita sauraron karatun alƙur'ani." Daddy da Malam Usman sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama akan zuwa wayewar gari Daddy zai je ya amsowa Raihan maganunguna.