Sashe 92
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Jin hayaniya ta fara yawa ya sa Nurses suka taho wurin da sauri, suna ganin abubuwan da Kabiru yake yi da sauri suka kira security don ya fita da shi, amma bugu ɗaya Kabiru ya yi masa har sai da ya bugu da bango sannan ya faɗi ƙasa yana ƙwalla ƙara. Nan take suka fita da gudu suna kuruwa don lamarin ba ƙaramin tsoro ya ba su ba, Maryama ce ta farka daga bacci tana ƙarewa wurin kallo ganin Kabiru a tsaye ya sa ta saki murmushi ko da tana jin nauyin Inna wuro amma ta ji daɗin ganinsa don ta yi kewar mijinta. Inna wuro ce ta ƙarasa wurin Kabiru cikin kuka ta furta, "Ka dubi girman Allah Ibrahim ka yi haƙuri." Shiru Kabiru ya yi adaidai lokacin su Baffa suka ƙaraso cikin asibitin, tun ba su ƙarasa cikin ɗakin ba Inna wuro ta nufe su cikin tashin hankali cikin kuka tana faɗin, "Baffa ku zo ku gane min halin da yaron nan yake ciki, yana ganin jaririn Maryama shi kenan Ibrahima ya ziyarce shi." Da hanzari su Baffa suka ƙarasa gaban Kabiru Baffa ya dubi Kabiru sannan ya furta, "Ibrahim ka dubi girman Allah ka kama gabanka indai har yadda ka faɗa gaskiya ne Kabiru aboki kuma ɗan uwanka ne." Baffa ya dubi Inno wuro da ke sharɓar kuka sannan ya ci gaba da cewa, "Ka na ganin yadda mahaifiyar Kabiru take zubda ƙwallah shin jin daɗinka ne ko kuwa za ka so abin da zai musgana ran mahaifiyar amininka? Don Allah ka tashi mu wuce can gida amma a nan za ka tara mana jama'a ne." Kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayan su Baffa suka wuce gida. Tun da suka tafi uffan Kabiru bai sake tankawa ba don haka babu wanda zai kalli Kabiru ya yi tsammanin baya cikin hayyacinsa. A haka har Maryama ta shafe kwana uku tana karɓar kulawa daga wurin likitoci, a kwanansu na huɗu aka sallame ta ita da jaririnta. Sai dai tun ranar da Kabiru ya tafi gida har ranar da aka sallami Maryama uffan bai sake tanka musu ba, wannan lamarin ba ƙaramin sake ɗaga hankalin su Inna wuro ya yi ba don komai ka cewa Kabiru sai dai ya bika da ido. Sai dai ya ci abinci ya yi sallah ya shiga banɗaki amma babu wani abu da yake yi bayan wannan, don haka koda lokacin suna ya zagayo babu wani taro da aka yi kasancewar shi kansa jaririn ba lafiyayye bane ga kuma shi ma Kabiru halin da yake ciki Kullin cikin yi masa turare da jiƙe-jiƙen magunguna suke.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
47
Ibrahim Alƙasim Bn Muhammad Mustafa shi ne ainihin sunan aljanin da ke jikin Kabiru, asalin haɗuwarsu sun haɗu ne a tsangaya tun suna ƙanana. A lokacin da aka kai Kabiru karatu ne suka ƙulla abota da Ibrahim da ke ɗauke da siffar mutane don ko kaɗan babu wanda ya san Ibrahim ba mutum ba ne sai Malaminsu, dalilin da ya sa ta su ta zo ɗaya kasancewar kusan shekarunsu ɗaya, kuma lokacin da aka kai Kabiru almajiranci ya daɗe idan ya tuno su Inno wuro yana kuka. Idan yana kuka shi ma sai Ibrahim ya zo kusa da shi ya zauna ya fara kuka sakamakon tuno na shi mahaifan da ya yi. Haka za su zauna su ci gaba da koke-koke idan suka gama su share hawayensu su tafi yawon bara. Kamar yadda Baffajo yake ziyartar Kabiru shi ma haka Mahaifinsa yake kai masa ziyara bayan wani lokaci, a haka suka taso cikin soyayya da shaƙuwar junansu saboda duk inda aka ga Ibrahim za a ga Kabiru, a wannan rayuwar suka girma har suka yi saukar Alƙur'ani. A lokacin Kabiru na shekara ashirin daidai haka shi ma Ibrahim, tun da lokacin saukarsu ta ƙarato idan suka tuna lokacin rabuwa ya zo kowannensu yana jin babu daɗi hasali wani lokacin har ƙwalla Kabiru yake yi. Saura sati guda su Kabiru su tafi wata rana suna zaune suna hira Ibrahim ya dubi Kabiru ya ce, "Kabiru ga shi lokacin rabuwarmu ta zo amma daga ni har kai babu wanda ya san garin kowa." Cikin damuwa Kabiru ya ce, "Wallahi kuwa Ibrahim amma mai zai hana na fara zuwa garinku idan ya so in Baffa zai zo tafiya da ni ba sai ka bi mu ni ma ka gano ƙauyenmu ba." Ibrahim bai damu ba ya ce, "Shi kenan babu damuwa amma ba za ka ji tsoron mutanen garinmu ba kuwa?" Cikin halin ko'inkula Kabiru ya ce, "Sai ka ce wasu dodanni zan ji tsoronsu. Allah ya kaimu kawai mu tsayar da lokaci." Nan take suka tsayar da ranar tafiya sai dai tun da aka tsayar da lokacin tafiya Ibrahim yake cikin damuwa, fargabarsa ɗaya kada ya bayannawa Kabiru kansa ya zo ya guje shi a ɓangare ɗaya kuma yana tsoron kada ya kai shi duniyarsu wani abu ya faru Kabiru ya razana abotarsu ta zo ƙarshe duk da ya san babu wani abin cutarwa da ahalinsa za su yi masa. A haka har suka samu Malaminsu da maganar, da farko ya so ya hana su tafiyar amma a wani dare sai Ibrahim ya samu Malam ya roƙ shi akan ya bar shi su tafi. Ba don ya so ba ya amince musu Kabiru ya ɗebi kayansa kala biyu suka ɗauki hanya, sai da suka ɗan yi tafiya ta ƙasa mai nisa har sun fara shiga cikin daji Kabiru ya dubi Ibrahim ya ce, "Kai Abokina wannan wacce irin tafiya ce haka har yanzu ba mu zo tashar da za mu shigar motar garinku ba?" Ibrahim ya yi murmushi ya ce, "Kai ragon maza rufe idonka." Babu musu Kabiru ya rufe ido yana faɗin, "Ni da kai a samu ragon don ko makaho ya shafa ƙwanjinmu ya san da bambamci." Jin hayaniya ya sa Kabiru buɗe ido da sauri ya fara bin wurin da kallo tare da mutanen da ke wurin, Ibrahim ne ya riƙo hannun Kabiru ya ce, "Mun ƙaraso waɗannan mutanen garinmu ne ka ga ƙofar gidanmu can." Ya nuna masa wani katafaren gida mai siffa da na sarauta, daga bayansa ya ji wasu magidanta suna faɗin, "Abokin Ibrahim muna yi maka barka da zuwa." Kabiru ka sa amsawa ya yi ya dubi Ibrahim ya ce, "Ibrahim yaushe ka fara aiki da aljanu ban sani ba, wato duk gargaɗin da Malam yake yi mana akan laƙanin rufa ido baka ji ba kenan?" Dariya ce ta kama Ibrahim sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce, "Kai don Allah wuce mu je." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka Kabiru ya bi bayan Ibrahim har suka shiga cikin gidan, cike da girmamawa Mahaifiyar Ibrahim ta sauke su da abinci kala-kala. Har lokacin jikin Kabiru a ɗarare yake don haka Ibrahim da ya lura da yanayinsa ya riƙa jan sa da hira amma gabaɗaya ji yake wani iri. Yayar Ibrahim ce ta shiga gidan hannunta ɗauke da ƙaramin jariri, tana ganin Kabiru ta washe baki tana faɗin, "Ikon Allah, wannan fa shi ne karo na farko da bil'adam ya zo cikinmu gaskiya Ibrahim abotarka da Bil'adam ɗin nan ya matuƙar burge ni." A fusace Mahaifiyarsu Ibrahim ta dubi Yahanasu ta ce, "Wai me ya sa wani lokacin baki da tunani Yahanasu kamar ba ki ji kashedin da Malam ya gama yi ba jiya ko?" Daga bakin ƙofa Kabiru ya hango yadda yara da manya suke leƙensa don haka ya sake shan jinin jikinsa, ya dubi Ibrahim a tsorace ya ce: "Don Allah kar ka cutar da ni Ibrahim domin a zamantakewata da kai ban taɓa zalintarka ba, idan ma na yi sai dai wataƙila lokacin da muna cikin ƙuruciya." Dafe kai Ibrahim ya yi jiki a sanyaye don ya fahimci Kabiru ya gano shi ya ce, "Ba zan taɓa cutar da kai ba Kabiru domin jin ka nake har cikin zuciyata saboda Baffajo bai taɓa bambamta mu ba duk abin da zai kawo maka sai ya kawo min, kuma zaman da muka yi na amana ne babu zalinci a tsakaninmu." Ganin hankalin Kabiru ya tashi ya sa Ibrahim ya saka shi sake runtse ido, muryar malaminsu ce ta farkar da shi yana buɗe ido ya gan shi zaune a shagon Malam. Malam ya kalli Kabiru ya yi murmushi ya ce, "Dama abin da na yi gudu kenan amma gudun kar ku yi min mummunar fahimta ya sa na amince da tafiyarku. Ibrahim ba mutum ba ne kamar yadda ka yi tsammani, tun kafin zuwanka Mahaifinsa ya kawo shi karatu wurina saboda Mahaifinsa abokina ne mun haɗu da shi ne a wani aikin Hajji da na je. Ka kwantar da hankalinka Ibrahim da zuri'arsa ba za su taɓa cutar da kai ba domin su cikakkun musulmai masu kyawawan ɗabi'a ne, sai dai ka yi haƙuri don na tabbata ba lallai ka sake ganin Ibrahim a nan tsagayata ba sai dai wataƙila idan ka koma rugarku." Kabiru cikin damuwa ya furta, "Amma har yanzu tsoro nake ji, zuciyata ta gaza aminta da Ibrahim na jinsina ba ne Malam." Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ka ji tsoron Allah Kabiru domin shi zai isar maka, babu abin da mutum ko wani jinsi zai yi maka wanda Allah bai ƙaddara ba, ka yarda da maganata Ibrahim da zuri'arsa ba za su cutar da kai ba." Jinjina kai Kabiru ya yi ya miƙe ya ci gaba da harkokinsa sai dai gabaɗaya ji yake babu daɗi kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa, don a daren ranar da ya je kwanciya ya kalli wurin kwanciyar Ibrahim sai kawai ya fashe da kuka, haka ya ci gaba da rayuwa cikin kaɗaici da damuwa har ranar da Baffajo ya zo ɗaukansa a nan Malam yake sanar masa da komai game da Ibrahim, bai gama amincewa da maganarsa ba sai da Malam ya kira Mahaifin Ibrahim da Ibrahim suka bayyana a wurin suka gaisa cikin mutumtawa sannan suka sake ɓace wa. Shi kansa Baffajo ya yi mamaki da wannan lamarin, daga haka ya yi wa Malam alheri da godiya mai yawa sannan ya ɗauki Kabiru suka tafi daga Malam har Kabiru kowannensu yana zubda ƙwallah. Wannan dalilin ne ya saka lokaci zuwa lokaci a duk lokacin da Kabiru ya shiga wani yanayi yake kawo masa ziyara ba tare da ya fahimci shi ba ne, don ko kaɗan baya son ya razana abokinsa don haka a duk lokacin da ya ziyarce shi baya taɓa bari ya ga fuskarsa. Lokacin da lamarim gidansu Raihan ya same shi a lokacin Mahaifiyarsa ce babu lafiya a gaggauce ta tafi birnin ƙudus don ɗebo mata wata ciyawa wacce take tsakiyar tekun Milabi, don yi mata magani. Shi ya sa bai nemi karawa da Huzaifa ba, a ɓangare ɗaya kuma yana ganin duk abin da yake faruwa akan lamuran Raihan sai ya yi kamar ya shiga sai wani uzurin ya faɗo masa.