Sashe 70
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin babu wanda ya waigo balle ya nuna alamun ya ji kiranta ya sa ta cire takalminta ta jefa a saitin wurin da Mama Hafsat take tsaye haɗe ta ƙwala mata kira, amma ko alamin juyo wa Mama Hafsa bata yi ba. Huzaifa yana daga wurin da yake tsugunne ya saki murmushi haɗe da cewa, "Da ma kin bar wahalar da kan ki domin babu wanda zai ji ki balle ya waiwayo gare ki, saboda wurin nan da kike yana da kamceceniya da dajin ƙare kukanka." A wurin Raihan ta durƙushe tana zubda hawaye mai zafi, Huzaifa yana son ƙarasawa wurinta amma wani irin turiri yake ji a duk lokacin da ya kusanceta. Takawa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce, "Kina da buƙatar abinci ne?" Cikin kuka Raihan ta girgiza masa kai haɗe da cewa, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena." Guntun tsaki Huzaifa ya yi ya juya a fusace yana faɗin, "Idan na mayar da ke tabbas na san ta kowanne hali sai sun raba ni da ke ko kuma su hallaka ni, wallahi da na mayar da ke gara na hallaka ki kowa ma ya huta." Yana gama maganar ya fice daga wurin, jin maganar Huzaifa ta ƙara hargitsa tunaninsa cikin tashin hankali ta furta, "Innalillahi wa'inna'ilahirraji'un." Jin tashin motar su Mama Hafsa ya sa Raihan ta sake leƙa wa ta windo sai kawai ta kifa kanta ta wurin tana zubda ƙwallah. Raihan haka ta ci gaba da zama a wurin tana zuba wa sarautar Allah ido, don duk abin da yake faruwa a harabar wurin tana kallo har waɗansu yara ta gani masu buhu a hannu suna tsince-tsince a wurin gidan nata amma kiran duniya ta yi musu babu wanda ya amsa mata. Ta jima a wannan yanayin kamar almara bayan wani lokaci ta ji muryar Daddy, wannan karon a haukace ta ƙwallah ƙara haɗe da bubbuga ƙauren windon amma ko kaɗan Daddy bai ji ba. Tana ji tana gani Daddy ya ja motarsa ya bar wurin, wannan karon zama ta yi a wurin daɓas don tuni hawaye ya ƙauracewa idonta ta ji gara ma mutuwarta da rayuwarta.
Damuwa goma da ashirin ce ta mamaye zuciyar Daddy, ban da zarya a cikin asibitin babu abin da yake yi. sauƙin da ya ji da likitoci suka samu damar ceto rayuwar Mommy, amma sun sake jadadda masa zuciyarta tana barazanar bugawa. A ranar tawagar D.P.O suka ƙarasa unguwar su Huzaifa suka kwashe iyayensa domin zargi ƙururu ake yi akan Huzaifa na ɓatan Raihan. Duk ciwon da Raihan take da shi sai da Daddy ya zayyana wa D.P.O tas sannan ya bashi labarin yadda aka yi Dr Hussain ya rako Huzaifa har cikin gidansa, nan take zancen ɓatan Raihan da Huzaifa ya watsu a cikin garin Kano da sauran garuruwa daga ƙasar Nigeria. A wannan karon duk yadda ƴan jarida suka so jin ta bakin su Daddy abin ya ci tura, don haka suka dangana ga wurin ƴan sanda a nan suka samu bayanin da ba a rasa ba. Wannan tashin hankali da aka wayi gari ya sa ƴan bikin da suka ziyarci gidajen bukukuwan tuni kowanne ya kama gabansa zuciya a dagule, maganar ɓatan su Raihan ita ta kai har kunnen ƙungiyoyin lauyoyi ta ƙasa. Babu shiri suka tuntuɓi hukumar ƴan sanda haɗe da neman a haɗa su da iyayen Raihan don jin duk yadda abin ya kasance. Kamar yadda abin ya faru haka Daddy ya sanar da su iya abin da ya sani, daga ƙarshe ɓangarorin biyun suka ci alwashin binciko duk wurin da Raihan da Huzaifa suke. Tuni Hotunan su Raihan ya karaɗe kafofin sada zumunta lamarin da ya sake hautsina labarin kowa da abin da yake faɗa, wasu su ce aljanun Raihan kashe mazanta suke yi, wasu su ce su suka sace Raihan har ma su zargin tuni an gama da Huzaifa sai jiran bayyanar Raihan. Lokacin da Dr Hussain ya tabbatar da ɓatan Raihan ya shiga banɗaki ya fi a irga don ko a radio ya ji maganarta sai cikinsa ya karta ya faɗa banɗaki, daga ƙarshe Daddy ya bayar da umarnin a tafi da Dr Hussain shi ma. Har kawo wannan lokacin Iyayen Huzaifa na kulle ba a sake su ba, sai da aka kai ruwa rana sannan Daddy ya lamunce aka saki iyayen Huzaifa da sharaɗin a kowanne lokaci za a iya buƙatarsu don bayar da bayani.
BAYAN KWANA BIYAR.
Duk waɗannan kwanakin mutanen gidansu Huzaifa da Daddy sun yi su cikin rashin nutsuwa, fargaba da tashin hankali. Su Inno ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, ko abincin kirki ba sa iya ci. Kabiru tuni ya fige ya rame ya lalace don ko abinci bai fi ya yi cokali biyu ya ajiye shi ba, ba shi da aiki sai addu'a da sallar dare yana fatan Allah ya kuɓuto da Raihan cikin ƙoshin lafiya. Daddy tuni ya sanarwa da Malam halin fa ake ciki, ya bi makarantun islamiyyu da ta allo ya riƙa rarraba kuɗi yana neman a yi wa Raihan addu'a akan Allah ya bayyanata cikin alheri ko a mace ko a raye. Jikin Mommy yana sauki amma sai dai a kira shi da samun sauƙin mai haƙan rijiya, don kullin tana kwance ana bata kulawar da ta dace amma kullin ta farfaɗo maganarta ɗaya, "Ina Raihan?" Da ta kalli Daddy sai dai ta riƙa zubda ƙwalla. Ana cikin wannan yanayin Inna wuro ta kira Kabiru hankalina tashe tare da sanar da shi ciwon Baffajo ya tashi, wani sabon tashin hankalin ne ya dirarwa Kabiru don haka a ranar da Raihan ta kwana shida da ɓata, ya shirya da safe zuwa asibitin da Mommy take ya sanarwa da Daddy duk abin da yake faruwa, tare da faɗin zai je ya gano halin da yake ciki. Duk da Daddy na cikin damuwa bai hana ya gano tsananin damuwar da Kabiri yake ciki ba, kuɗi ya tura masa masu yawa ta Account ɗinsa. Kuka Kabiru ya gashe da shi har ƙasa ya tsugunna yana yi wa Daddy godiya. Daga asibitin gida Kabiru ya koma ya yi wa su Inno Sallama ya ɗauki ƙaramar jakarsa ya fita. Lokacin da ya fice daga gidan zuciyarsa ce ta karye game da lamarin Raihan, zuciyarsa ta fara tunane-tunane akanta don haka idanunsa suka ciko da ƙwalla ya sake waigawa ya kalli gidan sannan ya goge ƙwallar idonsa ya fara tafiya.
"Tabbas na sake lamincewa Huzaifa ya dawo da ƙarfinsa fiye da na baya, ina da yaƙinin ya samu taimako ne daga Kakansa Jabbul-ƙasi. Idan ba haka ba babu yadda za a yi ace Huzaifa shi kaɗai ya dagakatar da dukkan tsafi da sihirinmu. Ya auri Raihan ba tare da mun iya dakatar da shi ba, jikina ya gama ba ni ya fara fahimtar wani abu daga gare mu domin babu yadda za a yi Mugaza tana ji tana gani ta bari Huzaifa ya auri Raihan ba tare da wani abu ya gifta a tsakani ba. Ku shaida ne yau kusan watannin Mugaza huɗu kenan ba tare da ta halarci ƙungiya ba, kuma duk iya bincikenmu mun yi don ganin mun gano halin da take abin ya ci tura, shin me kuke tunani meye abin yi a wurinmu?" Abar bauta ta yi maganar a sanyaye saboda ta gama tsinke wa da lamarin Huzaifa. Hatsabibiya ta rungumo mijinta tamkar wani zai ƙwace shi tana shirin magana, ya miƙe zumbur ya fara sauya launi sai da ya rikiɗa zuwa kaloli kusan biyar sannan ya tsaya cikin kalar yello da baƙi. Kallon abar bauta ya yi ya numfasa sannan ya ce, "Yau kusan shekarata bakwai ban tofa muku komai a game da lamarin ƙungiya ba, ina buƙatar a bani damar na furta wani ba." Da yake Abar bauta mafita take nema don haka cikin sauri ta amsa masa, "Faɗi koma meye a bakinka." Mijin Hatsabibiya can gefenta ya koma ya maƙale matarsa sannan ya ce, "A wannan halin da ake ciki Huzaifa ya gawurta, tasirin tsafi da sihiri ba za taɓa aiki a kansa ba. Laƙanin Jabbul-ƙasi yana da matuƙar ƙarfi. A shawarce duk yadda ake ciki kar mu sake mu tunkari Huzaifa gaba da gaba. Kar ma mu jefa rayuwarmu cikin tashi domin matuƙar ya fahimci muna mu'amala da Raihan a cikin ƙungiya ta mu ta zo ƙarshe, don haka sai mun yi takatsantsan koda za mu cimma burinmu akansa. Sannan dole mu tabbatar da mun ceto Mugaza a kowanne yanayi take ciki idan ba haka a kowanne lokaci asirinmu zai iya tonuwa." Abar bauta ta jinjina kai cike da gamsuwa don bayaninsa ba ƙaramin ankarar da ita ya yi ba. Miƙe wa ta yi tana kai wa da kowo wa sannan ta dube shi ta ce, "Yanzu ta ina za mu fara?" Kai tsaye ta ji ya furta, "Dole mu ziyarci tsibirin Jabbul-ƙasi mu nemi agajinsa." A haukace duka suka kalle shi cikin hargitsattsiyar tsawa Abar bauta ta ce, "Kana hauka ne za ka ce mu ziyarci Kakan Huzaifa don mu nemo sa'a?" Murmushi ya yi sannan ya ce, "Na san waye Jabbul-ƙasi ba ruwansa da duba nasaba ko dangantaka. A yadda muka je da buƙata to buƙatar kawai zai kalla babu ruwansa da wanda za a aikatawa." Daɓass! Abar bauta ta zauna jiki a sanyaye zuciyarta na yi mata wasu-wasi akan ta amince da maganarsa ko ta yi watsi da ita. Tashi ta sake yi za ta shige raminta sannan ta waigo ta ce, "Ku dakace ni don na yi nazarin abin da ya kamata mu yi don gaskiya zuciyata na rawa akan wannan shawarar taka." Tana gama maganar ta shige ciki.