← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 110

Sashe 42

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubuwa da dama sun faru ciki har da mutuwar iyayen waÉ—annan bayin Allah, wato Goggo da Malam Bala Magini. Abubakar ya fara bin wani yayan Goggo suna tafiya Lagas suna sayar da kayan gwari, a lokacin Mommy ta zama budurwa tana da shekara goma sha shida a duniya. A wannan lokacin tana aji biyu na babbar sakandire sakamakon Mahaifinta bai bi sunnar Mahaifinsa ba, don ya ci burin yadda bai yi karatun boko ba Æ´aÆ´ansa ba za su taso haka ba. Dukda ya tsaya musu tsayin daka akan karatun addini, Abubakar sai da ya yi diploma sannan ya fara tafiya neman kuÉ—i. Ita kuwa mommy a lokacin da take aji biyu na sakandire ne wata rana ta fita É—iban ruwa ta haÉ—u da Daddy sun shigo garin Albasu don siyan wata gona su mayar da ita kamfani, HaÉ—uwar Mommy da Daddy babu jimawa Allah ya yi wa Malam Bala Magini rasuwa, bayan wani lokaci da rasuwarsa Daddy ya tura Æ´an uwan Mahaifinsa don a nema masa aure. Da farko Goggo ta so dakatar da maganar a cewarta bai kamata a katse wa Mommy karatu ba alhalin ta kusa candy, amma da Daddy ya nuna ba zai hanata karatu ba ya sa Goggo ta amince. Sai dai a É—aÉ—É—are take da su Daddy musamman ta da ga irin galla-gallan motocin da suke shigo wa da su cikin garin albasu.

Bayan auren Daddy da mommy ko shekara biyu ba su yi ba ya ɗauko Goggo ya dawo da ita gidan da ya sayawa Inno, saboda tun bayan bikin Mommy zaman garin ya gaza yi mata daɗi. Ga Abubakar yana nesa ga ba miji ita ma Mommy da suke kashewa su binne an yi mata aure, ga ƴan uwan Goggo da suke Uba ɗaya sun saka ta a gaba wai ta ga kuɗi ta sayar da ƴarta saboda zalama. Ɗaukan da Daddy ya yi wa Goggo ba ƙaramin daɗi ya yi wa mommy ba a lokacin Hafsa ita ma ta fara zama budurwa, daga ci da sha har karatun Hafsa Daddy ne yake ɗaukar nauyi. Daga baya da ya kammala gidansa wanda ya fi wanda suke ciki girma, sai ya kwashe su gabaɗaya ya mayar da su kusa da shi. Mommy da Daddy sai da suka shafe shekara sama da goma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, sun yi wayon asibitoci gari-gari ƙasa-ƙasa amma duk wurin da suka je sai dai ace lafiyarsu ƙalau. Da yake Daddy sam bai yarda da maganin gargajiya ba shi ya sa ko na hausa bai yarda sun nema ba, tun suna damuwa har suka fauwalawa Allah lamuransu. Inno ta so Daddy ya ƙara aure amma da yake ta lura bashi da ra'ayi sai ta kawo ido ta saka masa, kuma da yake Mommy na matuƙar basu kulawa tana haƙuri da su ya sa take jin daɗin zama da ita. Don shi kansa Daddy wani lokacin idan suna rikici abin ɓata masa rai yake, sai a sannu da Mommy take nusar da shi wani abin da suke yi har da yanayin tsufa sai Daddy yake zura musu ido.

Bayan sun fitar da rai da samun haihuwa kwatsam wata rana mommy ta wayi gari da matsanancin zazzaɓi da ciwon ƙirji, da yake tana da olsa ko da ta je asibiti abin da ta cewa likita kenan. Suna bata tasa-tasai ciki ya bayyana, nan fa suka shiga murna da farinciki su Inno baki ya ƙi rufuwa. Daddy da kansa ya shige musu gaba suka fita ƙasashen waje don siyayyyar kayan jarirai. Bayan wata tara mommy ta haifo kyakkyawar ƴarta mace, tun a ranar Daddy ya saka mata suna Raihan. Haka ya ƙwallafa rai a kanta ko ƙuda baya son taɓa ta, soyayyar duniya ya ɗora mata duk abin da zai saka ta kuka baya so don wani lokacin har faɗa suke yi da Mommy akanta. Haka suka ci gaba da rayuwa da har Raihan ta fara girma kyau da wayonta ya sake fito.

Lokacin da Raihan tana da shekara biyar a duniya, kwatsam watarana sun fita shan Ice-cream suna hanyar dawowa ta hango wata agwagwa a bakin wani kanti da Daddy ya yi parking zai sayi kayan provision, murfin ƙofar ta buɗe da sauri tana fita ta tunkari agwagwar ta ruƙota da hannu biyu, a daidai lokacin Daddy ya fito daga shagon. Murmushi ya yi don ya yi tsammanin agwagwar birge Raihan ta yi, daga wurin da yake ya furta: "My love kina son na saya miki ne..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta ɗago agwagwar ta damƙe fuka-fukanya ta da hannu sosai sannan ta talata da ƙarfi lokaci ɗaya fuka-fukan agwagwar suka fita daga jikinta, suka tsintsinke gabaɗaya. A haukace ta juyo wurin Daddy cikin ƙaraji tana faɗin, "Ita ta cin ye min Ɗana shi ya sa nima ba kasheta." Ilahirin mutanen da ke wurin sakin baki suka yi a tsorace suna kallon ikon Allah, don wannan abin da Raihan ta yi ba su taɓa ganin irinsa ba. Nan take wasu suka dasa mata ayar tambaya suna ganin kamar mayyace maitarta ce ta fito fili.

Littafin kuɗi ne Idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624

22

Daddy kusan suman tsaye ya yi jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa wurin Raihan yana fisgo hannunta ya ce, "Ke Raihan me kike yi haka?" Idanunta jajawur ta ɗago tana kallonsa cikin wata irin ta ce, "Duk wanda ya hallaka min ɗana sai na yi masa abin da ya fi haka." Da sauri Daddy ya waiga yana kallon mutanen da ke zagaye da su, ya yi ƙasa da murya a daidai kan Raihan ya ce, "To zo mu je gida duk abin da kike so ta zauna." Yana rufe bakinsa ya kai hannu zai riƙota ta fisge, ba tare da ta kula shi ba ta wuce ta buɗe murfin mota ta shiga. Cike da kunya Daddy ya kalli mai kanti yana faɗin, "Don Allah wa kuka sani mai agwagwar nan?" Mai kanta ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya Alhaji ba na ce ga mai ita ba tun da muma a inda ka ganta mu ma a nan muke ganinta." Daddy ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa musu ya ce, "Gashi nan sadakar kuɗin agwagwar ne." A ɗaɗɗare mutanen wurin suka karɓa don ganin abin da Raihan ta yi ya dasa musu shakku a zuciya. Lokacin da Daddy ya shiga mota Raihan na zaune ta kifa kanta a tsakankanin cinyoyinta, kai tsaye daga nan wurin asibiti ya wuce da ita. Bayan ya gama yi wa Likita bayani allurar bacci suka samu suka yi mata da ƙyar don fisge-fisge da bige-bige take yi har sai da ta kai wa Daddy cizo a hannu fatar wurin ta kwaile. Mommy na gida lokacin Daddy ya sanar da ita abin da yake faruwa, hankali a tashe ta tafi asibitin ba tare da ta sanar wa su Inno takamaiman abin da ya faru ba. Bayan ta farka daga bacci garau ta yi kamar ba ita ba, ba a ɗauki lokaci ba likita ya sallame su. Haka suka ci gaba da rayuwa tun Raihan na yin abin sama-sama har ya fara bin jikinta, tun da ta haɗu da wannan larurar babu damar Daddy ya siyo kifi cikin gidan ko wuce wa suka je ta wurin da ake suyar kifi take haukace musu ta yi ta neme-neme tana cewa wani ya sace mata ɗanta zai hallaka shi. Idan kuwa ɗanyan kifi ta ci karo da shi babu wanda ya isa ya ƙwace daga hannunta. Rungume shi take yi ta ƙwaƙume shi tana sunbatarsa haɗe da yi mata wasa kamar yadda babar mace take yi wa ɗanta ko ƴarta.

Duk wanda ya tunkareta a lokacin da take riƙe da wannan kifin cikin biyu za a yi ɗaya, inma ta illata shi da yaƙushi ko kuma ta kafa masa haƙora har sai an kwace shi da kyar. Wannan lamari ba ƙaramin saka su Mommy ya yi a uku ba, duk farincikin da suke ciki ya dakushe kullin cikin fargabar wannan ciwon nata suke yi, kuma idan ciwon nata bai tashi ba sai ta yi ta sabgoginta kamar yadda sauran yara suke yi.Wannan dalilin ya su Inno suka fara ɗari-ɗari da ita, akwai ranar da ciwon ta ya tashi ranar mommy ta je shopping wani store a lokacin daga Goggo sai Inno a gidan, Inno na tafe ta hango Raihan a tsaye ta ƙurawa kusurwar bango ido tana murmushi Inno ta ja guntun tsaki ta ce, "Ƙarfi da yaji Audullahi ya koma bayahude, yanzu saboda Allah yarinyar nan ko makaho ya shafata ai ya san ba ita kaɗai ba ce." Goggo da ƙarasowarta kenan wurin ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi don kar na faɗa Abu ta ji haushi na shi ya sa na yi shiru, ki dubi yarinyar kamar jikar ifiritu yau da lafiya gobe ta hau cije-cije ni tun da na yi rayuwa a Albasu ko mai kwantankwacin wannan ciwon ban gani ba." Mama Uwani ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da mopper ta ce, "Gafaranku dai." Cikin haɗin baki suka amsa mata, jin yadda suke yi wa Raihan ya sa ta ce, "Yanzu dai Inno tun da ba wani abu kuka ga ta yi ba don Allah ku sararawa Uwar ɗakina haka." Rufe bakin Mama Uwani ya sa Raihan ɗagowa ta kalle su da jajayen idonta, Inno na ganin haka fara salati tana ƙoƙarin jan ƙafarta zuwa ɗaki. Kamar tsuntauwa haka Raihan ta dira a gaban Mama Uwani ta fisgi mofar hannunta ta fara bin su Inno tama raɗa musu sandar mofar a baya. Ganin Raihan ta tasamma nakasa su ya sa ba shiri suka neman tsira da rarrafe suka fita gate, a lokacin Marigayi Ado mai gadi yana nan, yana zaune yana jin rediyo ya hango su Inno sun tunkaro shi da rarrafe. Da sauri ya nufi wurin yana son kora Raihan gida ta yo kansa gadan-gadan, tana faɗawa Ado su Inno suka samu nasarar bankawa ɗakinsa. Sufa Raihan ta yi ta fisgo ƙafar Goggo ɗaya ta Inno ɗaya ta fara saka baki tana gantsara musu cizo, Mama Uwani ce ta zo ta janye Raiham daga wurin su Inno ban da kuka babu abin da suke yi, Goggo kuwa saboda ruɗewa ta yi fitsari ya kai uku a wurin.
Chapter 42 · 0% Book details