← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 110

Sashe 87

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Gabanta ne ya ci gaba da faɗuwa jin Al'amin na ƙoƙarin shigarta, ƙwace kanta ta shiga ƙoƙarin yi don yadda fargaba ta mamaye zuciyarta gani take kamar yadda Huzaifa ya yaudareta da siffar bil'adam haka Al'amin zai yi mata, cikin fitar hayyaci ya sake janyota jikinta a hankali ya furta, "Shiiiii." Shiru Raihan ta yi ta saka hannu tana shafa fuskarsa sannan ta ce, "Don Allah Al'amin kai ne dai?" Idonsa a lumshe ya gyaɗa mata kai Raihan na shirin sake magana suka ji an fara buga ƙofa da ƙarfi, muryar Sumayya ce take ihu haɗe ta ƙwala masa kira tana cewa, "Habibi ka taho maciji da kunama za su kashe ni." Hankali a tashi Al'amin ya miƙe ya janyo jallabiyyarsa ya saka. Raihan na daga kwance ta ɗauko zaninta ta ɗaura sannan ta saka hijabinta. Al'amin na buɗe ƙofa Sumayya ta maƙale shi jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi, ƙofar ɗakinta take nuna masa bakinta na rawa ta ce. "Wallahi suna ciki." Janyeta bayansa ya yi ya mayar da ita wurin ƙofar ɗakin Raihan, a hankali ya fara takawa har ya ƙarasa ƙofar ɗakin yana maimaita addu'a a bakinsa. Yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ga mamakinsa wata irin tafkekiyar kunama ya gani kwance a tsakiyar gadon Sumayya, tun da ya zo duniya ko a labari bai taɓa ji labarin makamanciyar wannan kunamar ba. Haka kawai ya ji tsigar jikinsa ta tashi yaarrr! Idanu ya lumshe ya buɗe yana sake ƙurawa kunamar ido, motsi ya ji daga gefen madubi yana kai idonsa ya hango wani baƙin maciji jikinsa baƙi siɗik har sheƙi yake. Tsalle macijin ya yi ya haye kusa da kunawar yana zagayeta tuni ta maƙale jikinsa tana wani irin zagaye a doron bayansa, tsoro ne ya fara kama Al'amin don haka ya ci gaba da karanto ayayon kariya yana tunkarar macijin, yana kusantarsu suka fara nufar hanyar windon Sumayya da yake a buɗe. Da sauri suka ɗare suka fice daga ɗakin, Al'amin sai da ya lalleƙe ko ina sannan ya zuge windon ya rufe shi ruf. Ƙofar ya rufe ya zagaya ta bayan gidan don ganin wurin da macijin ya yi amma babu shi babu alamarsa, duk iya dube-dubensa babu abin da ya gani don haka ya janyo ƙofar ya rufeta ruf sannan ya dawo wurin su Raihan, a daidai lokacin Sumayya ta dafe mara tana ihu haɗe da faɗin, "Wash marata Al'amin." Da sauri ya kamata yana faɗin, "Lafiya Sumayya?" Bai rufe baki ba ya ga jini na bin ƙafarta, ƙirjinsa ne ya buga hankali a tashe ya furta, "Me ye wannan sumayya?" Ganin jini ya sake hartsiga Sumayya ta sake ruɗewa, Raihan ya kalla yana faɗin, "Ɗauko mata hijabi mu tafi asibiti." Jiki na rawa Raihan ta koma ɗakinta ta sako doguwar rigar bacci ta saka hijabi ta ɗauko wa Sumayya hijabinta ta fita, a gaggauce Al'amin ya saka mata ya ɗauke ta cak saboda yadda ciwon mara ya murɗeta suka wuce asibiti, asibitin ba shi da nisa da gidansu don haka ba su jima ba suka ƙarasa. Cikin gaggauwa likitoci suka karɓeta suka shiga bata agajin gaggawa, duk yadda suka so ceto abin cikin sumayya sai da ta yi ɓarinsa. Ta sha wahala sosai don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ta ji jiki, Raihan ta yi jigum don ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba. Kimanin ƙarfe ɗaya na dare aka samu jikin Sumayya ya yi sauki saboda fitar cikin jikinta, allurar bacci suka yi mata sannan Al'amin ta ɗauki Raihan suka wuce gida don ɗauko duk abin da ya kamata su buƙata. Daga Raihan har Al'amin babu wanda ya tankawa ɗan'uwansa sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci kowannensu yana cikin tashin hankali. A gaggauce suka ɗauki abin da za su ɗauka suka koma asibitin sai dai har lokacin bacci Sumayya take yi, daga Al'amin har Raiban a zaune suka kwana kowane na yin gyangyaɗi. Tun asuba Sumayya ta farka Raihan ce ta taimaka mata ta gyara jikinta, duk kayan jinin da ya ɓaci Raihan ce ta wanke su tas ta gyara wurin sannan ta haɗa wa Sumayya ruwan tea, tun da sumayya ta farka take aika mata da harara tun Raihan bata lura da irin kallon da Sumayya take yi mata ba har ta ankara ta sha jinin jikinta.Tun da suka tashi Raihan take yi mata sannu amma ko sau ɗaya bata amsa mata, ban da yauƙi da shagwaɓa babu abin da take yi wa Al'amin. Kimanin ƙarfe takwas na safe Mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka shiga cikin asibitin, Mami na shiga Sumayya ta fashe da kuka tamkar a lokacin ne ta yi ɓarin cikin.A wulaƙance suka riƙa kallon Raihan suna yamutsa fuska, Al'amin na gaida su ya fice daga wurin. Cikin girmamawa Raihan ta gaida ita tana yunƙurin tashi Mami ta ce, "Yo dama tun da na ji an ce wai kin ga maciji a ɗakinki ai nasan ture ne aka yi miki, ana baƙinciki kin samu ciki ba gara a ɓarar da shi ba. Ai duk makircin mutum ya ƙare akansa don ba a taɓa canjawa tuwo suna kece dai Uwargida wacce kike zaune ɗaram a zuciyar Al'amin amma su shigege sai dai a yi ta cusa kai babu kwarjini to laƙadija'akum tsakaninta da ke, dama ba ance aljani ya aureta har ya taɓa tserewa da ita ba, ni babban tashin hankalina ma kar haukan jikinta ya tashi watarana ta shaƙe min ke a gida ta kashe ki, ta cuce ni tun da ba a shari'a da mahaukaci." Ƙwalla Raihan ta ji na niyyar zubo mata a hankali ta nufi ƙofa ta fice don idan ta ci gaba da jin kalamanta za ta iya gaya mata mara daɗi. Tana fita ta kira Mommy ta sanar da ita abin da ya faru da Sumayya daga ƙarshe Mommy ta ce tana nan tafe da yamma, suna gama waya Ammi da ƙannen Al'amin suka ƙaraso cikin asibitin. Da gimamawa Raihan ta gaida Mami suma ƙannen Al'amin suka gaishe ta ba yabo babu fallasa, sannan suka wuce cikin ɗakin da Raihan take, da yake Malam baya gari sai a waya ya duba Sumayya. Bayan fitar Raihan daga ɗakin Mami ce ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi sai mun yi da gaske akan yarinyar nan idan ba haka ba na lura haramta miki zaman cikin gidan za ta yi, a yau ba sai gobe ba zan tafi na amso miki alƙwarin da muka yi da ke. Da zazzaɓi nake fama da shi amma ko ma meye dole na shirya na je don wallahi yarinyar nan dole ta bar miki gidan nan." Daɗi ne ya kama Sumayya ta sake rungume Mami tana faɗin, "Shi ya sa nake ji da ke Mommcy." Shigar su Ammi ya daidaita nutsuwar Sumayya ta sake narkewa tamkar wani azababben ciwo na damunta. Ammi na zama bayan sun gaisa ta fara tambayar Sumayya yadda lamarin ya kasance, Sumayya ta sauya fuska cikin damuwa tana cewa, "Wallahi mommy ina cikin bacci na ji kamar an kira sunana, ina tashi na ga babu kowa sai na koma na kwanta. Ban yi aune ba sai ji na yi abu mai ƙayoyi yana bin jikinta, ina buɗe ido na ga wata irin murtukekiyar kunawa ga maciji a gefen cikina a kwance shi ne na tafi ina ƙwalawa Al'amin kira. Daga haka kawai jini ya ɓalle min, wallahi ni dai Ammi na san lafiyata ƙalau ko ciwon kai ba na yi sai da abin nan ya faru gashi yanzu Likitoci sun ce cikin ya zube." Sumayya ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, lallashinta mutanen ɗakin suka riƙa yi sai daga ƙarshe ta yi shiru, su Ammi sun jima a asibitin sannan suka yi wa su Mami sallama suka tafi. Da yammacin Ranar Mommy ta zo hannunta ɗauke da kayan dubiya niƙi-niƙi, da murna Raihan ta tare ta don wannan ne gani na biyu da ta yi wa Mommy bayan aurenta. A lokacin da Mommy ta zo su Mami sun tafi daga Sumayya sai Raihan da Al'amin, sai da ya gaida Mommy sannan ta ce masa Daddy yana bakin gate, a hanzarce Al'amin ya je ya shiga da shi. Daddy bai zauna ba atsaitsaye ya duba Sumayya ya dire mata kuɗi masu yawa sannan ya tafi, Mommy ta lura da irin ramar da Raihan ta yi, ta rame sosai sai dai ta yi haske, amma sai Mommy bata kawo komai ba don a zatonta ita ma ko Raihan ɗin cikine da ita. Ganin yadda zamansu yake ita da kishiyarta sai ta ji daɗi sosai, don ko kaɗan babu wani abu da Sumayya take nunawa Raihan a idon mutane, har a gaban Al'amin ta rage nunawa Raihan komai sai dai ta yi ta kissa da kisisina tana jan hankalinsa ta yadda sai ya yi mata abin da zai baƙanta ran Raihan. Mommy ba ita ta tafi ba sai da dare ya fara yi sannan Daddy ya kirata yana bakin gate don shi ma wata unguwar ya je ya dawo zai ɗauke ta su tafi. Raihan da Al'amin har bakin mota suka rakata suna yi mata ta gaida gida, duk wanda ya ga su Raihan ba zai ɗauka babu wata rashin jituwa a tare da su ba. Kafin su koma ɗaki tuni Sumayya ta kwashe kuɗin da Daddy da Mommy suka ajiye mata ta ɓoye su don a tunaninta Raihan za ta gaya wa Al'amin wanda sam Raihan bata damu da abin da aka bata ba. Sannu a hankali Sumayya ta warware jikinta ya yi sauƙi kafin a sallameta sai da ta samu Likitar ta zana mata irin dokokin da ya kamata ta gayawa mijinta dangane da lalurarta, lokacin da Dr Halima ta ji bayanin Sumayya bata kawo komai ba ta ɗauka tana son a gayawa Al'amin ne don ta samu kulawar da bata samu, don ko kaɗan bata kawo Raihan kishiyarta ba ce saboda irin kulawar da Raihan take yi da ita. Sai da suka gama komai Dr Halima ta kira Al'amin office ɗinta sannan ta ce, "Malam Aminu yau dai mun sallami Sumayya saboda jiki ya yi kyau, amma fa ba yana nufin shi kenan ta ci gaba da aikin gida ba. Ya kamata ta haƙura da mai gida na tsawon wata guda nan gaba, sannan idan da hali a bari sai bayan wata shida ta sake samun wani cikin saboda mahaifarta ta yi ƙwari. Sannan ta daina aikin wahala da duk wani abu da aka san zai jigatata..." Dr Halima ta jima ta gayawa Al'amin hanyoyin da ya kamata su bi don kaucewa sake samuwar wannan matsalar saboda su a ɓangaren asibiti ba su yadda da asiri ko turen iska.
Chapter 87 · 0% Book details