Sashe 67
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hannuwa biyu Raihan ta sa ta kare fuskarta tana ci gaba da kuka jikinta sai karkarwa yake kamar mai jin sanyi, Huzaifa bai damu da ganin halin da take ciki ba ya ci gaba da kai hannunsa masu ƙayoyi yana shafar fatar jikinta. Duk shafa ɗaya idan ya yi mata sai dai ta ji kamar yana zane jikinta da ƙananan allurai, ganin bata da Mafita ya sa Raihan ta sadaƙar rayuwarta ta gama zuwa ƙarshe, tana jin hannunsa ya sauka a gabanta jikinta ya ci gaba da ɓari zuciyarta ta sake tsinkewa. Huzaifa wannan karon har ya fi karon baya rikicewa don haka ya tasamman kusantarta ta kowanne hali, Raihan na ganin haka ta runtse idonta hawaye na zuba ta fara karanto duk wata addu'a da ta zo bakinta don ubangiji ya kawo mata ɗauki. Jin shiru kamar an yi ruwa an ɗauke ya sa ta buɗe idonta da mamaki take kallon ɗakin, ganin Huzaifa baya ciki zumbur ta miƙe cikin sauri ta fara laluben kayanta. A can gefen gado ta hango su hannunta har rawa yake ta yi sauri ta saka su tana waige-waige amma ko motsinsa bata ji ba, ɗaukwali kawai ta iya ɗaurawa ko mayafi bata bi ta kansa ba ta yi maza ta buɗe ƙofar ɗakin ta fara zabga gudu don fice wa daga gidan, don a yanda ta ayyana ko a ƙafa ne za ta ƙarasa gida matuƙar ta samu ta fice daga gidan. Tana zuwa bakin ƙofar da za ta sada da gate ta ci karo da tashin hankalin da ya fi na baya, tana buɗe ƙofar da niyyar zuwa gate ta ga wani ƙaton kogi tsayuwarta keda wuya wasu tafka-tafkan kadoji suka ɗago haɗe da buɗe mata baki tamkar za su haɗiye ta. Da sauri Raihan ta yi baya ta rufe ƙofar ƙirjinta na bugawa, babban abin da ya fi bata mamaki yadda aka yi cikin gidanta ya shafe da ruwa wanda a daren ranar da aka kawota ba haka ba ne. Su Daddy ne suka faɗo mata a rai, da gudu ta faɗa cikin ɗakin ta fara laluben jakarta. Daga can jikin bango ta fara jin numfashinsa sama-sama wannan ya sake ɗaga hankalinta hannu na rawa ta ɗago waya ta nemo lambar mommy, amma wayar duniya da ta yi bata shiga. Haka ta riƙa bin lambobin wayar mutane tana kira amma babu wacce ta shiga balle ta saka ran za ta ji an ɗauka.
Huzaifa da yake daga jikin bango ya dubi Raihan a ƙufule yana faɗin, "Akan wane dalili za ki yi addu'a ko kina son na haike miki ta dole." Raihan bata kalli wurinsa ba tana daga zaune ta cusa kanta cikin cinyoyinta nan take fashe da wani irin matsanancin kuka. Tana cikin kuka nasihar Mommy ce ta faɗo mata da take yawan gaya mata a duk lokacin da ta ganta cikin damuwa ta yi sallah ta yi addu'a ta kaiwa Allah kukanta, a hankali ta ɗago ta share hawayenta lokaci ɗaya ta ji tsoron komai ya fita daga ranta. Miƙe wa ta yi ta taka ta kan gado don ko kallon Huzaifa bata son yi balle ta bi ta ɓangarensa, banɗaki ta shiga bakinta ɗauke da addu'a ta ɗauro alwata. Tana fitowa Huzaifa ya fara nunata da hannu yana faɗin, "Kar ki yi abin da kike shirin yi, na gaya miki kar ki yi." Da farko tsoro ne kama Raihan har take ganin kamar Huzaifa zai iya yi mata wani abin, saboda ko kaɗan bata kawo Huzaifa ba mutum ba ne. A tunaninta yana daga cikin ƴan ƙungiyar tsafe-tsafe ya aureta ne don ya tsaface ta. A ɓangare ɗaya kuma wata zuciyar na azalzalarta akan ta je ta gabatar da nafila ta roƙi Allah ya kawo mata mafita a rayuwarta, tun da ta lura addu'a ta yi tasiri akan Huzaifa. Daga gefe ta raɓa ta fara sallah, tana sallah tana kuka a sujjada tana kaiwa ubagiji kukanta. Raihan ta yi salla ta fi a irga bayan ta idar ta zauna tana addu'a, daga gefenta ta ji Huzaifa ya zabga ƙara daga nan ba ta sake ganinsa ba. Bata saurara ba ta ci gaba da addu'a sannu a hankali ɓarawon da ya fi kowa iya sata ya yi awon gaba da ita.
Washegari.
Tun da sassafe wasu daga cikin baƙin da suka hallaci bikin Raihan suka fara haɗa kayansu, don yawanci a ranar suka ce za su tafi. Mommy zuciyarta fari ƙal da ta wayi gari da tunanin Raihan ɗin ta tana gidan mijinta, har tana ayyana a wannan lokacin tuni ta riga da ta zama cikakkiyar mace. Shi kansa Daddy zuciyarsa fes ya wayi gari da ganin an yi komai lafiya an gama lafiya ba tare da wani abu mara daɗi ya faru ba. Ko babu komai zuwa wannan lokacin hankalinsa ya kwanta tun da ya aurar da Raihan, don haka yake jin sa wasai kamar ba shi ba. Su Inno da Goggo sai hidima ake da baƙi suna yi suna masifa don ko abu kaɗan mutane suka yi ba daidai ba sun rinƙa faɗa kenan. Wani lokacin Mommy har kunya take ji har sai ta ja su ɗaki ta yi musu magana, amma suna fitowa duk irin faɗan da Mommy ta yi musu za su zayyane shi a waje. Kimanin ƙarfe goma wasu daga cikin tsirarin da ba su je gidan Raihan ba suka shirya tare da Mama Hafsa da wasu sauran waɗanda aka je da su da dare, Mommy ce ta ɗauko waya ta nemo lambar Raihan don ta kirata ta gaya mata ga baƙi nan za su ƙaraso gidanta. Sai dai a kiran farko aka tabbatar mata da wayar a kashe. Bata kawo komai ba don haka su Mama Hafsa kai tsaye suka shiga mota suka wuce unguwar Medile, Su Mama Hafsa sun zagaye unguwar da suka kai Raihan ya fi sau biyar amma ko mai fasalin kama da gidanta ba su gani ba, ganin haka ya sa suka fara jajantawa a junansu daga ƙarshe suka yanke shawarar tambayar wani Mai shagon aski, da yake sun gane shi shagonsa a farkon layin gidan Raihan yake. Sai da Mama Hafsa ta yi masa sallama sannnan ta jefa masa tambaya, "Ƙanina don Allah gidan wata amarya da aka kawo jiya muke tambaya." Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Amarya kuma a nan layin? Kai gaskiya ƙila ba a kwatanta muku daidai ba, amma nan kusan wata guda kenan ba a kawo sabuwar amarya ba." Mama Hafsa jin maganarsa ta ji kamar har da rainin wayo a ciki, don haka ta yi masa sallama suka ƙara gaba. A can gefen wata ƙatuwar bola ta yi parking ɗin motarta, ta dubi Hajiya Lawisa ƙawar Mommy ta ce: "A daidai wurin bolarce wallahi nake ganin kamar jiya nan nan ne daidai wurin da gidan Raihan yake." Hajiya Lawisa da ta cika da mamaki ta ce, "Ba kama ba ce, wancen shagon telan shi yake kallon gidanta kuma ga shi nan a yadda yake yanzu ma haka yake, tun da jiya har magana na yi da shi kafin mu tafi na ce zan kawo masa ɗinkin wani les. Tabbas jikina yana ba ni akwai matsala." Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Matsala babba ma kuwa, amma mu fara zuwa Fagge gidan Iyayen Huzaifa kafin mu koma gida." Tana rufe baki ta tayar da motarta kai tsaye suka wuce unguwar Fagge sauran motoci biyun da suka taho tare suka rufa mata baya.
Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
37