Sashe 80
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hankali a tashe Daddy ya fita yana ƙwala wa Likitoci kira, Kabiru har ya suka fita ya ji muryar Daddy yana juyawa ya ga Likitoci sun nufi ɗakin Raihan. A guje ya juyawa jiki na rawa don ya ji lokacin da Daddy yake gayawa Dr Bashir halin da Raihan take ciki, yana niyyar shiga ɗakin Dr Muhammad ya dakatar da su shi da Daddy suna nan tsaye Malam ya fito cikin tashin hankali, don tun da yake bai taɓa ganin matsanancin abin da ya faɗar masa da gaba kamar wannan ba. Mommy ce ta ƙaraso fuskarta ɗauke da fara'a da yake a lokacin ta fita raka wata ƙawarta da ta zo dubiya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ta sha jinin jikinta don haka jiki a sanyaye ta dubi Daddy ta furta, "Daddyn Raihan lafiya kuwa?" Jinjina kai ya yi ya ce jikin Raihan ne ya tashi." Tun bai rufe baki ba Mommy ta nufi ƙofar za ta shiga Daddy ya sha gabanta da sauri yana cewa, "Ina za ki shiga Zainab? Baki gan mu a waje ba Likitoci ne suke aikinsu don Allah ki bari su gama." Hawaye ne ya taru a idon Mommy ta ce, "Daddyn Raihan ina son ganin halin da take ciki ne." Girgiza mata kai ya yi don ya tabbata da tana nan Raihan ta fara aman jini babu ko tantama ita ma sai an tallafi tata rayuwar, cikin dakiya ya ce mata: "Na ce ba za ki shiga ba, idan ki shiga kina da abin da za ki yi mata ne?" Gefe mommy ta matsa tana hawaye don a wannan lokacin jikinta ya gama sanyi da lamarim ciwon Raihan, sun jima a nan wurin Dr Bashir ya fito fuska babu walwala jiki a sanyaye ya furta, "Alhaji gaskiya yuwar canja wa yarinyar nan asbiti domin lamarin ciwonta yana neman gagararmu, mun yi mata allurar tsayar da aman nan abin ya ci tura babban tashin hankalinmu yanda jini ya ɓalle daga gabanta. Yanzu haka bata cikin hayyacinta so za mu taimaka da Amblance aka kaita babban asibiti, da gudu Daddy ya faɗa ɗakin ba tare da ya tsaya jin ƙarashen zancen Dr ba. Yana zuwa kusan mutuwan tsaye ya yi ganin yadda Raihan take kace-kace cikin jini, jiri ne ya ji ya fara ɗaukansa a hankali ya dafa bango sannan ya riƙo gefen rigar Dr Bashir ya ce, "Dr don Allah kar ku yaudare ni, idan har kun san yarinyar nan ta rasu kada ku ɓoye min domin dukkan mai rai mammaci ne." Dr Bashir ya kalli Daddy ganin yana hawaye ya sake sanyaya gwiwarsa domin shi kansa baida tabbacin Raihan za ta tashi ko ba za ta tashi ba, don kar ya sake karya gwiwar Daddy ya girgiza kai ya ce, "Alhaji idan mutuwa ta yi ba za mu ɓoye muku ba domin ba ma ɓoye wa mutane mutuwar patient ɗin su. Raihan tana da rai sai dai tana cikin wani irin yanayi da take buƙatar agajin gaggawa. Mun yi bakin ƙoƙarinmu amma mun kasa sai dai aka kaita babban asibiti domin suna da manyan injinan da ba mu da su." A gaggauce aka ɗauki Raihan aka saka ta a mota ba tare da ta san waye a kanta ba. A wannan karon Mommy kasa kukan ta yi saboda yadda zuciyarta ta bushe, Malam da Kabiru a mota ɗaya suka tafi Daddy da Mommy a motar asibitin da aka saka raihan. Kai tsaye daga nan asibitin AKTH aka wuce da ita ɓangaren Emergancy, da sauri suka karɓe ta suka shiga bata agajin gaggawa. Allurai suka yi mata suka shiga ƙoƙarin neman jijiya domin saka mata ledar jini saboda na jikinta sai zuba yake, amma suka nemi jijiya sama da ƙasa suka rasa. Likitoci kusan bakwai ne akanta amma tana sharɓe tamkar gawa ko motsi bata yi. Daga mommy har Daddy babu wanda bai fidda rai da Raihan ba, saboda duk wanda ya ganta ba zai ce tana numfashi ba. Malam da Kabiru suna zaune duk sun yi jigum-jigum, kuɗi ya zaro ya miƙa wa Kabiru ya furta, "Siyo min ruwan gora guda biyu." Kabiru ya miƙa masa ya ce, "Yanzu miƙewar da ka ga na yi shi zan siyo ina son na yi wa Raihan tofi, riƙe kuɗinka Malam zan taho maka da shi." Malam ya ce, "Ah haba ina ba za a yi haka ba ni ma tofin nake son yi mata saboda wannan yanayin nata ya ba ni tsoro." Kabiru ya ɗora masa kuɗin akan cinyarsa ya fice, bai jima da fita ba ya dawo da ruwan gora guda huɗu tare da man zaitun ya ɗauki biyu ya miƙa wa Malam biyu. Bakinta ya buɗe ya ɗan kurɓi kaɗan sannan ya fara karanto ayoyon alƙur'ani yana tofawa. Daga ɓangaren Malam ma tofin ya fara yi mata don tun da ya ji an ce jini har ta gabanta yake zuba daga jikinta, Huzaifa ya faɗo masa duk da ya san ciwon zuciya babu abin da baya saka wa amma zuciyarsa ta ƙi aminta da ciwon zuciya ne ya haifarta mata zubar jini ta gabanta. Saboda ya san sheɗanu na iya shiga jikin mara lafiya musamman idan sun shafe shi su ƙara tunzura ciwonsa, idan har abin yanzo da ƙarar kwana sai a rasa. Idan kuma da yuwuwar a tashi sai a sha matuƙar wahala.