← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 110

Sashe 97

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Al'amin na zuwa gida a ɗarare ya shiga falon Mahaifinsa, ƙafa ɗaya ya saka Malam ya dakatar da shi da cewar, "Koma mu je gidansu Yarinyar nan za mu." Al'amin na son yin magana amma yana fargaba don yanayin Mahaifinsa ba ƙaramin tsorata shi ya yi ba. Al'amin ya yi tsammanin motarsa Malam zai shiga, amma ga mamakinsa sai gani ya yi ya buɗe ta shi motar ya shiga. Motarsa ya koma ya zauna sannan ya kunnata suka wuce gidansu Raihan, sai da suka je bakin gate sannan Malam ya ciro waya ya kira Daddy da yake ta zarya shi kaɗai a falon baƙi. Yana ɗauka Malam ya gaya masa suna ƙofar gida don haka da kansa ya je ya buɗe musu, Al'amin sai sunne kai ƙasa yake kamar sabuwar amarya. Falon baƙi ya kai su bayan sun sake gaisawa suka sake jajantawa juna abin da ya faru, sannan Malam ya ce sun zo ne su ba shi haƙuri don Raihan ta koma gidan Mijinta. Daddy da kansa ya je ya kira Raihan tana tafe gabanta na faɗuwa har ta shiga ɗakin, a can gefen ta rakuɓe ta gaida Malam ya amsa mata cikin tausayawa don kallo ɗaya za ka yi wa Raihan ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa. Raihan na daga tsugunne ta ji suna maganar komenta a hankali ta ɗago ta ce, "Daddy saki uku fa ya yi min." Daga Daddy har Malam buɗe baki suke yi haɗe ta yin salati, Malam ne ya fara faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daddy ne ya dakatar da Malam yana faɗin, "Malam ba haka ake ba, yaron nan yau tsawon watansu nawa ko ƙara ɗayansu babu wanda ya taɓa kawowa, ya kamata aji ta bakinsa ba a rufe shi da faɗa lokaci ɗaya ba." Daddy ya ƙarasa maganar yana tambayar Al'amin. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya sanar musu iya abin da ya sani game da duk abin da yake faruwa a tsakaninsa da Raihan, sannan ya ciro waya ya nuna musu duk abubuwam da aka taɓa tura masa na Raihan da wani matashin saurayi. A razane Daddy ya miƙe tsaye ya furta, "Kabiru? Wannan cin amanar Kabiru zai yi min?" Raihan da a lokacin ta kai idanunta wurin ta zaro ido ganin Hotonta da Kabiru a maƙale da juna a yanayin da suke kamar ma'aurata, ko ma'aurata bai kamata su ajiye irin wannan hoton a wayarsu ba. Jikinta na karkarwa ta miƙe tsaye tana faɗin, "Wallahi-wallahi Daddy ban san komai ba Allah ba ni ba ce sharri aka yi min..." Raihan ba ta ƙarasa magana ba Daddy ya katse ta, ta hanyar zabga mata mari. A fusace ya shaƙo wuyanta yana faɗin, "A gidan uban wa yake yi miki ƙarya? Allah ya sani mun baki tarbiyya daidai gwagwado don haka..." Daddy bai ƙarasa magana ba, Malam ya riƙo hannunsa ya zaunar da shi da ƙyar ya ƙwace Raihan daga hannunsa. A gefen ƙafarsa ya zaunar da ita ya nemi Raihan da ta sanar musu da duk abin da yake faruwa. Nan take Raihan ta zayyane musu duk abin da yake faruwa tun daga farkon aurensu har lokacin da Al'amin ya saketa. Ba ƙaramin mamaki suka yi ba Al'amin tun da ya sunkuyar da kai bai ɗago ba saboda kunya, Daddy ya kalli wayar Al'amin da ke hannunsa ya kalli Daddy ya ce, "Waye Kabirun?" Cikin huci Daddy ya furta, "Shi ne yaron da na gaya maka rashin lafiyarsa." Murmushin takaici ne ya suɓucewa Malam, Daddy ya bishi da wani irin kallo yana shirin magana Malam ya ce, "Alhaji ka nutsu ka ba ni hankalinka a nan?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana wurgawa Raihan harara, sai dai a lokacin ya rage jin zafinta. Malam ya ci gaba da cewa, "Yau kwanan Kabiru nawa yana jinya?" Daddy ya yi jim sannan ya ce, "Zai yi wata ko fi ma ina jin." Malam ya jinjina kai ya kalli Al'amin ya ce, "Na ji ka ce wannan na jikin hoton shi ne wanda ya fito daga ɗakin Raihan ɗazu ko?" Cike da gamsuwa Al'amin ya gyaɗa kai ya ɗora da cewa, "Kuma wallahi ko Sumayya aka tambaya za ta faɗa don ba wannan ne zuwansa na farko gidan ba." Malam ya kalli Daddy ya ce, "Ban yi mamaki ba." Daddy ya dube shi da alamun tuhuma yana faɗin, "Kamar yaya Malam?" Malam ajiye wayar Al'amin sannan ya ɗora da cewa, "Huzaifa!" Ɗauuu! Haka Daddy ya ji maganar Malam har tsakar kansa, yana cikin nazari ya riski muryarsa yana ci gaba da cewa, "Tabbas Huzaifa ya ci kasuwarsa ya watse kuma buƙatarsa ta biya domin ba na raba ɗaya biyun wannan yana daga cikin kaidinsa. Alhaji ba sai na yi maka dalla-dalla ba tun da, da idanunka ka je ka gano Kabiru a garinsu ko magana baya yi sannan kuma ace har yana zuwa wurin Raihan. Shin tun da kake kiran lambar ka taɓa samun ta shiga? Ko kuma ka taɓa zama ka tambayi Raihan don ka ji ta bakinta?" Al'amin sai girgiza kai yake, Malam ya kalle shi sannan ya ci gaba da faɗin, "Ka ba ni mamaki Aminu da baka da dogon nazari da lissafi domin tun kafin ka auri yarinyar nan ban zayyana maka matsalar da take fama da ita ba? Ban ce maka duk wani abu da ka gani ba daidai ba ka sanar da ni? Kai fa mai ilimi ne ina tarin ilimin naka da ba za ka yi aiki da shi ba? Tun wuri ka dawo hankalinka domin muddin ka ɗore a haka soyayyar matarka za ta kai ka jahannama." Malam ya dubi Raihan ya ce, "Je ki ciki ƴar gidan Abba." Raihan ta miƙe kanta na sara mata ta wuce cikin gida, a tsawace ya dubi Al'amin ya ce, "Sakaran banza sakaran wofi, ka buɗe kunne ka ji ni da kyau. Dama matuƙar matarka ta warke ka cewa iyayenta su wuce gidansu da ita. Yadda na faɗa maka haka za ka shaida musu." A firgice Al'amin ya dubi Mahaifinsa. Malam ya nuna masa ƙofa ya ce, "Fice ka ba ni wuri." Kamar sabon munafuki haka Al'amin ya fice sum sum sum daga ɗakin gwiwarsa a sanyaye. Malam ya kalli Daddy ya ce, "Khalid Saleh wani amintaccen Aljani ne da mun ɗauki tsawon shekaru tare, a daren jiya ya sanar da ni ya gano wurin da Huzaifa ya samu mafaka, ban so gaya maka ba na so ace sai sun kamo min shi zan kira ka, amma tun da lamarin har ya kai ga haka a gobe ina da buƙatar ganin wannan Kabirun mara lafiya." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya furta, "Shi kenan Alhaji zan kira Mahaifiyarsa mu yi magana."Malam ya miƙe yana daɗa bawa Daddy haƙurin abin da ya faru, har ƙofar gida Daddy ya raka shi sannan ya nemi Malam da ya janye hukuncin da ya yanke akan Al'amin amma fir ya ƙi amincewa.

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

49

Jiki a sanyaye Daddy ya dawo gida wurin su Mommy, Inno na ganin Daddy ta ce, "Audullahi yanzu nake shirin zuwa wurinku ni fa ban gane ba." Daddy ya zauna akan kujera yana faɗin, "Da me fa Inno?" Da yatsa ta nuna Raihan sannan ta ce, "Yarinya nan ko baiwa ka siyo daga garinku sai haka, saboda Allah haka yaron nan zai zo ya tafi shi da Mahaifinsa salin-alin babu wani cin mutumci da ka yi musu balle ka sa hukuma ta kama su?" Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya ce, "Inno duk wannan abin da yake faruwa Huzaifa..." Da sauri Inno da Goggo suka katse shi cikin haɗin baki suna cewa, "A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim." Goggo ta girgiza kai sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Audullahi ka bar ambatar sunan nan a gidan nan ko ma samu kurwarmu ta zauna lafiya." Daddy ya miƙe tsaye yana cewa, "Shi kenan Goggo." Har ya yi gaba ya juyo ya kira Mommy sannan ya shige cikin ɗaki. Nan take Mommy ta miƙe ta bi bayansa don ita ma bakinta cike yake da tambayoyin da take son yi masa. Mommy na wuce wa ɓangaren Daddy, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Wai Audullahi ko haushinmu ya ji?" Inno ta taɓe baki ta furta, "Ni ma abin da zan faɗa kika riga ni, amma saboda Allah ina ce Huzaifa dai ba ƙanin Alhaji Babba ba ne?" Goggo ta kalli hanyar sashen Daddy tana cewa, "Baki ga ya kira matarsa ba, ko shawarar me za su yi oho." Raihan na jin maganganun su Inno sun fara damunta ta tashi ta wuce ɗakin Mommy, tana shiga ta haye gado ta kwanta ta shiga tunanin matsalolin rayuwarta. Hawaye ne ya zubo mata saboda tausayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, tuno abubuwan da suke faruwa da ita ta fara yi tun tana ƙarama. Tun bata san kanta ba take wata irin wahalalliyar rayuwa gashi har ta girma bata samu sassauci a cikin ta ba.
Chapter 97 · 0% Book details